Abubuwan Da Ya Kamata Ka Sani Dangane Da Twitter

0
330

Twitter: Shi wannan shafin sadarwar mai suna Twitter na ɗaya daga cikin shafukan tattaunawa da muhawara, kamar yadda sauran shafukan suke, haka kuma, Twitter tana da yare nata na kanta, waɗanda waɗansu abubuwa ne da ya kamata a sani dangane da Twitter, domin sanin su tamkar fitila ce wadda za ta haska maka hanyar damar yin amfani da Twitter ba tare da wata matsala ba. Domin idan ka san yadda ake amfani da Twitter musamman wajen kasuwanci; sanin waɗannan zai ƙara ba ka damar bunƙasa kasuwancinka. Idan kuma ba ka da Twitter a kan wayarka, za ka iya shiga Google Play Store play.google.com ka sauke manhajar.

DM/Direct Message:

Wani saƙo ne na sirri da ake turawa tsakanin ka da wanɗanda kake son yin magana da su kai tsaye. Haka kuma, shi ma wanda ya karɓi saƙon yana da damar ya turo maka nasa saƙon da bai wuce harufa 140 ba, koda kuwa ba ya cikin jerin abokanka ko mabiyanka a shafin Twitter ɗin.

Follow:

Hanya ce da take haɗa mutane a shafin Twitter. Haka kuma, mutanen da ka zaɓi ka bibiye su, su ma za su iya ganin abubuwan da kake sanyawa a kan shafinka na Twitter. Haka kuma ba dole ba ne ba cewar wani ya bibiye ka, kai ma ka ce lalle sai ka bibiye shi, kana da damar dakatar da bibiyar ma da ya yi maka idan baka buƙata, musamman idan ka fahimci cewar bibiyar taka da ya yi ba ka da wani haɗi ko kasuwanci da shi, ko ka fahimci cewar macuci ne, wanda yake son yin amfani da wannan damar domin ya cutar da kai. To za ka iya rufe shi domin kada ya ga posts ɗin da kake yi, ko kuma don kada ya ci gaba da bibiyar ka.

Following:

Wannan wata hanya ce ta bayar da damar ka bibiyi wani domin ganin irin abubuwn da yake aiwatarwa a kan shafinsa na Twitter . Domin bibiyar mutane da kamfanoni musamman idan kana da buƙatar sanin abubuwa daga gare su.

Handle:

Wannan shi ne sunan da kake amfani da shi, wanda ana iya gane shi ne kuwa ta hanyar ganin alamar @. Misali @smart_Rogo wanda shi @smart_Rogo. Shi ne sunan da ni kaɗai ke amfani da shi a shafin Twitter, kuma idan ka sanya wannan sunan ni kaɗai za ka gani, haka kuma sanya wannan alamar shi ke nuna sahihancin

sunan me amfani da wannan shafin.

Hashtag:

Wata kalma ce dake da alamar # (misali #gtechhausa) wanda akan yi amfani da wannan domin samun haɗakar bayanai ga wannan mahaɗar, domin dukkanin wanda ya yi rubutu na wani bayani, sai ya yi amfani da #gtechhausa, to kuwa zai ga bayanin wani ma da ya yi amfani da wannan alamar ko kalmar a ƙarshen rubutunsa ko a ina yake a duniya, wanda ana iya amfani da wannan kalma ta Hashtag a taruka da dama, da gidajen TV da kuma gurin wasanni da makamantan su. Wanda da wannan hanya ne Twitter za ta ba ka damar haɗa dukkanin bayanai guri ɗaya, musamman idan aka yi amfani da Hashtag iri ɗaya.

Lists:

Wannan wani tsari ne na haɗa jerin sunayen mutanen da kake bibiya a Twitter domin ware muhimman mutane daga cikin jerin waɗanda kake bibiya. Wanda wannan yana iya zama abokanka na karatu, ko abokan wasa, ko kuma waɗanda kuke jaha ɗaya da makamantan su, domin samun tattaunawa ta musamman a kan abin da ya shafe ku.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Dawo Da Transfer Pin Na MTN Network Da Aka Manta Danna nan.

labarin da ya wuceYadda Za Ka Yi Amfani Da Keyboard Ɗinka A Matsayin Mouse
Labarin na GabaMece Ce Kwamfuta?
Engr. Suleiman Musa Abdullahi
Dalibi daga Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria Wanda na karancin bangaren addinin musulunci da koyar dashi a matakin farko, sannan na canja zuwa ga karatun fasahar sadarwar zamani Inda na halarci kasashe daban-daban India,Ghana, Africa ta kudu da Uganda domin samun horo da ha66aka karewa ta a bangarororin fasahar sadarwar da dangogin ta, ciki harda bada tsaro ga bayanai da binciken kwafkwaf da Na'ura domin bincikar masu laifi don samun hujjar gabatarwa a gaban kotu.