MyMTN APP: Yadda Ake Amfani Da MyMTN App Domin Gano Wasu Muhimman Bayanai A Kan Layinka Na MTN

0
337

Wannan wani masarrafi ne wanda kamfanin sadarwa na MTN ya samar wa abokan hurɗarsa domin aiwatar da wasu ayyuka na musamman, domin daɗa ba su damar sani da fahimtar bayanai a kan layukansu na sadarwa. Yana da amfani matuƙa, bayan ka san bayanai a kan layinsu na sadarwa, a ce ka san yadda masarrafin MyMTN App yake. Ga bayanin nan daki-daki a ƙasa a sauƙaƙe:

Yadda Masarrafin Yake:

Shi dai wannan masarrafi sunansa shi ne MyMTN App kuma ana iya sauke shi daga kasuwar hada-hadar masarrafai ta kamfanin Google wato Google Playstore wanda da zarar ka ɗauko shi (MyMTN App) sai ka sanya shi a wayarka, ma’ana ka yi (installing), bayan ka yi installing ne zai ba ka damar ka sanya lambar wayarka don yin rijista (register).

Sai ka sanya lambar wayarka domin tabbatar da buƙatarka, wanda da zarar ka sanya lambar wayar taka, wani saƙo nan take mai suna (OTP=One Time Password) lambar sirri ta lokaci guda, zai shiga cikin wayar da aka sanya lambar ta a cikin wannan masarrafi, sai a ɗauko wannan lambar a sanya ta a cikin gurin da shi wannan masarrafin ya bukata kamar yadda yake a hoton da yake ƙasa.

Da zarar ka gama da rijista, sukan bayar da kyautar 500MB.

Da zarar an sanya cewa, an amince da ya buɗe, wanda hakan zai bayar da damar ka ga abubuwa kamar haka:

1. Cikakken sunan da aka yi rijistar layin da shi.
2. Tsarin da layin ka yake kai.
3. Yawan adadin kudin kiranka.
4. Tarihin kiraye-kirayen layi.
5. PUK lambarka ta layi.
6. Bayar da damar shigar da akwatin sako na Email.
7. Bada damar sayen kati ko data daga bankinka, sannan suna ba da damar saka wa wani kati a layinsa.
8. Sanya hoto domin daɗa tabbatarwa.

Wannan shi ne cikakken bayani a kan yadda ake amfani da MyMTN App a sauƙaƙe.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Amfani Da Status Saver Na Whatsapp danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Addu’ar Ganin Jinjirin Wata
Labarin na GabaYadda Ake Buɗe Modem Ya Yi Aiki Da Kowanne Irin Layi
Engr. Suleiman Musa Abdullahi
Dalibi daga Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria Wanda na karancin bangaren addinin musulunci da koyar dashi a matakin farko, sannan na canja zuwa ga karatun fasahar sadarwar zamani Inda na halarci kasashe daban-daban India,Ghana, Africa ta kudu da Uganda domin samun horo da ha66aka karewa ta a bangarororin fasahar sadarwar da dangogin ta, ciki harda bada tsaro ga bayanai da binciken kwafkwaf da Na'ura domin bincikar masu laifi don samun hujjar gabatarwa a gaban kotu.