Yadda Ake Buɗe Transfer A Layin MTN Cikin Sauƙi.

0
4377

Bayani kan yadda za a iya buɗe transfer a layin MTN, a kan waya cikin sakan biyar (5).

Mafi yawan masu amfani da layin sadarwa na MTN kan sha wuya, ko ɓata lokaci wajen neman yadda za su tura kuɗi ta kan layinsu ya zuwa wani layin na MTN. Waɗansu kan yi tattaki har cikin kamfanin MTN domin a yi musu register kafin su fara tura kuɗi.

Hanya ta farko, kuma mafi sauƙi wajen bude transfer a layin MTN, shi ne ta hanyar amfani da USSD code (*123#).

Hanya ta biyu, ita ce hanyar tura sako ya zuwa kamfanin MTN, sannan su bude maka nan take.

Yadda ake buɗewa (Register)
Da farko a tabbatar wani bai taba bude transfer da layin ba. Sannan numbobin da za a saka wajen buɗewa, su zama na sirri ne, ba tare da an sanar da wani ba.

Da farko za a dannan star 600*1234* sannan a zabi numbobi guda hudu, wanda sune ake amfani dasu a ƙarshe wajen tura kuɗi, sai a ƙara danna star (*), sannan a ƙara saka numbobi huɗun da aka zaɓa, sannan a danna hash (#), sai a danna madannin kira. Misali;
*600*1234*5555*5555#

Bayan an tura, idan ya nuna;

“Your PIN have been changed succesfully”

Register tayi.

Hanya ta biyu, ta amfani da sakon SMS.
Za’a shiga akwatin tura sako, sai a rubuta
1234 sannan a bada tazara (space) sannan a saka numbobi huɗu da ake so misali 5555, sannan a sake bayar da tazara, sannan a tura zuwa ga 777, misali;
“1234 5555 5555”
Ba tare da ɓata lokaci ba, za a aiko da sakon cewar registar da aka yi tayi.

Yadda ake tura kudi.
Bayan kammala registar, idan za a tura kudi, sai a dannan star(*) (600) sannan star (), sai a saka number wanda ake son turawa kuɗin, sai a ƙara danna (), sai a saka adadin yawan kuɗin da za a tura, wanda yake farawa daga kan #50 zuwa #5000, sannan (), sai kuma numbobi huɗu da aka zaba wajen bude transfer, sai alamar (#) sannan a dannan kira. Bayan gama loading idan ya yi za a nuna

“Thank you for using share n sale”

Sannan sako ya shigo wayar na alert, wanda zai tabbatar da transfer ya yi.

labarin da ya wuceAna Kiran Sallah Hailata Ta Zo
Labarin na GabaBuɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Iyaye Mata A kan ‘Ya’yansu Mata