Asalin Samuwar Intanet

0
653

MA’ANAR INTANET

Kalmar Internet kalmomi biyu ne suka hadu wajen ginuwarta wato International da Network wadda a Hausa muke cewa Yanar gizo ko Giza-gizan sadarwa. A Makalar sa The Internet as Mass Medium Farfesa Merril Morris ya ce: “Intanet na nufin hade-haden da ke tsakanin kwamfutoci dake basu damar mika sakwanni ko karba

ASALI DA SAMUWAR INTANET.

Wannan tsarin kirkira na fasahar Intanet ta samo asali ne 1964 kasar Amurka ta samar da tunanin tsarin Advanced research Projects Agency Network (ARPANET) da NODES domin tanadi da kariya bayan yakin duniya na II. Sai kuma zangon farko a farkon shekarar 1969CE a University of California, Los Angeles (UCLA), da yan kwamfutoci da basu shige dari ba,

amma a halin yanzu akwai wajen mutane Biliyan 4.5 da suke ta’amuli da wannan fasaha mafi girma ta karni na Ashirin da daya(21st Century).

Gidan Intanet ya na da kofar shiga wato www. Wadda ka’ida ce da Farfesa Tim Bernes-Lee (Baban Intanet) ya kirkira a shekarar 1991 da Hypertext Markup Language (HTML), da zarar ka shiga farfajiyar gidan akwai biliyoyin dakuna wanda kowa da irin wainar da yake toyawa a irin nasa dakin

Fasahar Intanet ta na da muhimman bangarori daga cikinsu akwai fasahar imel (E-Mail), shafukan yanar gizo(Web), shafukan sada zumunta (Social Networking Sites), wasanni da shakatawa a yanar gizo (online gaming) da kuma Software Update.

Marubucin shahararriyar mujallar The Future Organization Farfesa Jacob Morgan ya bada ma’anar IoT (Internet of things) da cewa:
“Tsari ne na auratayya tsakanin shafukan sada zumunta da kayayyakin gida, abubuwa marassa rai ko dabbobi ta yadda zasu iya sarrafa kan su ta hanyar UIDs (Unique Identifiers)”
Fasahar IoT a shekarar 2012 ta na kunshe da na’urori mabanbanta kimanin Biliyan 8.7, amma daga watan Yuli, 2019 wancan adadi ya hauhawa zuwa Biliyan 26.66. Manazarta alkaluma sun tabbatar da cewa zuwa 2025 za’a samu na’urori a kan IoT kimanin Biliyan 75.447. Tirkashi!, akwai abin lura game da wannan alkaluman da hasashen.

Danna koren rubutun nan domin karanta amfani da hadurran shafukan sada zumunta 

BAR AMSA

Please enter your comment!
Please enter your name here