Yadda Ake Buɗe Modem Ya Yi Aiki Da Kowanne Irin Layi

0
256

Modem: Barkan ku da warhaka, ‘yan uwa daliban ilimin fasaha, yau na zo muku da sabon bayani a kan yadda ake buɗe modem ya yi aiki da kowanne irin layi(sim).

Wanda bayan ka buɗe shi kana da damar sanya dukkanin layin daka ga dama a ciki, domin yin aiki da shi.

Haka kuma, da yawa wasu sukan bada kuɗaɗe masu yawa wajen ganin sun aiwatar da wannan aiki.

Amma a wasu lokutan ba a da buƙatar sai an buɗe shi da mabuɗin lambar buɗewa, sai dai a ɗan yi wasu saite-saite kamar yadda zai zo a ƙasa, misali wajen chanja setin na APN, misali idan kana da modem na kamfanin Airtel, sai ka bi wadannan matakai domin saita shi ya yi aiki da layin MTN ko wani layin.

  • A buɗe cikin Airtel Setting wizard.
  • A je cikin Configuration Setting sai ka zaɓi APN.
  • Sannan a chanja sunan APN (misali idan kana son ka sanya layin da ba na Airtel ɗin ba sai ka chanja airtelgprs.com zuwa ga mtngprs, ko makamantan sa).
  • Sai a ajiye Settings ɗin.

Yanzu sai mutum ya yi connecting ɗin modem nasa zai ga ya yi connecting (wanda wannan yana aiki a cikin modem na Airtel ne kawai – Huawei E1731).

Hanya Ta Biyu Da Ake Amfani Da Ita Wajen Bude Modem

Yadda ake yi shi ne, a sami masarrafin (software) na UNIVERSAL MASTER CODE GENERATOR, wanda da yin amfani da wannan za a iya buɗe ZTE, NEC, LGkg110, Nokia, Huawei, VK ne kaɗai.

Idan ana son a bude daya daga cikin wadannna modem din, sai a bi matakan da zasu zo, a kasa.

1. Ɗauko Universal Master Code Software.(za ka iya sauke wanann masarrafin daga kan wannan link din. http://www.opendrive.com/files/12363728_miv7O_b84d/UniversalMasterCode.zip ).

2. Mataki na 2 -> Bayan an ɗauko wannan software ɗin sai a danna kansa sau biyu, wanda ba ya buƙatar wani installation. A duba hoton dake kasa za a ga yazo kamar yadda yake a hoton nan.

3. Shigar da nambar IMEI number, wacce tazo a jikin modem din.

4. Yanzu sai ka dannan kan Calculate; zata kirga maka nambar budewar UNLOCK code da kuma nambar sharewa FLASH code.

Abin Lura:

Bayan an ƙirga nambar buɗewar Unlock code da kuma nambar sharewa flash code; sai ka sanya wani layin da ba na wannan modem ɗin ba, misali idan modem ɗin na MTN ne sai ka sanya layin GLO ko wani layin daban; bayan ka jona moden ɗinka da computer naka ka sanya shi, zai tambaye ka, ka sanya nambar buɗewar kodai Unlock code ko Flash code, sai ka sanya ɗaya daga cikin abun da ya tambaya, sai ka yi connecting da yanar gizo-gizo, wasu lokutan kuma wasu modem ɗin ba sa buɗuwa da wannan tsarin, sai dai da wata hanyar ta daban.

Domin karanta cikakken bayani a kan Menene Shafin Blog danna nan

labarin da ya wuceMyMTN APP: Yadda Ake Amfani Da MyMTN App Domin Gano Wasu Muhimman Bayanai A Kan Layinka Na MTN
Labarin na GabaYadda Ake Raba Hard Disk Gida Biyu (Partition)
Engr. Suleiman Musa Abdullahi
Dalibi daga Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria Wanda na karancin bangaren addinin musulunci da koyar dashi a matakin farko, sannan na canja zuwa ga karatun fasahar sadarwar zamani Inda na halarci kasashe daban-daban India,Ghana, Africa ta kudu da Uganda domin samun horo da ha66aka karewa ta a bangarororin fasahar sadarwar da dangogin ta, ciki harda bada tsaro ga bayanai da binciken kwafkwaf da Na'ura domin bincikar masu laifi don samun hujjar gabatarwa a gaban kotu.