Da farko yadda ake ajiye lambobi a asusun Gmail, akwai buƙatar a ce kana da Gmail, sai ka yi rijista da shi a akwatin saƙon (Gmail) wanda ke a cikin wayarka bayan ka yi rijista.
1- Za ka shiga cikin contact din wayarka kamar haka:
2- Bayan ka shiga cikin contact ɗinka daga sama, za ka ga wasu ɗugo guda uku, sai ka taɓa su, za ka ga sun fito maka da wasu rubutu kamar haka:
3- Sai ka taɓa inda aka rubuta import/export, zai mayar da kai wani waje, sai ka taɓa inda aka rubuta COPY TO kamar haka:
4- Bayan ka taɓa zai kai ka inda za ka zaɓi inda za ka saka lambobinka, da ka saka za ka ga sunan gmail ɗinka sai ka taɓa shi kamar haka:
5- Zai kawo ka inda lambobinka suke, sai ka yi makin É—in su kamar haka:
6- Daga sama za ka ga inda aka rubuta “Done” sai ka taÉ“a shi shi kenan lambobinka sun yi copy a kan gmail dinka. Ko da ka canza wayarka ko ka sayi wata indai ka yi SIGN IN din Gmail ÆŠinka, za ka ga lambobinka sun dawo koda kuwa SIM É—inka ya fadi lambobinka ba za su É“ata ba.