Yadda ake ɗaukar sauti a cikin ɗaki cikin sauƙi, za ka iya ɗaukar sauti a cikin ɗakinka, ba tare da ka shiga studio ba.
Kafin ka fara ɗaukar sauti a cikin ɗaki ko a waje, akwai matakai da ya kamata a kiyaye, sannan irin kayan aikin da ya kamata a samu kafin a fara.
Na farko a kiyaye ɗaukar sauti a cikin ɗakin da yake da hayaniyar mutum babba ko yaro.
Na biyu a kiyaye ɗaukar sauti a cikin ɗaki, ba tare da an rufe taga ba, ko kofa, domin hana iska shigowa cikin sautin.
Na uku a tabbatar kayan aikin da za a yi amfani da su masu inganci ne.
Na huɗu, duk abin da za a faɗa ya zamanto a rubuce yake domin gudun yawan kuskure lokacin ɗaukar sautin.
Bayan kiyaye waɗannan sharuɗa, za a fara samun shi kansa gundarin abin da za a faɗa, kuma ya zama a rubuce, idan kuma ba a rubuce yake ba, a kula sosai wajen kiyaye maimaita kuskure.
Sannan akwai yiwuwar ka fara sanin wane irin nau’in kayan aiki ya kamata ka yi amfani da shi, domin samar da sauti mai inganci, sannan da wane irin abin magana (MIC) za a yi amfani.
Ɗaukar sauti a cikin ɗaki zai fi sauƙi idan aka yi amfani da abin da yake ɗauke da chaji domin gujewa daukewar wutar lantarki. Misali wayar hannu mai dauke da ingantaccen abin naɗar sauti, sannan akwai Computer wadda ita ma na ɗauke da abin naɗar sauti wanda zai wadatar. Na ƙarshe ita ce Radio wadda ke dauke da na’urar recording.
Bayan samu ɗaya daga cikin waɗannan kayan aiki, sai a kula sosai wajen sanin inda za a ajiye shi, domin ya dace da inda ake buƙata.
Kafin a kunna na’urar ɗaukar sauti, a kula da yin rehassal na shi, abin da ake son karantawa ko faɗa.
Yadda za a fara ɗaukar sauti
1. A matsar da na’urar ɗaukar sauti daga kusa da baki, ya kasance akwai tazara tsakanin ta da bakin mai karatu.
2. A samu wani abu a ɗora ita na’urar ɗaukar, ta yadda ba za ta dinga motsawa ba idan an fara.
3. A kunna na’urar, ta fara tafiya da kamar daƙiƙa (second) 2-5 kafin a yi magana.
4. Idan an fara, kar a dinga kautar da kai ya zuwa gefe, sai idan za a huta ko jan dogon numfashi.
4. Idan an kammala, kafin tsayar da daukar, a ƙara daƙiƙa (second) kamar 3-5 sannan a tsayar da ɗaukar.
5. A saurara kafin a tabbatar da shi a matsayin ɗauka mafi kyau, da za a yi amfani da shi, idan ɗaukar bai yi kyau ba sai a sake.
Wannan shi ne bayani game da yadda ake ɗaukar sauti a cikin ɗaki.