Tag: Ilimin kimiya da fasaha

  • Yadda Za Ka Kare Facebook Ɗinka Daga Hackers

    Yadda Za Ka Kare Facebook Ɗinka Daga Hackers

    Assalam alaikum, barka da wannan lokaci. Duba da irin matsalolin da ake samu a shafukan sada zumunta; musamman shafin Facebook da Instagram, ta yadda wasu ɓata-gari ke amfani da basira wajen ƙwace asusun ɗin mutane domin su damfari bayin Allah.

    Mutane da yawa na kukan an ƙwace musu Facebook account, an chanja musu suna, an cire bayannansu, an ɗora na wasu; kuma ba su san dalilin yin hakan ba.

    Wannan yasa naga ya dace, na yi wa ƴan’uwa bayanin yadda za su kare kansu, don gudun faɗawa komar kifi, ta yadda babu wanda ya isa ya yi maka hacking account ɗinka na Facebook ko Instagram, ba tare da izininka ba, ko da ya san password ɗinka.

    2FA (Two Factor Authentication)

    Akwai abin ake kira Two Factor Authentication; wani Security ne wanda ake kunnawa, akwai shi a cikin mafi yawan shafukan sada zumunta, wanda idan ka kunna shi; ɓarawon account ba zai samu damar yi maka hacking ba, ko da ya san password ɗinka. Abin da 2FA yake nufi shi ne, mukulli na biyu wanda zai tabbatar da kai ne mai wannan shafin, a duk lokacin da ake je yin Login (shiga).

    Duk lokacin da wani ya yi ƙoƙarin shigar da bayanan Account ɗinka, domin ya buɗe; idan ka kunna #2FA za a tura maka saƙo da lambobin sirri a cikin wayarka ko email ɗinka; ya danganta da wanda ka zaɓa, dole sai an shigar da su sannan wannan Account zai buɗe.

    Yadda Ake Kunna 2FA A Facebook

    Da farko za ka shiga cikin #Settings a cikin facebook, sai ka shiga ‘Security and Login’; a ciki za ka ga inda aka rubuta “Two Factor Authentication”; sai ka shiga ciki, za ka ga “Your Security Method” sai ka shiga, zai nuna maka inda za ka shigar da lambar wayarka, wacce za a dinga tura maka saƙo akan ta; sai ka saka Password na Facebook ɗinka, za su nuna maka “Two Factor Authentication is active” shi kenan, komai ya yi daidai.

    Note!!!

    Ya kamata ka shigar da number da ka san kai ne ka yi registration na layin; saboda ba za ka iya Login Facebook ba, sai wannan layin yana cikin wayarka, saboda halin faɗuwar waya, Allah ya kare. Kar ku manta da yi wa ‘yan’uwa sharing saboda kowa ya ƙaru.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Amfani Da Kafar Sadarwa Ta Whatsapp danna nan.

  • Yadda Ake Dawo Da Abin Da Aka Goge A Kan Komfiyuta

    Yadda Ake Dawo Da Abin Da Aka Goge A Kan Komfiyuta

    Mafi yawancin dukkanin wani abu da aka goge a kan komfiyuta ba wai an goge shi ne ba gaba ɗaya; mafi yawanci yana zuwa cikin wata ma’ajiyar datti ne; wanda ake kira da “recycle bin” a Turance; wani kuma ta wajen gogewa ake sa shi, a tsarin da idan an goge ba ya shiga wanann ma’ajiyar dattin (Recycle Bin).

    Shin ko ka taɓa goge wani abu daga komfiyutarka ba tare da kana son ka goge shi ba ? kuma kana bukatar ka dawo da shi, sannan kuma ba ka gan shi a cikin ma’ajiyar datti ba (recycle bin) wanda ta yiwu ka goge shi ne ta yin amfani da shift+delete ko kuma ka zazzage ma’ajiyar datti (emptied recycle bin) . Sabo da haka kada a damu, hakan yana iya yiwuwa domin ana dawo da irin wannan abin da aka goge.

    A wannan bayanin za a kawo yadda ake dawo da abubuwan da aka goge ta hanyar amfani da wasu massarafai da aka samar domin aiwatar da irin wannan aiki.

    Mafi yawanci duk wani file da aka goge a kan komfiyuta, ba wai ya goge daga kan kwakwalwar komfiyuta ba ne (hardrive) yana samun wani guri ne ya shiga, inda ba zai zama mai nauyi ba sabo da an nuna ba shi da muhimmanci, to zai je nan ya tsaya jiran ko za a iya dawo da shi, haka kuma zai ta zama ne har sai an sanya wani a madadin sa wanda zai cinye wannan guri da aka sanya wancan abin da aka goge na farko, a mafi yawancin kwakwalwar comoter ma ko an sanya wani ana iya dawo da shi.

    Akwai masarrafai (softwares) da yawa waɗanda ake amfani da su domin aiwatar da wanann aiki ga kaɗan daga cikin su:

    1. Tokiwa data recovery

    Wanna masarrafi bai wuce kimanin 200 kb ba, kusan ma shi ne masarrafi mafi ƙanƙanta/mafi ƙarancin nauyi wajen aiwatar da wannan aiki na dawo da abubuwan da aka goge, wanda yana ɗauko abubuwan da aka goge daga kan tsarin ƙwaƙwalwar da ke da FAT 12, FAT16, FAT32 da kuma NTFS file, haka kuma yana dawo da abin dake kan tsarin NTFS wanda aka yi compressed da kuma na kan EFS encrypted file. Haka kuma wannan masarrafi yana taimakawa wajen dawo da su ba tare da an sha wahala ba, haka kuma da wannan masarrafin za a iya goge abin da ba a buƙatar sa har abada.

    2. Pandora recovery

    Ita ma wannan wata massarrafar ce (software) dake bayar da damar yin wannan aiki da muka faɗa a baya, wanda a nan ita tana ba da cikakkiyar dama wajen gani ka nemi irin abin da kake so ka dawo da shi, ko kuma file na abin da kake son ka dawo da shi, haka kuma zai ba ka damar nemo wata hanyar amfani da sunan file naka da kake nema, musammam wanda ka san sunansa, ko kuma ranar da ka yi aikin,

    Haka kuma, yin amfani da wannan hanyar ba ya iya nuna maka asalin inda aikin yake, yana nuna maka aikin ne kawai da aka goge daga kan computer, musamamn daga inda ake ganin ya lalace , ko kuma ake ganin kamar ba zai dawo ba, ko kuma aka yi formated gaba ɗaya, haka kuma yin amfani da wannan hanya ba wai sai a kan ƙwaƙwalwar komfiyuta kaɗai yake aiki ba, za ka iya dawo da abin dake kan CDs da kuma DVDs.

    3. Recuva:

    Wannan ma wani masarrafi ne mai saukin aiki, wanda yake aiwatar da irin aikin da muka yi bayanai a baya , wanda shima yana ba ka damar ka yi serch ne na abin da kake son ka dawo da shi, ta yin amfani da sunan file misali, Waƙoƙi ne , hotuna, rubuce-rubuce ko kuma wasu abubuwa makamantan waɗannan kamar hoto mai motsi (vidios) haka kuma yana iya ba ka damar neman abin da ya daɗe , da gogewa, kamar yadda waɗanda suka gabata suke aiwatar da nasu aikin, haka kuma wannan masarrafin yana da versioin kala-kala sai wanda ka ga zai iya yi a kan computer naka, sannan za ka ɗauko domin amfani da shi.

    Haka kuma dukkanin waɗannan massarafi da ma wasu da ba aka kawo a nan ba, suna aiki ne wajen dawo da abin da aka goge daga kan memory na waya ko na kan computer , ko kan camera, ɗaukar hoto, haka kuma yana dawo da dukkanin hotuna, video, Waƙoƙi , rubutattun ayyuka daga kan tsarin FAT da kuma NTFS wanda aka yi formating , sanna kuma ana iya amfani da su a kan tsarin massarfin komfiyuta na win xp, win vista win 7,8,8.1 da kuma win 10.

    Hanyoyin Da Ya Kamata A Bi Wajen Samun Damar Dawo Da Abin Da Aka Goge

    1. Idan aka goge wani abu bisa rashin sani daga kan wata ma’ajiya, a tabbatar ba a sanya wani abu ba a kan inda aka goge wannan ma’ajiyar, misali abin da zai iya zama ya shige gurin da ka goge wancan bayanan, wanda in ya shiga gurin wanda aka goge hakan ba zai sami damar dawo da abin da aka goge ba kasancewar wanda aka sanya daga baya ya rufe gurin wancan da aka goge, hakan kuma zai iya hana dawo da wancan da aka goge.

    2. Idan ka yi ƙoƙarin dawo da abin da ka goge sai hakan ya gagara, hakan ba yana nuna abin ba zai yiwu ba ne, abin yi a nan shi ne, ka nemi wani kalar masarrafin wanda zai maka wannan aiki, ta yiwu wannan wanda kake da shi shi ne ba zai iya aiwatar da aikin ba.

    3. Idan ka goge abu a kan computer naka da kake aiki da shi, yi ƙoƙari kada ka sanya wani abu a kanta, sai dai kawai in kana da filin da za ka ɗauko ɗaya daga cikin massarrafan da suke taimakawa wajen dawo da abin da aka goge, sai ka ɗauko domin aiwatar da wannan aiki, bayan ka gama, sai ka kashe komfiyuta sannan ka kunna sai ka fara aiwatar da aikin dawo da abin da ka goge.

    Haka kuma yana da kyau ya zama kana da waɗannan masarrafan a cikin wata ma’ajiya taka ta musammamn “flash drive” , ko da za ka goge wani muhimmin abu bisa kuskure.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Za Ka Dawo Da Martabar Batirin Wayarka danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Komfiyuta (Computer) danna nan.

  • Mene Ne Shafin Blog

    Mene Ne Shafin Blog

    Blog wani shafi ne da ake buɗewa domin ilmantar da al’umma wani ilmi na daga mai shi wannan shafin; ko kuma tunasarwa a kan abubuwan da suke faruwa a tsakanin al’umma, hakan nan kuma yana a matsayin wata kafa ta yaɗa labarai da tallace-tallace.

    Abubuwan Da Za a Tattauna:-

    A. Menene Blog.
    B. Matakan da ake bi wajen samar da shafin na Blog
    C. Muhimmancin shafin Blog.
    D. Yadda ake amfani da shafin Blog.

    A. Ma’anar Blog:

    Blog wani shafi ne da ake buɗewa domin ilmantar da al’umma wani ilmi na daga mai shi wannan shafin; ko kuma tuna sarwa a kan abubuwan da suke faruwa a tsakanin al’umma, hakan nan kuma Blog na matsayin wata kafa ta yaɗa labarai da tallace-tallace.

    B. Matakan Da Ake Bi Wajen Buɗe Shafin Blog

    Matakin Farko: Zuwa Shafin Domin Yin Rijistar (create your Blog now)

    Ka shiga adireshin samar da shafin na http://www.Blogger.com sai ka je inda aka ce create your Blog now; ma’ana ka bude shafinka na Blog yanzu. Sai ka cike sunan da kake son Blog naka ya zama, amma ya zama babu mai irin shi. Haka kuma wannan suna shi ne sunan da zai ba ka damar shiga shafin naka duk san da kake so.

    Mataki Na Biyu: Zaɓar Kalmar Sirri (select a password)

    Sai ka zaɓi lambar sirrinka wato password wanda kake buƙatar ya zama, wanda wannan lambar sirrin ”password” yana kamawa daga alamomi guda shida zuwa sama da haka; amma akwai buƙatar wajen sanya lambar sirrin ”password” ya zama haɗakar baƙaƙe: lambobi, da kuma wani abin da ba kowane zai iya ganowa ba.

    Haka kuma ya zama ka sanya lambar sirrin da za ta yi wahalar ganowa ga wasu, amma mafi sauki a gare ka wajen tunawa.

    Mataki Na Uku: (Select a Display Name)

    Sai sunan da zai zama na Blog naka, ma’ana DISPLAY NAME; wanda da wannan sunan ne za ka iya amfani da shi wajen shiga ka yi rubutunka domin ƙaruwar waɗanda kake so su amfana.

    Abin Lura:

    Wajen zaɓar sunan, yana da kyau ka zaɓi sunan da zai kare mutuncin kanka, kuma ya zama babu mai irin sa; domin yin rijista a shafin internet idan da wanda ya riga ka buɗewa da irin wannan sunan; kai sai dai ka nemi wani sunan ko kuma bayan kasanya sunan sai ka sanya wata alama da za ta nuna kai ne ba wancen na farkon ba.

    Haka kuma, wannan suna shi ne sunan da zai ba ka damar shiga shafin naka duk san da ka so. Sannan yana da kyau ka sanya sunan da ba zai yi wahalar nema ba.

    Mataki Na Huɗu : (enter an email address)

    Sai ka sanya email address naka, wanda yana da matuƙar muhimmancin sa shi, kasancewar ma idan babu shi rijista ba ta yiwuwa, wanda daga baya ma za ka iya canja wannan email din; domin idan ya zama ya lalace ko ya sami matsala. Haka kuma wannan email, ba zai nuna ba a shafinka na Blog, sai in ka so; domin boyewar zai taimaka maka ka sami tsaro daga masu kutse/mafasa. Bayan ka kamala wannan sai ka karanta dukkanin tsare-tsaren da suke bada damar buɗe shafin Blog; ”read terms of services” kafin ka danna zuwa gida na gaba, wato “continue”.

    Mataki Na Biyar: Bawa Blog Naka Tittle (Give your blog a tittle)

    Wannan shi ne wani suna ko alama da zai ba ka damar ya fito a saman dukkanin wani rubutu da za ka yi; a kan kowanne shafi, sai dai ya danganta da rubutun da za ka yi, kuma ya zama ka canja.

    Mataki Na Shida Zaɓar Adireshinka Na Blog: (choose a web address to your blog)

    A wannan guri zai ba ka damar zaɓar adireshin da zai yi sauƙi wajen samun ka a shafin Blog; wanda kuma zai bayyana ga ma’abota shiga shafin.

    Misali http://yourblogspacename.blogspot.com, da ga wannan sai zaɓar tsarin da blog naka zai zama domin kayatarwa wato “template” kada a zaɓi dukkan abun da aka gani wajen zaɓe a nutsu wajen zaɓin; domin samar da kalar da masu bibiyar shafin za ta ƙayatar da su. Domin zai iya ba ka damar canjawa daga baya a cikin jerin saiti na shafin. Da zarar ka kamala wannan to shafin ka na blog ya buɗu.

    C. Muhimmancin Shafin Blog

    Dangane da bayannan da ya gabata, a kan mene ne Blog kuma ya ake buɗe shi, ku san dai yana da matuƙar muhimmanci musammam ga, masu san su yaɗa wasu bayanai da jama’a za su amfana, haka kuma yana da matuƙar muhimmanci ga ‘yan Kasuwa da kuma ɗaliban ilmi dama sauran al’umma masu san ci gaba ta hanyar amfani da yanar gizo wato “internet” a Turance.

    D. Yadda Ake Amfani Da Shafin Blog

    Da zarar ka samar da wannan shafi na blog domin watsa rubututtukanka. Shi kenan sai farawa, yadda ko za ka fara shi ne :
    Bayan ka buɗe shafin naka, sai ka shiga “start posting” inda a nan ne za ka sami damar tsara rubutunka da kuma watsa shi. Shirya tsari mai ƙayatarwa domin jan hankali wato “tittle”; sai ka rubuta rubutun ka haɗi da cika ka’idojin rubutu domin mai karatu ya fahimta.

    Sannan bayan ka kamala sai ka dannan kan “publish post” da hakan shi zai ba ka damar rubutunka ya tafi duniya kuma ya zama duk wanda ya bi cikin internet a kan abu makamancin naka; to zai ba shi damar ganin rubutun tare da saƙon da kake son isarwa.

    Haka kuma, idan kana buƙatar wani ya je ya karanta sai ka gaya masa “tittle” na saƙonka; ko rubutunka wanda da zarar ya bincika zai samu.

    Duk lokacin da ka sanya sabon rubutu a kan Blog naka, yana da kyau ka watsa shi domin amfanuwar mutanen da kake so su amfana, saboda haka wasu ma idan suka nemi makamancin abin da ka sanya za su gani su ƙaru .

    Domin neman Karin bayani za ku iya samu na a 08087633060.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Ya Kamata Ka Sani Dangane Da Twitter danna nan

  • Abubuwan Da Ya Kamata Ka Sani Dangane Da Twitter

    Abubuwan Da Ya Kamata Ka Sani Dangane Da Twitter

    Twitter: Shi wannan shafin sadarwar mai suna Twitter na ɗaya daga cikin shafukan tattaunawa da muhawara, kamar yadda sauran shafukan suke, haka kuma, Twitter tana da yare nata na kanta, waɗanda waɗansu abubuwa ne da ya kamata a sani dangane da Twitter, domin sanin su tamkar fitila ce wadda za ta haska maka hanyar damar yin amfani da Twitter ba tare da wata matsala ba. Domin idan ka san yadda ake amfani da Twitter musamman wajen kasuwanci; sanin waɗannan zai ƙara ba ka damar bunƙasa kasuwancinka. Idan kuma ba ka da Twitter a kan wayarka, za ka iya shiga Google Play Store play.google.com ka sauke manhajar.

    DM/Direct Message:

    Wani saƙo ne na sirri da ake turawa tsakanin ka da wanɗanda kake son yin magana da su kai tsaye. Haka kuma, shi ma wanda ya karɓi saƙon yana da damar ya turo maka nasa saƙon da bai wuce harufa 140 ba, koda kuwa ba ya cikin jerin abokanka ko mabiyanka a shafin Twitter ɗin.

    Follow:

    Hanya ce da take haɗa mutane a shafin Twitter. Haka kuma, mutanen da ka zaɓi ka bibiye su, su ma za su iya ganin abubuwan da kake sanyawa a kan shafinka na Twitter. Haka kuma ba dole ba ne ba cewar wani ya bibiye ka, kai ma ka ce lalle sai ka bibiye shi, kana da damar dakatar da bibiyar ma da ya yi maka idan baka buƙata, musamman idan ka fahimci cewar bibiyar taka da ya yi ba ka da wani haɗi ko kasuwanci da shi, ko ka fahimci cewar macuci ne, wanda yake son yin amfani da wannan damar domin ya cutar da kai. To za ka iya rufe shi domin kada ya ga posts ɗin da kake yi, ko kuma don kada ya ci gaba da bibiyar ka.

    Following:

    Wannan wata hanya ce ta bayar da damar ka bibiyi wani domin ganin irin abubuwn da yake aiwatarwa a kan shafinsa na Twitter . Domin bibiyar mutane da kamfanoni musamman idan kana da buƙatar sanin abubuwa daga gare su.

    Handle:

    Wannan shi ne sunan da kake amfani da shi, wanda ana iya gane shi ne kuwa ta hanyar ganin alamar @. Misali @smart_Rogo wanda shi @smart_Rogo. Shi ne sunan da ni kaɗai ke amfani da shi a shafin Twitter, kuma idan ka sanya wannan sunan ni kaɗai za ka gani, haka kuma sanya wannan alamar shi ke nuna sahihancin

    sunan me amfani da wannan shafin.

    Hashtag:

    Wata kalma ce dake da alamar # (misali #gtechhausa) wanda akan yi amfani da wannan domin samun haɗakar bayanai ga wannan mahaɗar, domin dukkanin wanda ya yi rubutu na wani bayani, sai ya yi amfani da #gtechhausa, to kuwa zai ga bayanin wani ma da ya yi amfani da wannan alamar ko kalmar a ƙarshen rubutunsa ko a ina yake a duniya, wanda ana iya amfani da wannan kalma ta Hashtag a taruka da dama, da gidajen TV da kuma gurin wasanni da makamantan su. Wanda da wannan hanya ne Twitter za ta ba ka damar haɗa dukkanin bayanai guri ɗaya, musamman idan aka yi amfani da Hashtag iri ɗaya.

    Lists:

    Wannan wani tsari ne na haɗa jerin sunayen mutanen da kake bibiya a Twitter domin ware muhimman mutane daga cikin jerin waɗanda kake bibiya. Wanda wannan yana iya zama abokanka na karatu, ko abokan wasa, ko kuma waɗanda kuke jaha ɗaya da makamantan su, domin samun tattaunawa ta musamman a kan abin da ya shafe ku.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Dawo Da Transfer Pin Na MTN Network Da Aka Manta Danna nan.

  • Yadda Za Ka Yi Amfani Da Keyboard Ɗinka A Matsayin Mouse

    Yadda Za Ka Yi Amfani Da Keyboard Ɗinka A Matsayin Mouse

    Sau da yawa wasu sukan samu matsala da manunin kwamfutarnsu, wato “mouse”

    To daga lokacin da mouse ɗinka ya daina, a lokacin da za ka yi amfani da shi, to sai ka mayar da keyboard ɗinka ya zama kana iya aiki biyu da shi, ya yi aikinsa na keyboard sannan ya yi kuma na mouse.

    Yadda za a yi kuwa shi ne abi waɗanann matakan:

    • Sai ka yi amfani da Alt+Shift na hannun hagu +number lock sannan a danna Enter Key.
    • Sai a yi amfani da lambobi don gabatar da aikinka misali;

    Danna lamba 5 Yana matsayin Click

    Ko ka danna alamar + Yana matsayin Double click

    Ko kuma ka danna alamar – Yana matsayin Right click

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Za ka Lalata Wayarka Idan Ta Ɓata danna koren rubutun nan

  • Yadda Za Ka Dawo Da Martabar Batirin  Wayarka

    Yadda Za Ka Dawo Da Martabar Batirin Wayarka

    Idan battery na wayarka ya yi ƙasa ko ma ya ƙare gaba ɗaya…

    Za ka ji idan kuma ka ɗan sanya batiri a kan harshenka kana jin wata wuta;

    To ita wannan wutar ko ka taɓa tambayar kanka cewa ta mece ce?

    Wannan shi yasa aka gabatar da bincike, aka gano cewa a kowanne battery akwai ɓoyayyar wuta wacce kasonta ya kai 50% cikin 100%. Haka kuma, za ka iya dawo da martabarsa da kaso 50% cikin 100% ta hanyar yin amfani da wata fasahar zamani ta wasu lambobi ta hanyar dannan *3370#, sai ka tura, ka ɗan jira na ɗan wani lokaci.

    Martabar batirinka za ta dawo da wancan kaso da na faɗa na 50% bayan ta kashe kanta ta kunna.

    Abin Lura

    Wannan lambobi (code) yana amfani ne kawai musamman ga wayoyi kirar Nokia da wasu kuma kaɗan da ba Nokia ba;

    Sai a kula.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda za ka Dakatar Da Kowanne Irin Kira Wayarka danna nan

  • Yadda Ake Duba Rijistar Layin Waya

    Yadda Ake Duba Rijistar Layin Waya

    Mafi yawa daga cikin ma’abota amfani da layukan waya; ba su san yadda ake gano layin nada rijista ba ko akasin haka.

    Haka ba su san yadda ake amfani da waɗansu lambobi ko kuma hanyoyi ba, wajen duba Rijistar layikansu;

    Domin sanin cewar layukan nasu nada rijista ne ko babu.

    A wannan ɗan taƙitaccen bayani, za a sanar da al’umma yadda ake duba rijistar kowanne layi kamar haka:

    • Yadda Ake Duba Rijistar Layin MTN

    Domin duba rijistar layin MTN sai ka shiga wajen da ake rubuta saƙo, ka rubuta kalmar REG sai ka tura zuwa ga 789, da zarar saƙon ya je, za ka ga sun turo maka da wani saƙo wanda ke ɗauke da bayanin cewa rijistarka ta yi, ko kuma ba ta yi ba.

    • Yadda Ake Duba Rijistar Layin GLO

    Shi ma wannan kamar wancan na baya ne, domin duba rijistar layin, sai ka je wajen rubuta saƙo, ka rubuta kalmar REG sai ka tura zuwa ga 3456, da zarar saƙon ya je, za ka ga sun turo maka da wani saƙo wanda ke ɗauke da bayanin cewa rijistarka ta yi, ko kuma ba ta yi ba.

    • Yadda Ake Duba Rijistar Layin Etisalat/9Mobile

    Shi ma layin Etisalat ana iya duba rijistarsa ta yi; ko kuma ba ta yi ba ta hanya biyu. Wanda hanyar farko ita ce: A kira lambar kulawa da abokan hulɗa, wato customer care number a kan 200.

    Ko kuma a tura musu saƙon neman sanin rijistar layi ta akwatun email kamar haka: care@etisalat.com.ng; bayan wasu ‘yan lokuta za su dawo da saƙon sanin matsayin rijistar na cewar; ta yi ko kuma ba ta yi ba.

    • Yadda Ake Duba Rijistar Layin Airtel

    Shi ma wannan kamar sauran ne da suka gabata a baya. Domin duba rijistar layin sai rubuta *746# sai ka tura.

    Da zarar ya je ya dawo; za ka ga sun turo maka da wani saƙo wanda ke ɗauke da bayanin cewa; rijistar ka ta yi, ko kuma ba ta yi ba.

    Haka kuma, za a iya kiran lambar kulawa da aboka nan hulɗa, wato customer care number akan nambar 111 ko kuma a tura da saƙon neman sanin rijistar ta akwatin saƙon email na customercare@ng.airtel.com.

    Domin karanta Yadda Ake (Recording) Ɗaukar Videon Abin da Kake Gabatarwa A Fuskar Computer danna nan

  • Yadda Ake Samar Da Website Na Kyauta Ta Hanyar Amfani Da Google Site

    Ka san kuwa za ka iya samar da haɗaɗɗe da ƙayataccen shafin yanar gizo, kuma mai sauƙin aiki ta hanyar yin amfani da shafin Google?

    Google Site wata mahaɗa ce mai sauƙi kuma mara wahalar aiki, wacce za ta samar maka da ajiyayyen shafin internet kyauta.

    Musamman idan kai ɗan ƙaramin ɗan kasuwa ne, kuma ba ka da damar gina babban shafi domin tallata kayanka;

    Googe site zai ba ka damar yi ko da kuwa ba ka da ilmin sanin harsunan kwamfuta wato “Programming Languages”.

    Ko sanar da mutane ya kasuwancinka yake.

    Ga kaɗan daga cikin hanyoyin da ake bi domin aiwatar da Website a Google Site:

    Mataki Na Ɗaya

    Ziyarci https//sites.google.com/ sai ka shigar da Account ɗinka na Google zai ba ka damar ya zama shi ne kamar jigon shafinka wajen shiga domin aiwatar da gyara ko kuma wani abu makamancin haka.

    Mataki Na Biyu

    Sai ka danna kan red box, wanda yake nuna ka samar “Create,” za ka gan shi daga sama a hannun hagu na shafin. Waɗansu bayanai za su buɗe nan take.

    Mataki na Uku

    Sai ka zaɓi “New Sites” wani ɓangaren zai buɗe maka domin ya ba ka damar gyara shafinka.

    Idan ka danna kan “Your page title” sai ka canja rubutun da sunan shafin da kake son buɗewa, nan take zai buɗe maka kuma zai zama mai rai akan shafin na google, ba tare da ka rufe shafin ka ƙara buɗewa ba, nan take shafin zai buɗe, haka kuma za ka iya buɗe shi a wani gun domin ganin sa.

    Mataki Na Hudu

    A ɓangaren hannun dama, a inda sidebar yake, click the “THEMES” tab and select the option you would like to use. In your selected option, you choose the color and font you would like to use for your website.

    Mataki Na Biyar

    A jikin inda zai buɗe maka wajen sidebar, sai ka buɗe “INSERT”. Za ka iya ganin dukkanin saitin da kake buƙata.

    Haka kuma, za ka iya turawa zuwa ga wasu, domin su san cewa ka buɗe shafin ‘content in this sidebar’.

    Click the one you want and it will appear in the body of the page live, where you can edit the content.

    Want to move the item? Move your cursor to the left of it until it turns into a four-point of arrows. Then click, drag and drop it.

    Mataki Na Shida

    Once you are happy with the content and style of your website.

    Click the eye symbol at the top of the body of the page to preview how it will look.

    Mataki Na Bakwai

    Click the person symbol, also above the body, and choose others to appoint as editors by adding their email addresses and a message. Be sure to select “Send a copy to myself” for your records and then click “Save.” This is much safer than having everyone access the website as one user and access your sensitive email account.

    Mataki Na Takwas

    Under “Who can edit,” select “Change” to make the website public or choose another privacy option. Once you’ve made your option, click “Save”.

    Domin Karanta Cikakken Bayani A kan Tarihin Samuwar Shafukan Sada Zumunta danna koren rubutu

  • Yadda Za Ka Lalata Wayarka Idan Ta Ɓata

    Yadda Za Ka Lalata Wayarka Idan Ta Ɓata

    Dazarar wayarka ta ɓata, ko an sace,to tabbas kana da damar lalata wayar ta hanya mafi sauƙi kamar haka:

    Za ka yi hanzari ka nemi waya musamman Nokia 3310, sai ka shiga inda ake rubuta saƙo(messages);

    ka yi maza ka rubuta serial number na wayar, wanda ake kira IMEI number;

    Sai ka tura zuwa ga Emergency call number, ko kuma layin wayar da ta ɓace a ciki. Domin ganin IMEI number danna *#06#

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Duba Rijistar Layin Waya danna nan

  • Yadda Za Ka Dakatar Da Kowanne  Irin Kira Wayarka

    Yadda Za Ka Dakatar Da Kowanne Irin Kira Wayarka

    Idan kana ko kina son hana shigowar kira kowannne iri ne cikin wayarka a sakamakon wasu dalilai;

    Sai a yi amfani da waɗannan lambobi a kan layin wayar da ba a son kiran ya shigo**21*999999#;

    Sannan a danna madannin kiran waya wato (send), shi kenan wato duk wanda ya kira za a ce masa lambar da ya kira ba daidai ba ce (the number you call does not exist).

    Domin fita daga wannan tsarin sai a danna ##21# domin warwarewa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Za ka Lalata WayarKa Idan Ta Ɓace danna nan

    Don karanta bayani akan Yadda Za Ka Dawo Da Martabar Batirin Wayarka danna nan