Tag: Ilimin kimiya da fasaha

  • Kafar Sadarwa ta WhatsApp: Yadda Ake Amfani Da Kafar Sadarwa ta WhatsApp

    Kafar Sadarwa ta WhatsApp: Yadda Ake Amfani Da Kafar Sadarwa ta WhatsApp

    Kafar Sadarwa ta WhatsApp; Sau da yawa mutane na mu’amala da kafar social media ta whatsapp; amma akwai tarin abubuwa da ba su san yadda ake amfani da su ba yadda ya dace; ko kuma ba su san yadda za su aiwatar da wasu abubuwa ba. Ga waɗanda ba su da WhatsApp a wayarsu, za su iya hawa kan Google Play Store https://play.google.com/ su sauke shi.

    Waɗannan wasu kaɗan ne daga cikin irin abubuwan da ake iya aiwatarwa; wanda ba kowa ya sani ba a Kafar Sadarwa ta WhatsApp:

    • Tura Saƙo Guda Ɗaya Ga Mutane Da Yawa (Broadcasting)

    Wannan wata hanya ce da ake tura saƙo guda ɗaya zuwa ga mutane da yawa; da zarar ana son a yi wannan, sai a je kan MENU, inda ke da wasu alamomi guda uku. Sai mutum ya zaɓi Broadcast wanda a nan ne zai ba ka damar tura saƙon zuwa ga mutane da yawa; wanda idan za ka aiwatar da wannan, zai ba ka damar ƙara wanda za ka turawa ta hanyar zaɓar alamar + sai ka zaɓi sunan da za ka ƙara.

    • Sauya Nau’in Rubutu

    Wanna ma wata alama ce da za ka iya sauya nau’in rubutu; misali ya tafi a kwance ko kuma ya yi kauri ko ya zama a cikin alamar sokewa

    Domin tafiyar da rubutu a kwance sai a rubuta _rubutu_ sai a tura. Ø
    Domin sanya rubutu ya yi kauri sai a yi amfani da *rubutu* sai a tura.Ø
    Domin sanya alamar sokewa sai a yi amfani da ~rubutu~ sai a tura.Ø

    Domin Karanta Cikakken bayani a kan Yadda Ake Amfani Da MyMTN App Danna nan

  • Yadda Ake Horon Masu Yi Maka Flashing (ɗungushen kira) A Waya

    Yadda Ake Horon Masu Yi Maka Flashing (ɗungushen kira) A Waya

    Sau da yawa wasu na damuwa matuƙa dangane da yawan Gajeren kira (flashing) da ake musu; ba tare da sun san wanda yake musu gajeren kira (flashing) ba; haka kuma wasu mutane na amfani da wannan damar wajen takurawa rayuwar wasu; ta hanyar hana su sakewa a lokacin da suka ga dama, saboda damun su da gajeran kira wato (Flashing).

    Yanzu akwai hanyoyi da dama da ake bi domin horar da masu irin wannan hali na gajeran kira (flashing call); yadda ake yi shi ne, sai a danna wadannan lambobi: **21*174 sai lambar da ake yawan kiran naka da ita; sai a rufe da # misali: **21*1748133706929# sai a danna send.

    To daga nan da zarar mai wannan lambar ya kira ka; kamar yadda ya saba damun ka, to za a ɗaukar masa N30. Idan kuma kuɗin ba su kai haka ba, za a ɗauke su duka; idan kuma kana so ka cire shi, daga wannan tsarin, sai ka danna ##21#

    Abin Lura:

    Ba’a yin irin wannan, sai ga wanda ya takura maka da gajeren kira (flashing call), saboda haka, a kiyaye.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Za Ka Lalata Wayarka Idan Ta Ɓata danna nan

    Domin karanta bayani akan Asalin Samuwar Intanet danna nan