Yadda Ake Duba Rijistar Layin Waya

3
501

Mafi yawa daga cikin ma’abota amfani da layukan waya; ba su san yadda ake gano layin nada rijista ba ko akasin haka.

Haka ba su san yadda ake amfani da waɗansu lambobi ko kuma hanyoyi ba, wajen duba Rijistar layikansu;

Domin sanin cewar layukan nasu nada rijista ne ko babu.

A wannan ɗan taƙitaccen bayani, za a sanar da al’umma yadda ake duba rijistar kowanne layi kamar haka:

  • Yadda Ake Duba Rijistar Layin MTN

Domin duba rijistar layin MTN sai ka shiga wajen da ake rubuta saƙo, ka rubuta kalmar REG sai ka tura zuwa ga 789, da zarar saƙon ya je, za ka ga sun turo maka da wani saƙo wanda ke ɗauke da bayanin cewa rijistarka ta yi, ko kuma ba ta yi ba.

  • Yadda Ake Duba Rijistar Layin GLO

Shi ma wannan kamar wancan na baya ne, domin duba rijistar layin, sai ka je wajen rubuta saƙo, ka rubuta kalmar REG sai ka tura zuwa ga 3456, da zarar saƙon ya je, za ka ga sun turo maka da wani saƙo wanda ke ɗauke da bayanin cewa rijistarka ta yi, ko kuma ba ta yi ba.

  • Yadda Ake Duba Rijistar Layin Etisalat/9Mobile

Shi ma layin Etisalat ana iya duba rijistarsa ta yi; ko kuma ba ta yi ba ta hanya biyu. Wanda hanyar farko ita ce: A kira lambar kulawa da abokan hulɗa, wato customer care number a kan 200.

Ko kuma a tura musu saƙon neman sanin rijistar layi ta akwatun email kamar haka: care@etisalat.com.ng; bayan wasu ‘yan lokuta za su dawo da saƙon sanin matsayin rijistar na cewar; ta yi ko kuma ba ta yi ba.

  • Yadda Ake Duba Rijistar Layin Airtel

Shi ma wannan kamar sauran ne da suka gabata a baya. Domin duba rijistar layin sai rubuta *746# sai ka tura.

Da zarar ya je ya dawo; za ka ga sun turo maka da wani saƙo wanda ke ɗauke da bayanin cewa; rijistar ka ta yi, ko kuma ba ta yi ba.

Haka kuma, za a iya kiran lambar kulawa da aboka nan hulɗa, wato customer care number akan nambar 111 ko kuma a tura da saƙon neman sanin rijistar ta akwatin saƙon email na customercare@ng.airtel.com.

Domin karanta Yadda Ake (Recording) Ɗaukar Videon Abin da Kake Gabatarwa A Fuskar Computer danna nan

3 SHARHI

  1. Sharhi: Aslamu alaika bayan gaisuwa da fatan lana lafiya engr dan allah mekekawo idan nayi linking da ninmc number sai anuna min inbalid wato invalid yana numa min kamar batayiba nagode engr sulaiman abdullahi.