Abubuwan Da Ya Kamata Ka Sani Akan Android

0
19

Android shi ne ƙwararren masanin nan wato Andy Rubin kuma shi ne ya ƙirƙiri ko kuma mu ce shi ne shugaban ma da ya fara samar da wannan tsari na android. Haka kuma shi ya ba da wannan sunan ga aikin sa, lokacin yana aiki da kamfanin Apple kafin ya koma aiki da kamfanin Google.

Tsarin android wannan wani kamfani ya samar da shi da ake kira android inc a shekara ta 2004 bayan an samar da kamfanin google wato kamfanin matambayi ba ya ɓata. Daga baya kamafanin na google ya saye shi a shekarar 2005 akan farashin dala milliyan hamsin $50 .

Tsarin android an samar da shi ne kawai domin samar da masarrafar daukar hotuna, daga baya kuma aka mai da tsarin zuwa sanya shi a cikin wayoyi domin ganin hakan shi zai fi dacewa. Google ya gabatar da tsarin android a ranar 5 ga watan Nuwamba a shekarar 2007 wanda aka yi shi a mazubin tsarin Linux.

Kamfanin samar da tsarin android na google yana da masu hulɗa da shi da suka haura adadin billion ɗaya a duniya, wanda Bahaushe ke cewa malala gashin tunkiya. Akan abubuwa daban-daban kamar wayar hannu da kuma wayar rataye wato tablets.

Htc dream ko t-mobile g1 shi ne tsari na farko da aka fara sanyawa akan manyan wayoyi wanda tsarin android ya fara aiki akai wanda aka sake shi aka fara aiki da shi a shekarar 2008. Banda Tsarin android 1.0 da 1.1, duk wani tsari da zai biyo baya ana kiranshi da wasu sunayen ne saɓanin na da, kamar jelly bean, ko kuma ice cream sandwich, wani kuma honeycomb da lollipop.

Mutane da dama suna tunanin wannan sunan na android da kuma alamar sa shi ake kira android, abun ba haka yake ba asalin sunan da ake kiran android Mascot da shin shi ne Bugdroid, ganin wannna ba zai zama sananne ba ko karɓuwa shi yasa kamafanin google suke kiran shi da wannan sunan na android.

Cikin abubuwan da wannan kamfani da ke samnar da android ya fi shahara da shi shi ne wannan babbar kasuwar ta hada-hadar massarafai wato google play store wadda aka yi ƙiyasin tana da masarrafai fiye da billion 48 wanda kuma kullum yana samun ɗimbin masu halarta daga gurare daban-daban na duniya, wanda kuma mafi yawancin waɗannan masarrafai na kyauta ne.

Haka kuma wannan kamfani dake samar da wannan tsari yana da wani tsari ko masarrafi dake a sararin samaniya wanda ake kira da NASA wanda aka sanya shi a sararin samaniya mai kama da mutum-mutumi na Nexus S wanda yakan yi amfani a tsarin wasu wayoyin kamar mutum-mutumin biredi mai suna “Gingerbread”.

Haka kuma dukkanin mutum-mutuimin da kamfanin android ya samar ko kuma yake kama da alamar android shi ne namiji, shi kuma mai kama da siffar mace shi ne ake kira da Gynoid. Kamafanin dake samar da android wato Google shi ne kamfani na farko da ya ba da damar a san yadda ake haɗa application domin sanya shi ko kara shi akan wani tsarin na masarrafai.

Wannan tsarin na kamfanin android an samar da shi a mazubai daban-daban wanda mafi yawanci suna tafiya ne bisa tsari. Wanda an samar da:

1. Android Asto (1.0)
2. Bender (1.1)
3. Cupcake (1.5)
4. Donut (1.6)
5. Éclair (2.0)
6. Froyo (2.2.x)
7. Gingerbread (2.3.x)
8. honeycomb (3.0)
9. ice cream sandwich (4.0.x)
10. jelly bean (4.x)
11. Kit Kat (4.4)
12. Lollipop (5.0-5.5.1)
13. marshmallow (6.0 -6.0.1)
14. Nougat (7.0 – 7.1.1)
15. Oreo (8.0).
16. New age (9.0.1)

Yanzu kamfanin android yana samar da abubuwan da suke aiki na ban mamaki kamar google glass, watches da dai sauran su. Haka kuma nan gaba kamfanin da ke samar da tsarin android suna ta ƙoƙarin kawo wasu sabbin tsare-tsare na zamani wanda su ma za su iya zuwa da nau’in sunayen su.

Domin Karanta Cikakken Bayani Akan Abubuwan Da Ya Kamata Ka Sani Dangane Da Twitter Danna nan.

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceAddu’a Idan Mutum Yana Cikin Damuwa
Labarin na GabaNeman Aure Bisa Koyarwar Musulunci
Engr. Suleiman Musa Abdullahi
Dalibi daga Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria Wanda na karancin bangaren addinin musulunci da koyar dashi a matakin farko, sannan na canja zuwa ga karatun fasahar sadarwar zamani Inda na halarci kasashe daban-daban India,Ghana, Africa ta kudu da Uganda domin samun horo da ha66aka karewa ta a bangarororin fasahar sadarwar da dangogin ta, ciki harda bada tsaro ga bayanai da binciken kwafkwaf da Na'ura domin bincikar masu laifi don samun hujjar gabatarwa a gaban kotu.