Bayanin yadda za ka yi amfani da Gmail account, cikin sauƙi, da kuma hanyoyin da ake amfani da shi.
Gmail account na nufin Google Account, asusun manhajar Google dake amfani a ɓangarori daban-daban. Gmail ya kasance ɗaya daga cikin manhajar karɓar saƙonni mafi suna da ake amfani da shi a yanzu. Zuwa yanzu akwai aƙalla masu amfani da Gmail mutum million 500.
Amfanin Gmail account.
Gmail na da akwaitin karɓar sako dake bayar da damar aika sako da kuma karɓa, sannan za ka iya adana bayanan hotuna da kuma videos har ya zuwa adadin 15 Giga byte (15GB) a matakin farko, idan kuma akwai buƙata, Google zai iya sayar da adadi mafi yawa, har da matakin da ba shi da iyaka, wanda aka fi sani da (Unlimited).
Adireshin Gmail na amfani wajen shiga manhajoji daban-daban, waɗanda ke da alaka da Google, dama waɗanda ba su da alaƙa da shi, kamar su; Google+, YouTube, Duo, Chrome, Drive, Playstore da sauran su.
Google+
Google+ wanna na ɗaya daga cikin shafukan sada zumunta wanda aka samar da shi ƙarƙashin kamfanin Google. Ana rijista da Gmail domin shiga Google+.
YouTube
Shafin YouTube na ƙarƙashin kamfanin Google, wanda ake iya sakawa da kuma kallon videos. Ana rigista da adireshin Gmail ne kaɗai, domin saka Videos a cikin shafin.
Duo
Wannan wata manhaja ce da ake amfani da ita domin kira na ji da na kallo, ƙarƙashin kamfanin Google. Ana rigista da Gmail domin samun damar amfani da manhajar Duo.
Drive
Drive (Google Drive) wata ma’adana ce ta yanar gizo, dake baiwa masu amfani da asusun Gmail ajiye kaya a ciki kamar hotuna, waƙoƙi, videos da document ƙarƙashin kamfanin Google
Playstore
Play store ma’adanar manhajar Application ne dake baiwa masu wayar Android damar saukar da (dawnloading) Application ƙarƙashin kamfanin Google.
Ana iya amfani da adireshin Gmail domin yin register a shafukan sada zumunta daban-daban kamar su: Facebook, Twitter, Instagram, Linkdin, Snapchat da sauransu.
assalamu alikum yan uwa musulmai inamika gaisuwana ga maza da mata dafatan kowa yana cikin koshin lfy
Sharhi:lfy kalau
yy gajiya
omotayademola@gmail.com