Shin Me Ake Iya Yi Da Komfiyuta?

0
408

Mutane da dama suna amfani da Komfiyuta wurin samun sauƙin aikinsu na yau da kullum. Misali idan muka duba; mutum zai iya ɗauko aiki daga ofishinsa zuwa gida domin ƙarasa aikin da ya fara a can.

Haka ɗalibai suna iya ci gaba da nazari ko binciken da suka fara a Komfiyutar makaranta idan sun dawo gida, wannan aiki kuwa mutum zai iya yin amfani da safe ko da rana ko cikin dare;

Haka mutum zai iya amfani da wannan kwamfutar domin tafiyar da harkokin kasuwancinsa ta hanyar rubuta wasiƙa; ko waɗansu bayanai masu muhimmanci na kasuwancinsa, ko kuma shirya kasafin kuɗi.

A taƙaice dai duk wani irin aiki da za ka iya yi da Komfiyutar wurin aiki; za ka iya yin shi da kwamfutar da ita a cikin gida.

Lura Da Hada-Hadar Kuɗaɗe Da Kasuwanci

Ba ka buƙatar zama ƙwararren masanin harkokin kuɗi wurin kula da kuɗaɗenka da kasuwancinka idan aka zo maganar Komfiyuta.

Akwai waɗansu manhajoji a cikin Komfiyuta waɗanda da su za ka iya lura da kuɗaɗe kamar irin su Microsoft money ko kuma Quicken wanda da waɗannan za ka iya shirya kasafin kuɗi.

Ko kuma rubuta takardun karɓar kuɗi ko kuma bincikar labarin ragowar kuɗaɗen da suke asusunka; da ke bankinka take daga jikin kwamfutarka ba tare da kana da ilmin a kanta ba.

Haka zalika, za ka iya sanya kwamfutarka ta ɗauki ragamar biyan kuɗaɗe ta banki da kanta na haƙƙoƙin jama’a ko biyan kuɗaɗen harajin gwamnati, wanda ba sai ka je banki don gabatarwa ba.

Ƙulla Alaka Tsakanin Mutane

Da kwafuta ana iya aikawa da wasiƙa wacce ake kira da imel [email] ga ‘yan uwa da abokan arziƙi ba ka buƙatar jiran lokaci mai tsawo kafin wannan saƙo ya kai ga wurin daka aika shi.

Haka ana amfani da kwamfuta wurin yin magana ko muhawara da jama’a kai tsaye ta hanyar amfani da intanet.

Ko kuma kiran kwamfuta da wata kwamfuta wanda aka fi sani da pc to pc call; wannan duk wani sauƙi ne ake samu a wurin kwamfuta.

Yin Hada-Hada A Intanet

Kamar yadda muka faɗi, amfani da fasahar email ya kawo sauƙi wurin aikawa da saƙonni haka ma intanet.

Internet wata kafa ce da mutane ke amfani da ita wurin gabatar da abubuwa masu muhimmanci da kuma aikace-aikacen da suka saba yi a zahiri da jama’ a.

Kamar gabatar da harkokin kasuwanci wanda ya haɗa da sayarwa, yin karatu da manyan jami’o’i na duniya, karanta jaridu da mujallu duk a kan intanet, alhali mutum na zaune a gida ko ofishinsa waɗannan kaɗan ne daga cikin irin aikace-aikacen da ita komfiyuta take iya yi da kuma sauƙin gabatar da al’amura.

Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Komfiyuta (Computer) danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Activating Windows 10 Da Batch File (CMD)
Labarin na GabaJinin Haila Da Jinin Biƙi
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.