Tatsuniyar Gizo Da Giwa

0
556

Ga ta nan ga ta nan ku

Tatsuniya! Tatsuniya!! Tatsuniyar!!!

Tatsuniya! Wani mutum ne dai ya ba wani malami kuɗi don a yi masa asiri. Sai malamin ya ce, “Sai an samo hauren giwa domin ya haɗa maganin da shi”.

Sai mutumin ya je cikin jama’a ya ce, “Wa zai iya samo min hauren giwa in ba shi kuɗi?’

Aka rasa wanda zai iya.
Sai Gizo ya ce, “Shi zai iya”.
Sai mutumin ya ce, “To shi ke nan, sai ka samo ka kawo”.

Shi ke nan, sai Gizo ya tafi gida, ya daka nakiya mai zaƙin gaske. Sai ya je gidan giwa da ɗan ƙunshin nakiyar a hannunsa, ya ce, “Gafaya dai masu gida”.
Sai giwa ta ce, “Maraba da Gizo”.
Ya ce, “Yauwa, Wata nakiya ce na kawo miki da na samo a pa”.
Shi ke nan sai giwa ta ce, “To”.

Ta gutsiri nakiya ta kai bakinta. Da ta ji zaƙin nakiyar, sai ta ce, “Don Allah Gizo, ni ma ka raka ni in je in samo?”
Sai ya ce, “Haba yaya! Me zai hana in raka ki? Ki zo gobe in kai ki”.
Shi ke nan, sai ta zo washegari, suka je wajen kan pa. Sai ya ce da ita, “Idan kika doka bakinki sau ɗaya, kika doka sau biyu, a na ukun sai ki ga nakiya ruɓus a bakinki”.

Shi ke nan, sai giwa ta doka bakinta sau ɗaya fas a kan pa. Ta kuma dokawa. Da ta doka na ukun, sai haƙorinta ya ɓalle ya faɗo ƙasa.
Sai jini shar.
Sai Gizo ya ce, “Assha, assha! Yaya aka yi haka kuma?” Ya yi maza ya ɗauki haƙorin giwar, ya sa a aljihunsa. Ita ba ta gani ba. Tana ta kanta.
Shi ke nan sai gizo ya bar giwa a nan. Ya yi sauri ya kai wa mutumin nan haƙorin.

Mutumin ya ba shi ladansa.

Sai gizo ya je daji ya tattara namun daji, suka je gidan da giwa take a kwance, suka tarar kanta ya kumbura, suntum.

Gizo ya gaya wa namun dajin cewa, “In na ce, “Babbanmu da giɓi”, ku ce, Ɓurum ɓaɓurka”.
Sai ya fara waƙar:
Babbanmu da giɓi,
Sai suka amsa:
Ɓurum ɓaɓurka.
Shi ke nan sai suka gama, suka koma. Gizo ya bar giwa a wahala, shi kuwa ya karɓe kuɗinsa.
Shi ke nan.
Ƙurunƙus.

Domin karanta Tatsuniyar Yarinya Da Dodanni danna nan

Domin karanta Hausawa Da Al’adunsu danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Duba Rijistar Layin Waya
Labarin na GabaShinkafa Mai Ƙwai
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.