LAIFIN WAYE???

0
3086

GODIYA:
Duk kannin godiya su tabbata ga Allah S.W.A mai kowa mai komai wanda shine ya bani ikon rubuta wannan littafi.Jin jina da yabo su tabbata ga Annabi Muhammad S.A.W.

SADAUKARWA:
Na sadaukar da wannan littafi nawa ga ‘yan uwana da abokan arziki musamman ma’abota karanta littafina.

GARGADI:
Mugun kuskure ne wani ko wata su juya wannan littafi nawa ta kowacce siga ba tare da izinina ba kiyaye wannan doka kuwa nada muhimmanci.
A kiyaye!

JINJINA:
Ina mika jinjinata mara musaltuwa ga ma’abota karanta littafina Allah yabar zumunci Amin!.

Wasu zafafan hawaye ne masu d’umi ke cigaba da kwaranya a idanun Rukayyah yayin da take sunkuye a gaban Alhaji Muktar,zuciyarta cike take da bak’in ciki muryarta na rawa tace d’an Allah Alhaji karufamin asiri kadda ka kwace yarannan don hakan yana nuna bara zana a gareni da kuma aure na.Muddun mijina da iyayena suka fahimci halin da nake ciki nasan babu makawa tawa ta k’are,kashina kuma ya bushe.

Alhaji Muktar bai kalli ko inda Rukayyah take ba ballema yayi tunanin tausayamata, shima a halin yanzu ji yake yafita buk’atar wad’annan yara,yace nifa wannan kukan da kike ba zaisa na janye kudirina na k’arbar yarana ba.Domin kinfi kowa sanin matsalata a halin yanzu banida wata mafita da ya wuce na karbi ‘ya’yana,sanin kanki ne tunda Allah yayiwa ‘ya’yana da mahifiyarsu rasuwa a sanadiyyar had’arin mota da mukayi likitan ya shedamin cewa bazan k’ara haihuwa ba,sanadin wata muguwar buguwa da nayi a gabana wanda hakan yayi silar mutuwar kwayoyin haihuwa ta.Kinga kuwa ni nafi ki buk’atar su a halin yanzu.Motarsa ya ja Inda ya barta a tsugunne tana cigaba da zubda hawaye.

Tunda Rukayyah ta koma gida yanayinta ya sanja ta zama tamkar mara lafiya a dalilin maganar Alhaji Muktar da take ta bibiyawa a zuciyarta.Ni kan najawo wa kaina babban tashin hankali na jefa kaina a cikin babbar matsala na shiga uku ni Rukayyah yaya zanyi da raina Allah ya gani banida laifi a cikin wannan al’amari Zayyad shine silar fad’awata cikin masifar nan,amma nasan cewar babu wanda zai fahimce ni balle ma ya fahimci ba laifina bane.Wad’annan maganganun su Rukayyah ta cigaba da nana tawa a zuciyarta,Wanda har ya kai ga sautin kukan da take ya fara fitowa fili.

Kyaran muryar Zayyad da Rukayyah taji shiya bata damar share hawayen dake fuskarta cikin gaggawa,amma duk da haka sai da ya fahimci halin da take ciki fuskar sa cike da tuhumar sonjin abida ke damunta yace lafiya kuwa my dear yau naganki cikin yanayin da bansaba ganin ki ba? Cikin sanyin murya Rukayyah ta fara fad’awa Yusuf sab’anin abinda ke zuciyarta,tace wallahi yaya yau tunda na tashi ba najin dad’in jikina jinakeyi kamar anyimin duka duk gab’obin jikina ciwo sukayi.Fuskar Zayyad cike da tausayinta ya janyota kan cinyarsa ya fara tambayar ta kinsha magani kuwa my dear? Don Ina ganin kamar zazzabine yake shirin kamaki ya kamata kisha ko paracetamol ne kafin gobe muje asibiti.

Zuciyarta ce ke cigaba da tafarfasa bala’in da tajawo kanta ya fara fink’arfinta,haka ta kwana bata rintsa ba washegari da safe zayyad yace ta shirya suje asibiti amma sai ta nuna mai tasami sauki tunda tasha paracetamol jiya.kudin cefane ya d’auko ya bata sukayi sallama ya tafi portacourt kamar yadda ya saba.

Misalin k’arfe takwas na safe Rukayyah ta kammala shirya yaranta Inda ta zuba musu ido tana kallonsu yayin da suke karyawa,tausayin k’aramin cikin su Abdulmajeed shine yafi d’aga mata hankali domin shi yarone du-dudu shekararsa d’aya a duniya,bai sanma me duniyar take ciki ba gashi Alhaji Muktar yayi rantsuwa bazai bar mata koda d’a d’aya ba.

Karar wayar da ke gefanta ne ya firgitar da ita wanda yayi silar wata muguwar faduwar gaba da tayi, Abdulwahab ne babban d’anta ya d’auko wayar ya miko mata. Ki same ni a inda muka saba haduwa nan da minti ashirin.Maganar da Alhaji Muktar ya fad’amata kenan yayin da tadauki wayar,ba tare da yaji amsar da zata bashi ba yasa hannu ya katse wayar. Bata San lokacin da hawaye ya subuce mata a idanunta ba sai ji tayi yaranta suna tambayarta lafiya Ummah waye ya rasu? Cikin gaggawa Rukayyah tasa hannu ta share hawayen dake fuskarta tace musu babu komai ku tashi na kaiku makarantar.

Kamar yadda Alhaji Muktar ya sheda mata wurin da zasu hadu haka ta tafi, bayan ta kai yaranta makaranta.A tsaye yake ya juya baya jikinsa sanye da k’ananan kaya,fuskar sa a murtuke babu alamun wasa a tartare da shi.Yace Rukayyah wannan shine kashedi na biyu da zanyi miki akan ki dawomin da yarana kink’i,to wallahi na uku sai dai kotu ta rabamu dake.dam! gabanta ya yanke ya fadi har sai da takai ga kirjinta ya fara wani irin buguwa.Jikinta ya dau rawa wata hajiji ta lullubeta kamar zata fad’i. Tayi ta maza tace anya kuwa kana cikin hayyacin ka Muktar? Kasan abinda kake furtawa kuwa? Kasan cewa in kashigar da maganarnan kotu bani kad’ai ka tonawa asiri ba harda kanka.

A fusace ya juyo yace baza ki gane bana cikin hankalina ba,sai ranar da na kawo miki takardar sammaci inyaso daga nan duk duniya taji abinda muka aikata,ni kuma daga nan sai kisa ayi dani asibitin mahaukata,bai k’ara tsayawa ya saurareta ba ya ja motar sa ya tafi.

Al’amarin nan kullum k’ara d’aga wa Rukayyah hankali yake, matukar ba Alhaji Muktar bane ya janye kudirinsa to babu ita ba kwanciyar hankali.Sai da takai ta kawo ko kwayar abinci bata iya kaiwa bakinta,tabi ta rame tayi bakikkirin inka ganta bakace Rukayyah bace.Zayyad baya gajiya wajen yi musu aike tare da dauke duk wata d’awai niya da tashafe su,kamar yadda duk safiyar duniya sai ya kirata a waya don yaji ya suka kwana.Shi kansa ya fuskan ci Matarsa tana cikin damuwa amma a koda yaushe ya tambayeta sai ta nuna mai babu komai, kawai dai kewar rashinsa a kusa itace take damunta.

Zaune take akan daya daga cikin kujerun dake sittirum din gidanta tayi shiru yayin da K’aramin danta Abdulmajeed ke wasa a gefenta, d’aga idanunta tayi ta kalli agogo taga har lokacin tashin su Abdulwahab ya wuce amma basu dawo gida ba,nan take hankalin ta ya tashi ta d’auki Abdulmajeed ta goya bata nufi ko ina ba sai makarantar su,Inda ta sami Headmaster na shirin kulle office,cikin gigicewa tayi Sallama bayan sun gaisa ne ta tambaye shi yaranta.Amma abin ta kaici sai ya fad’amata cewa sun dade da tafiya gida,suna cikin hakanne mai gadin makarantar ya sheda mata cewa yaga lokacin da mahaifin su ya daukesu a mota.

Mahaifin su kuma? Rukayyah ta tambaye shi cikin mamaki.Nan da nan fuskarta ta cika da hawaye,cikin kuka tace ba mahaifin su bane domin shi baya gari.Amma nasan ko waye bazai wuce Alhaji Muktar ba,amma….. Ba tare da ta k’arasa maganar ba ta fashe da matsananci kuka,Headmaster yayi kok’arin kiranta don ta tsaya amma bata saurare shiba.

Wuni tayi tana kewaya duk Inda tasan zata sami Alhaji Muktar amma babu shi ba labarin sa,wayoyin sa duk a kashe Rukayyah ta zama tamkar wata mahaukaciya tayi nan tayi can,Sai da ta kai har gabannin magariba amma babu labarin yaranta.Gidan yayarta Amina ta nufa inda ta shiga gidan cikin kuka,hankalin Amina ya tashi saka makon irin yanayin da Rukayyah ta shigo da shi,kunce mata d’an dake bayanta tayi ta cigaba da tambayarta lafiya kuwa Rukayyah? Ba tasamu wata cikakkiyar amsa daga bakin taba saka makon matsanancin kuka da takeyi,da kyar dai Amina ta sami kan Rukayyah ta sheda mata dukkannin abinda ke faruwa.

Mekike fad’a Rukayyah? Kina nufin an sace miki yaranki duka? Hankalin Amina a tashe yayin da take yiwa Rukayyah wannan tambayar. Cikin muryar kuka tace eh Aunty an sace su duka,kuma amma akwai wanda nake zargi.Anan hankalin Amina ya d’an kwanta ta dubi Rukayyah tace wakike zargin ya sace miki yara?

Aunty ina zargin wani mutumi mai suna Alhaji Muktar don banida tantama shine ya sacemin yarana,Amina tace indai hakane ki kwantar da hankalin ki ta kwana gidan sauki tunda dai akwai hukuma. To amma Baban su yasan da wannan zancen kuwa? Rukayyah ta girgiza kai wanda ke nuni da mahaifinsu bai san da wannan al’amarin ba.

Amina tace mata gaskiya kinyi kuskure ai ya kamata ace kafin kowa yaji zancen nan shi ya kamata ki fara fad’a wa.Shine shugaba a gareku kuma shine Uban yarannan kin ga kuwa inhar aka kwana ba’a fad’amasa ba a kwai babbar matsala,Yanzu kisa waya ki kirashi ki fadamai duk abinda ake ciki.

Muryar ta na rawa tace wallahi Aunty bazan iya tunkarar Zayad da wannan maganar ba,kinfi kowa sanin halinsa a kan yarannan ni yanzu na’isa na tunkareshi da wannan zancen.Gaskiya Aunty sai dai inke zaki fad’a mai amma ni bazan iya ba. Fad’awa cinyar Amina ta k’arayi tana kuka yayin da ita kuma take cigaba da rarrashinta.

Hankalin Zayyad ya tashi matuk’a a lokacin da Amina ke bayyana mai abinda ya faru,take ya d’auki fad’a wai laifin Rukayyah ne mesaya da taga lokacin tashin su yayi bata je ta d’auko su ba.Ya cigaba da fad’a ba tare da ya saurari abinda suke cewa ba,ta Inda ya hau ba tanan yake sauk’a ya kuma ce a fad’amata kadda ta sake ta koma mai gida ba tare da yaransa ba. A take ya kashe wayar sakamakon bakin cikin Rukayyah da ya turni keshi.

Muryar Rukayyah na rawa tace Aunty daman sai da na fad’a miki domin nafi kowa sanin halin Zayyad,bazai dauki wannan a matsayin tsautayi ko k’addara ba lafina zai gani,to yanzu Aunty ya zanyi da raina da bakin cikin b’atan yaran nan zanji kokuma da bakin cikin da ya tusamin.Rarrashin da Amina keyiwa Rukayyah a baya yanzu ma shi ta cigaba da yimata,tace bakomai kiyi hakuri Rukayyah yanzu dai zama bai kama mu ba tashi zakiyi muje gida musanar da su Inna abinda ke faruwa.

Bayan sun idar da sallar magariba suka nufi gidan Inna,sunyi babbar sa’a domin har mahaifin su Malam Garba yana gida a lokacin.Yanayin yanda suka shiga gidan kad’ai ya bayyanawa mahaifan nasu cewa suna tafe ne da babbar matsala,saka makon tunda suke basu tab’a irin wannan shigowa da sukayi ba.Inna ta dube su tace lafiya kuwa kuka shigo gida ko sallama babu balle kuyi tunanin gaishe damu?

Wata muguwar ajiyar zuciya Amina taja tace ina lafiya Inna,ai yaran Rukayyah aka sace da Abdulwahab da kuma Fauziyya.Hankalin Inna a tashe tace yaran Rukayyah aka sace fa kika ce? Amina tace eh Inna tun da suka tafi makaranta basu dawo ba kuma Rukayyah tabi sawun su akace wani ne ya daukesu a mota,sai dai tace tasan mutumin dama ta dade tana zargin yana kaiwa yaran hari. Malam Garba mahaifinsu yayi saurin shafa addu’ar da yake bayan ya idar da sallah, inalillahi wa inna’ilaihirrajuun wannan itace kalmar da ta cigaba da fita a bakin Malam Garba,yace to yanzu tasan Inda mutumin yake ne? Rukayyah ta d’ago kanta idanunta sun kad’a sunyi jajur tace a’a Baba ban sani ba,amma dai duk Inda nake tunanin yana zama naje ban same shi ba.

To ai yanzu ba zama yakamata ayi ba hukuma za’a shedawa su zasu binci ko shi duk Inda yake,amma kafin nan Mahaifin su yasan labarin? Amina ce tayi saurin cewa yasani Baba donni da kaina na sanar da shi,sai dai yanata fad’a don har yace idan Rukayyah bata nemo mai yaran sa ba to kadda ta koma mai gidan sa.

Malam Garba yayi hannu bibbiyu yace babbar magana kenan,gaskiya baiyi adalci ba idan rai yab’aci ai hankalu baya gushewa duk son da yake yiwa yarannan ai baiyi ya na mahaifiyar su ba,ita kanta baza taso yaran nan su b’ata ba. Suna cikin jimamin ne sukaji ana doka sallama,kafin suce wani abu har an turo kofar ananiyar shigowa.Hajiya Habiba ce ta shigo a gigice tana ta rafka salati,wanda hakan ke nuni da Zayyad ya fada’mata duk abinda yake faruwa.

Sannu da zuwa Hajiya k’araso ki zauna mana,Inna ce keyi mata maraba a lokacin da ta shigo cikin d’akin.A Gigice Hajiya Habiba tace yanzun nan ai daga gidan Rukayyah nake na tarar gidan a kulle,shine nace bari nak’araso gidan nan watakilla ko nan ta taho.Wallahi tunda Zayyad ya fadamin hankalina ya kasa kwanciya.

Gaskiya ne Hajiya don mudinma duk hakanne,mu kanmu bamu da wannan labari sai yanzu du-dudu basufi minti talatin ba da shigowarsu ita da ‘yar uwarta. Fuskar Malam Garba cike da al’ajabi yayin da yake yiwa Hajiya Habiba mahaifiyar Zayyad wannan bayanin.

To amma inaganin dani da kai da kuma ita Rukayyah yakamata muje wurin hukuma domin a sanar da su halin da muke ciki,kuma in Allah ya kaimu gobe sai aje gidan redio a sanar ko Allah zaisa a dace.Malam Garga ya tari numfashin Hajiya Habiba yace haka ne baza muki ta takiba,,amma kema insan samune kije gida ni da Rukayyah ma kadai sai muje ko ya kikace Hajiya? Ya juyo ya dubi matar sa mahaifiyar su Rukayyah.Ita dinma abinda mijinta ya yanke shi tabi,don a lokacin ta bashi amsa da wannan gaskiya ne Malam.

Hajiya Habibi bata amince aje wurin hukuma ba tare da ita ba,don tana ganin kamar ita zata maye gurbin d’anta Zayyad,ganin cewa baya kusa duk wani hakki na uba ya raya a wuyan ta.

Idanun Rukayyah akan Inspector Abbas yake yayin da yake daukar statement din su,ji take tamkar ansamu yaranta angama saboda irin labarinsa da takeji akan kwarewar sa wajen aiki. Inspector Abbas ya cigaba da yiwa Rukayyah tambayoyi,ita kuma tana bashi amsar duk abunda ta sani.To meyasa lokacin da kikace kina zarginsa da kaiwa yaranki hari baki sanar da hukuma ba? Rukayyah tace yallab’a dayake ai a lokacin zarginsa nake kuma bani da wata kwakkwarar hujja, wannan shine dalilin da yasa ban doshi hukuma ba. Girgiza kai Inspector Abbas yayi yace hakane amma kinsan number motar tashi ne? Rukayyah tace gaskiya bansani ba yallab’a. Inspector Abbas ya cigaba da rubuta duk kannin abubuwan da yake buk’ata wanda ya samesu a maganganun da sukayi da Rukayyah.

Labarin b’atan yaran ya kewaye duk cikin garin na Yobe ko ina zancen su akeyi,daga cikin anguwa harma da gidajen redio. Jami’an tsaro sun shafe sama da kwana ki uku suna bincike amma babu wani labari mai dad’i,saka makon haryanzu ba’a samu ko wanda yaga yaran ba. Rukayyah da iyayenta ba suyi k’asa a guiwa ba ganin cewa kullum suna hanyar police station,a koda yaushe hankalinta a tashe yake don jita ke a halin yanzu koda asirinta zai tonu inzata ga yaranta bai dameta ba.

Zayyad da kansa sai da yabaro pothacot ya dawo Yobe,domin abin yaci tira ya kuma fara fin k’arfin jami’an tsaro.Yana shigowa garin bai tsaya a ko ina ba sai gidan su Rukayyah, inda ya tarar da ita zaune a baranda tana ta sharb’ar kuka ba tare da tasan ya shigo ba,ya tsayawa yayi tsam da ransa zuciyarsa cike da tausayinta ya nemi duk wani k’unci da yadebo a zuciyarsa ya rasa.K’arasawa kusa da ita yayi tare da yimata sallama cikin sanyin murya,Amincin Allah da yardar sa sutabbata a gareki ya mai kyawun sura gami da hak’uri,juriya,da kuma imani da k’addara. Cikin mamakin muryar da kunnuwanta kejiye mata ta juyo inda idanuta sukayi kicibus da idanun shi ta kuma fashewa da kuka.
Zayyad ya k’ank’ameta yace to kuma meye na kukan baza kiyi shiru ba.Ta d’augo kai ta kalle shi tace Abban Abdulmajeed saboda me zakace bazanyi kuka ba,bayan haryanzu ba’aga su Abdulwahab ba.Zayyad ya cigaba da rarrashinta yace nasani kuma nasan zafin da kikeji domin nima shi nakeji a zuciyata,amma ki sani wannan kukan bashi zaisa muga yarannan ba gara mu cigaba dayin addu’ar Allah ya bayyana mana su. Yanzu ina su Innan suke? Rukayyah tayi saurin d’ago k’anta daga kan kirjin sa tace suna cikin gida.Bayan ya shiga sun gaisa ne ya nufi police station ko zai sami sabon labari daga wurin su.

Alhaji Muktar ya cigaba da boye yaran nan guda biyu da ya sace a gidan gonar sa dake farkon shiga jahar Yobe,yana kuma basu kulawa kamar yadda ya kamata don ko da ace mahaifiyar su tana wurin iya abinda zatayi musu kenan.Sai dai kash kullum a cikin fuskantar matsala yake daga wurin yaran saka makon basu da wani aiki da ya wuce kukan a kai su wurin Umman su,sai da takai ta kawo ko abinci suka daina ci sukayi wata muguwar rama.Hankalin Alhaji muktar yayi mugun tashi ganin irin halin k’ak’anakayin da yaran suke k’ok’arin jefa kansu aciki,a kullum tausayin su yana damunsa sosai don wasu lokutan sai yayi kamar ya maida su wurin mahaifiyar su sai kuma yaji kaunar yaran ta mamaye zuciyar sa.Hakan nan suka cigaba da zama kullum yana cikin rarrashin su da abubuwan da zasu d’auke musu hankali.Kamar yadda kuma yake kokarin fahimtar dasu akan shine mahaifinsu,babban abin takaicinma yaran basa yadda dashi ko kadan ballema suyi tunanin daukar sa a matsayin mahaifin nasu.Wannan shine babban takaicin da yafi damun Alhaji muktar.

A lokacin da Zayyad ya dawo daga police station Rukayyah tayi tunanin ko zai zo mata da labarin yaranta,sai kuma aka sami akasin hakan don yanda yaje haka ya dawo ko Inspector Abbas dinma bai samu gani ba,saka makon meeting din gaggawa da manyansu suka kira su. Sai dai ya bawa Innan Rukayyah da kuma mahaifinta hakuri akan hukuncin da ya yanke cikin b’acin rai,na cewa Rukayyah da yayi kadda ta komamai gida ba tare da yaran sa ba,ya kuma roki alfarma da a bashi matar sa ya tafi da ita. Ba dan komai ba sai dan bin umarnin mahaifiyar sa da yayi.

Malam Garba yace bakomai zaka iya tafiya da ita,sai dai ina mai baku shawara da ku cigaba da hakuri a cikin rayuwarku ta yau da kullum.

Kwana Zayyad yayi baiyi bacci ba yana nanata maganar da Rukayyah tayi na cewa ta dade tana zargin mutumin daya sace musu yaran su,abinda zuciyar sa take sak’amai shine to a ina Rukayyah tasan wannan mutumin kuma tayaya tasan yana da niyar sace yarannan.Wannan tambayar ita ya kwana yana yiwa zuciyar sa har akayi kiran sallar asalatu.

Kamar yanda Rukayyah ta saba bayan sunyi sallar asuba yauma hakan tayi,tayi addu’oin safiya sannan tamik’e domin daurawa mijinta abin karyawa.Ba tare da tayi wani taku mai nisa ba Zayyad yace Rukayyah zomana inaso muyi wata magana dake,sai da gabanta ya fad’i kamar wacce tasan maganar Alhaji Muktar zaiyi mata.Ta dawo ta zauna a bakin gadon da Zayyad ke kwance.

Rukayyah inaso ki fad’amin wanene mutumin da kika ce kin dade kina zargin sa da yanaso ya sacemin yara,kuma a ina kika sanshi ya akayi kuma kika san hakan?A take gabanta ya kara fad’i dam! A dalilin wad’annan tambayoyin guda uku da Zayyad yayi mata masu rikitarwa. Ta rasa amsar da zata bashi domin kota ina ya d’aureta da jijiyoyin jikinta,basira ce ta fad’omata tace Abdulwahab yana yawan fad’amin cewa kullum idan nakaisu makaranta wani mutumi yana zuwa ya kawo musu chocolate da wafer iri-iri, kuma yana cemusu wai zaizo yadauke su ya tafi dasu gidan sa daga nan ma har racxy zai kaisu.Wani lokacinma har ya kaisu yawon bayan antashi a makaranta amma abin mamaki kafin naje makarantar daukko su har yadawo dasu,shine nake tambayar su sunan mutumin suka cemin Alhaji Muktar. Ni kuma akwai wanda nasani mai wannan sunan bashi da wani aiki da ya wuce satar yara yana garkuwa dasu.Wannan shine dalilin da yasa nace nasan shi kuma ina zargin sa da satar yaran mu.

Dogon numfashi Zayyad yaja bayan ya gama saurarar labarin k’anzan kuregen da Rukayyah ta gama basa,wanda kwatakwata hankalin sa bai dauka ba,yayi tsaki yace shikenan jeki.

Da misalin k’arfe 11:am na safe Inspector Abbas yazo har gida ya samesu,don k’arajin wasu bayyanai daga bakin Rukayyah ya kuma nemi ta bashi hotunan yaran domin zai taimaka musu wajen zurfafa bincike.Su kayimai godiya saboda irin k’ok’arin da yake wajen ganin ya nemo musu yaran su.

Yau har ta kaiga yaran sun doshi watanni uku a hannun Alhaji Muktar,sai dai duk wani kayan abinci da ya tanada sunk’are wanda hakan yasa ya yanke shawarar fitowa cikin gari ta b’arauniyar hanya kamar yanda ya saba domin nema musu abinci,ya kuma damk’a yaran a hannun wani yaron sa mai suna Hashim.

Ya samu nasarar zuwa Super market kamar yanda ya saba ba tare da kowa ya ganshi ba,sai dai ya samu labarin ‘yan sanda sun matsa bincike wajen neman sa. Har ya gama abinda yake yana sauri ya bud’e mortar sa zai shiga sai yaji anyi a resting dinsa da bindiga,yana juyowa Inspector Abbas ya daure hannayen sa da ankwa.Inda anan Inspector Abbas ya k’ara jinjinawa Rukayyah dalilin k’ok’arin da tayi wajen kiran su a waya a lokacin da taga Alhaji Muktar.

Malam Garba,Inna,Amina harma da Hajiya Habiba dukkanin su suka dunguma sukayi police station.A inda Inspector Abbas ya sheda musu cewa haryanzu Alhaji Muktar yak’i amincewa da shine ya sace yaran. A fusace Rukayyah ta tashi tace wallah k’arya yake inspector shine ya sace su,sannan ta k’ara fashewa da matsanancin kuka. Hajiya Habiba ce ke cigaba da rarrashinta tana kuma kwantar mata da hankali.Inspector Abbas ya tausayamata matuk’a da ya ga yanayi da ta shiga cikin k’ank’anin lokaci,yace kar ki damu insha Allah nayi miki alk’awarin nan da gobe sai ya amsa lefin sa,domin zanyi masa horo mai tsanani tunda nayi masa ta ruwan sanyi amma yak’i amsa lefin sa.

Tunda suka dawo gida hankalin Rukayyah bai kwanta ba saboda tunanin makomarta da takeyi idan har duniya tasan irin aika-aikan da suka yi ita da Alhaji Muktar,hankalinta ya tashi matuk’a duk dacewa ita a ganinta ba laifinta bane Zayyad da Mahaifanta sune silar fad’awarta cikin wannan masifa.To amma tasan babu wanda zai fashimce ta matuk’ar duniya tasan da wannan babban al’amarin.K’arar sautin wayarta dake gefenta shine ya dawo da hankalinta kan wayar,dam! Gabanta ya yanke ya fad’i sakamakon kiran inspector Abbas da ta gani yana shigowa wayarta. A sukwane tasa hannu ta d’auki wayar bayan sun gaisa ne ya sheda mata cewa ana bukatar ganinsu yanzu a police station,ba tare da inspector Abbas yaji ta bakinta ba ya katse wayar sa.

Zuciyarta ta shiga sake_sake a tunaninta Alhaji muktar ya bayyanawa hukuma dukkannin abinda ya faru tsakaninta da shi,duk ta gigice ta kuma rasa abinda yakeyi mata dad’i sai da ta kewaye duk cikin falonta,zuciyarta na cigaba da yimata zulimi iri_iri. D’akin Zayyad ta nufa inda ta tarar dashi kwance a kan sallayar da ya idar da sallar azahar. Wai ana san ganin mu a police station yanxu inspector Abbas ya kirani a waya ya fadamin.Fuskar Rukayyah cike da damu yayin da take shedawa zayyad wannan maganar.

Nan da nan Zayyad ya mike bai tsaya wata_wata ba tare da fadin ki dauko mayafinki mutafi Allah yasa muji alkhairi. A gaskiya ban tab’a ganin mutum mai taurinkan wannan Mutumin ba,duk ta inda mukabi yaki amsa lefinsa nayima sa horo mai tsanani amma inda kasan ba jikin sa ake duka ba saboda taurin kai. Amma ni a ganina yafi kyau mutura ku koto don inaga ananne kadai za’a samu maslaha. Kotu kuma inspector? Cikin kidimewa Rukayyah keyiwa inspector wannan tambayar. Eh lalle wannan itace kawai mafuta a gareku domin munyi iya kokarin mu sai kuma a gwada da kotun a gani watagila a dace. Bayan Insoector Abbas ya gama wannan jawa binne Zayyad ya amince da a turasu kotun sannan ya nemi alfarmar da akai su kotun shari’a ta addinin musulunci.

Hankalin Rukayyah a tashe yake tunda suka koma gida takasa cewa komai, banda tashin hankali da take ciki babu komai a zuciyarta. Ta kai ta kawo tarasa inda zata daura rayuwarta, a karshe ta yanke shawarar zuwa gidan su aminiyarta failusa. Ina zakije da yamman nan kike kokarin fita bayan kinsan nafadami ki cewa Barrister faisal zaizo anjima domin samun karin bayani daga bakin ki. Rukayyah sam bataji dadin wannan kalami da mijinta yayi ba amma haka ta daure zuciyarta tare ta cewa daman zanje gidan Aunty Amina ne nasanar da ita abinda ake ciki,kuma daga nan zan biya na shedawa su Inna.Zayyad yace to naji amma dai kadda ki dade domin kinsan munyi Alkawari da shi zaizo da yamma.

Bata nufi ko inaba sai gidan su aminiyarta Failusa,sai dai tayi rashin sa’a don bata tarar da ita a gida ba wayar dake hannunta tasa ta kirata inda Failusa tacemata tajirata zata zo nan da minti biyar. Ta shafe tsawon mintuna goma ba tare da Failusa ta dawo ba ,har sai da ta fito kofar gida tana jiranta ta cigaba da waige_waige don ganin ta inda zata bullu.

K’afarta ta fara fitowa da ita daga cikin k’ank’ararriyar motar da aka kawota a ciki,Rukayyah tasa ido ta bita da kallo badan abinda failusa take ya birgeta ba. A halin da take yanzu tayi nadamar yin rayuwa irin ta failusa.Cikin takun k’asaita Failusa ta karaso wurin da Rukayyah ke tsaya,mezan gani haka anya kuwa kece? Meyake damun ki kawata duk kin jeme haka kinyi bakikkirin. Fuskar Failusa cike da damuwa yayin da take tambayar Rukayyah. Ran Rukayya abace tace kedai bari k’awata akwai matsala don ina cikin babban tashin.

Tashin hankali kuma? Failusa ta tambayeta cikin al’ajabi. Eh kawata amma dai mushiga ciki kiji matsalar da ta addabeni. Failusa kanta tashiga wani irin yanayi cikin k’annanin lokaci,maganar da Rukayyah tazo mata da ita ta hargutsa mata duk wani lissafinta,badan komai ba sai dan itace silar faruwar duk wani abu da ya faru da ita. Doguwar ajiyar zuciya taja gami da cewa gaskiya k’awata Alhaji muktar bai kyauta mana ba,domin a iya zaman da mukayi da shi bai can canci yayi mana haka ba. Amma kema kinyi babban kuskure da baki sanar dani wannan al’amarin tun da farko ba,don nasan da yanzu munsamu mafita da izinin Allah.

Fuskar Rukayyah cike take da hawaye ta juyo ta dafa Failusa tace yanzu kina ganin babu wata mafita da tayi saura kenan. Kwarai kuwa babu wata mafita domin komai yariga ya lalace tunda maganar taje ga hukuma.Rukayyah ta dora hannayenta bibbyu a kanta tare da kara fashewa da matsanancin kuka. Failusa tayi saurin tarota daga k’asan da take k’ok’arinyi tace haba k’awata kiyi hakuri mana,kinaso ki k’ara sawa kanki wata cutane bayan abunda yake damun mu? Cikin shesshekar kuka Rukayyah tace haba Failusa mekike so nayi inbanyi kukan ba,ki tinafa narasa yarana har guda biya gashi nima inna dab da rasa tawa rayuwar iyayena da Zayyad sune silar afkawata cikin wannan masifar domin a lokacin dana kai musu kukana sun kasa sharemin hawayena kuma…………

Ba tare data k’arasa maganar ba Failusa ta k’atseta itama fuskarta duk ta jik’e da hawaye tsabar tausayin Rukayyah da ya mamaye zuciyarta,tace kadda ki k’ara daukan laifin nan ki dangana da mijinki ko iyayenki domin inda mai lafi to a bayana yake.Nice wacce na baki gur_guwar shawara har kika afka wannan bala’i,babu wanda ya kamata ki zarga sai ni k’awata.Wallahi bazan tab’a zarginki ba koda kina da laifi sune nafarkon masu laifi da suka tarwatsa rayuwata da duk wani farin cikina. Rukayyah da Failusa suka sha koke koken su suka gaji daga bisani kuma Failusa tace zata tuntub’i saurayinta commishinan ‘yan Sanda ko Allah zaisa a dakatar da kai maganar kotu.Don na tabbata indai naje masa da maganar komai ya kare.

Amina ce zaune a falon Rukayyah bayan tsawon awonnin da tashafe a gidan tana jiranta,Zayyad kansa a fusace yake saka makon tsayar da Barrister Faisal da yayi duk a dalilin Rukayyah.A karshe ya yanke shawarar sallamar sa daya tafi gami da bashi hakuri dalilin b’atamai lokaci da yayi,ba tare da ita Rukayyan ta dawo ba. Har anfara kiraye_kirayen sallar isha’i sannan Rukayyah ta dawo gida jikinta duk a sanyaye,don ganin Zayyad da tayi tsaye a k’ofar gida wanda kenuni da ita yake jira.Saurin shigewa gidan tayi ba tare da ta ko kalli inda Zayyad yake ba. Yaja wani mugun tsaki sannan ya bita cikin gidan.

Yanzu abunda kikayi kin kyauta kenan haka mukayi dake kafin ki fita? Sunkuyawa Rukayyah tayi har kasa tace dan Allah kayi hakuri Abban Abdulmajeed nasan na batama rai,amma nima hakan ta faru ne ba’a son rai na ba tunkafin ayi sallar magari ba nafito amma bansamu mota ba sai yanzu,ko gidan Innan ma bansamu naje ba banda gidan Aunty Amina da naje kwai…….. Yimun shiru Zayyad ya katseta daga maganar da takeyi. Makaryaciyar banza banda bakya jin kunyar yin karya ina Aunty Aminan kanta du_du batafi minti talatin da fita daga gidan ba,kuma baki dade da fita ba itama tazo ta hakan na nuni da cewa dukkannin inda kika cemin zaki je banan kika je ba. Uhmmm! Rukayyah taja dogon numfashi tace wallahi najeni inhar nayima karya meye ribata a rayuwa? Nacema daganan nake amma bai zama dole ne ka yadda ba ta wuce d’akinta ta bar Zayyad a tsaye a falo.

A kullum al’amarin Rukayyah yana mugun daurewa Zayyad kai yadda ta sanja halayyarta cikin kankanin lokaci,yarasa ma wanne irin mataki zai dauka a kanta gashi kuma gobe ne koma warsa potharcour.Sai da yayi kamar ya kyale ta da case din yaran inyaso tanemo masa su duk inda suka shiga,amma sai wata zuciyar tace kadda ya aikata hakan domin badan ita zaiyiba sai dan ceto rayuwar yaransa.

Da misalin Karfe shida na safe Zayyad ya shirya ya fito inda yasami Rukayyah kwance lame-lame a gado bata da niyar tashi.Zayyad ya kira sunanta Rukayyah!Rukayyah ki tashi nizan wuce sauri nakeyi don ina gudun kadda na makara.A hankali ta fara bude kyawawan idanun ta tayi wata mik’a wadda ke nuni da bacci bai isheta,har zaka wuce kenan tunda sassafennan? Rukayyah tayimai wannan tambaya cikin yanayin bacci. Yanzunne sassafe kinsan ma karfe nawa kuwa kike yimin wannan tambayar,Zayyad ya fada a fusace. Kadde kicema ko sallar asuba bakiyi ba.Ba tare da Zayyad yajira wata amsa daga bakinta ba ya dauko kudi ya ajiyemata a bakin gado yawuce yayi tafiyayarsa.

Wuni tayi ranar tana sharar bacci babu abinda ke tayar da ita illa sallah itama daga tayi take komawa baccinta,Abdulwahab kuwa ko samun damar yimai wanka batayi ba.Jin tab’ata gami da Kiran sunanta da ji anyi shine yayi silar farkawarta,inda idanunta sukaci karo dana aminiyarta failusa, fuskarta cike da murmushi tace kawata yau kece a gidan namu. Ke kwa yau wanne irin bacci kikeyi tundazu inata doka Sallama bakisan ma abinda akeba,gashi kinbar gida abud’e ko tsoron wani ya shigoma ke bakeyi.Failusa ce keyiwa Rukayyah wannan tambayar bayan ta zauna abakin gadon da Rukayyan ke kwance

Wallahi nikaina bansan dalilin wannan bacci nawa ba, tun safe nake abu d’aya ko abin karyawa ma bansamu na d’aura ba. Ko karyawa fa kika ce? Failusa ta tambayeta cikin mamaki. Rukayyah tayi murmushi tace eh wallahi kawata donni ko yunwar ma bajinta nake ba. Tab! Amma lalle kawata agaishe ki,to shikuma mijin naki fa mekika bashi yaci? Zayyad wai aini yau ko kallon arziki bai hadani da shiba,ballema nayi tunanin yimai abin karyawa haka ya kad’a yayi tafiyarsa pothacot ko sallamar kirki bata hadani da shi ba.

Ran Failusa ab’ace tace haba k’awata amma gaskiya banji dadin abinda kikayi ba ko kad’an,meya hadaki da Zayyad harkika yimai wannan wulakancin? Wallahi k’awata ba haka bane kawai donnaje gidan ku jiya shine yake ta yimin masifa nikuma na share shi kwai,kuma badon wani abu bane ila don nace gidan Inna da Aunty Amina zani shi kuma daya fahimci banje ba sai kawai ya daukeni da gaba.

Ita kanta Failusa bata d’aurewa Rukayyah gindi ba,tace gaskiya abinda kikayi baki kyauta ba ko kad’an kuma sam bai dace ba,ya za’ayi ke da yimai laifi kuma ace kece dayin fushi aikamata yayi ace kin bashi hakuri da irin dabarun mu na Mata,gaskiya kinban kunya sai kace ba mace ba. Ki tuna fa yanzu ba dabace komai yariga ya sanja,ko wannan iftila’in da muke ciki kad’ai ya ishemu amma gashi kina niyar b’allo mana wani haba k’awata. Mafita muke nema inkika tun zurashi kuma ai baza muci nasarar da muke nema ba, yanzu abinda nakeso dake ki kirashi a waya ki bashi hakuri

Shiru Rukayyah tayi yayin da take sauraron nasihar da k’awarta Failusa keyimata,abun ya d’aure mata kai sosai don Failusa tabata mamaki matuk’a, yaushema tayi hankali harta fara yimin nasiha.Rukayyah ta fad’a acikin zuciyarta..Kamar yadda Failusan ta shawarci Rukayyah hakan kwa akayi,don bata bar gidan ba sai da ta tabbatar ta dai-dai ta Rukayyah da mijinta. Sannan kuma ta sheda mata cewa sunyi magana da comishina na ‘yan sanda amma sai dai ba’a dace ba,don shima kansa yace case d’in yafi k’arfinsa anriga an dank’a shi a hannun babban alk’alin Shari’a.Dafe kirjinta Rukayyah tayi tare da cewa nikam shikenan tawa ta k’are k’wata,babu abinda ya ragemin domin komai ya riga ya lalace.

Tausayin Rukayyah a wannan lokacin shine ya k’ara mamaye zuciyar Failusa,ta dubeta tace haba k’awata bai kamata irin wad’annan kalmomin su ringa fitowa daga bakin kiba, babu abinda yafimana a halin yanzu da ya wuce addu’a itace kawai zatayi mana maganin komai. Amma ina da wata shawara wacce nake ganin insha Allahu zata zamo mafita agare mu.A take Rukayyah ta d’anji wani sanyi a zuciyarta,tace wacce irin shawara ce k’awata?

Gyara zama Failusa ta tayi tare da cewa inadai haryanzu baku d’auki lauya ba? Rukayyah ta girgiza kai wanda kenuni da basu dauka ba,sai kuma daga baya ta shedawa Failusa yadda sukayi da Zayyad akan lauyan da yace yayiwa maganar,amma Kuma ita kanta bata da tabbacin hakan a halin yanzu. Duk da hakan ma inaso kiyiwa Zayyad waya ki shedama sa cewa kinji labarin wani jajirtaccen lauya wanda kike sa ran indai Ya shiga case dinnan za’a sami mafita da yardar Allah.Ni kuma akwai wani lauya kwararre da zansa yayi mana wannan aiki,shi ko da kwa kisan kai mutum yayi indai zaka sakar mai kud’i tofa an wuce wuri. Rukayyah taji dad’in wannan shawara ta aminiyarta, inda daga bisani kuma sukayi sallama ta tafi tare da cewa zata dawo donji yadda sukayi da Zayyad.

Alk’ali ya bada ranar bakwai ga watan ugusta shekara ta dubu biyu da sha bakwai da misalin k’arfe tara na safe, amatsayin ranar da zai fara sauraron k’arar Rukayyah tsakaninta da Alhaji Muktar,bayan dama da aka bawa ko wannen su na daukan lauya domin kare shi. Barrister Mahammad Auwal shine wanda su Rukayyah suka dauka a matsayin mai karesu,wanda shine wanda k’awarta Failusa ta samo musu shi kamar yadda ta fad’a a baya.Ta kuma tsaramai duk kannin gaskiyar abinda ya faru da kuma yadda suke son shari’ar ta kasance,sun kuma sami had’in kansa cikin k’ank’anin lokaci bayan sun d’auki makudan kud’i masu yawa sun mallakamai.Ba tare da kowa yasan gaskiyar abinda suka kulla tsakanin su da Barrister ba.

Mahaifin Rukayyah Malam Garba shine ya cigaba da tsaye musu akan duk wata buk’ata da tataso,ganin cewa Zayyad da ya kamata ya d’auki duk wata d’awainiyar su baya gari.Sai dai a kullum baya gajiya da yi musu aik’en kud’i a duk lokacin da buk’atar hakan ta taso,kamar yadda itama Hajiya Habiba take iyakacin k’ok’arinta na ganin ta taka muhimmiyar rawa a dukkan lamuran nasu. Failusa da Rukayyah kuwa basa samun zama kullum suna cikin kai kawo ta yadda zasu shiga su fita domin samun nasarar su.

Saura kwanaki biyu kacal suka rage a fara gabatar da shari’ar tasu a babbar kotun ta addinin musulunci dake jahar Yobe. Amma sai dai haryanzu hankalin Rukayyah yaki kwanciya ko kad’an,jita keyi a jikinta tamkar ba zatayi nasara ba idan ta zauna ta cigaba da tuna ire-iren abubuwan da suka faru a baya. A halin yanzu bata rayuwarta take ba babban burinta a koda yaushe shine ceto rayuwar yaranta,ko da kwa zata rasa tata rayuwar. Sai dai abin takaicin d’ayane wanda a kullum ke d’aga mata hankalinta da wacce fuska zata kalli iyayenta da kuma mijinta inhar asirinta ya tonu? Wannan tambayar ita take yiwa zuciyarta a koda yaushe.

Ranar litinin da misalin k’arfe takwas da rabi na safe dukkanin su suka bayyana a kotun suna jiran k’arasowar alk’ali,sai dai tunda sukaje gaban Rukayyah yake cigaba da muguwar fad’uwa, Amina yayarta ce da ta fahimci halin da take ciki ta cigaba da k’ok’arin kwantar mata da hankali. Cikin tsoro ta dubi Amina tace wallahi Aunty tunda mukazo kotun nan hankalina yaki kwanciya,narasa ma menene yake yimin dad’i a duniya. Kedai abinda zance miki kwai ki kwantar da hankalin ki da yardar Allah babu abunda zaifaru,kuma insha Allahu gaskiya zata bayyana.Amma mudun kika d’aga hankalin ki tofa lalle zakiyi kwab’a wajen amsa tambayoyin da za’ayi miki a……K’arar sautin wayar Rukayyah ne ya katse Amina daga nasihar da take yimata. Cikin sauri ta d’auki wayar don ganin sunan mijinta da tayi.Bayan sun gaisa Zayyad yace daman nakira ne naji ko kun k’arasa kotun ne.Eh yanzu hakama muna can dukkan mu harda su Inna da kuma Hajiya,muna jiran k’arasowar alk’alin ne kawai. Zayyad yace to ina fatan dai babu wata matsalako? Rukayyah ta k’ara bashi amsa da babu sannan sukayi sallama ta kashe wayar.

Taci karo da missed call din Failusa sama da biyar a yayin da ta kammala wayar.Ba tare da iyayenta sun fahimta ba ta fito daga kotun ta kirata,k’awata kin zo ne? Rukayyah ta tameta cikin murna. Cikin fishi Failusa tace babu abinda zaki fad’amin kin shanyani tun d’azu ina waje,bayan kuma nakira ki har sau biyar ba tare da kin d’aga ba. Haba k’awata yi hakuri mana wallahi Zayyad ne ya kirani shiyasa kika jini shiru,amma ke kanki kinsan ai bazan yimiki haka ba.Dan Allah yanzu kina dai-dai ina? Failusa ta fad’a mata inda take.

Rukayyah ta tarar da Failusa tare da Barrister Mahammad Auwal a tsaye k’ark’ashin wata bishiya,ya kuma k’ara jadda dawa Rukayyah da tasan irin maganganun da zasu fito daga bak’in ta. Sannan ya bayyana mata duk abubuwan da ya dace ta fad’a a yayin da lauya keyi mata tambaya. Sun shafe sama da mintuna biyar suna tattaunawa a tsakanin su,sai da ya rage saura minti biyu tara tayi sannan suka koma kotun.

Inspector Abbas ya kaddamar da Alhaji Muktar a kotun,k’arfe tara na cika Alk’ali ya bayyana a kotun.Maga ta kadda ya mik’e tsaye tare da cewa a yau litinin bakwai ga watan ugusta,shekara ta dubu biyu da sha bakwai da misalin k’arfe tara na safe kotu zata saurari k’arar Rukayyah Abubakar tare da Alhaji muktar Ahmad,wanda take zarginsa da sace mata yaranta har guda biyu. Bayan maga takaddar ya kammala jawabinsa ne ya mik’awa mai girma Alk’ali takaddun shari’ar.

Idan malama Rukayyah tana kusa kotu tana buk’atar ganinta tare da shi wanda ake tuhuma. Alk’ali ne ya nemi ganin su domin fara gabatar da shari’ar. Rukayyah ta juya sukayi ido biyu da Failusa sannan ta mike ta fito gaban koto.Ya mai girma mai shari’a sunana Rukayyah Abubakar nice wacce nake k’arar Alhaji muktar Ahmad a matsayin wanda ya sacemin yarana guda biyu. Alk’ali ya sake juyawa wurin Alhaji muktar yace kaji laifin da ake tuhumar ka da shi shin kana da ja? Eh ina da ja yamai shari’a domin kuwa ni ban sace mata yara ba. Alk’ali ya cigaba da rubuce-rubucen sa sannan yace ko wacce take k’ara da wanda ake k’ara suna da lauya mai kare su?

Cikin nutsuwa lauyan Rukayyah ya tashi.Sunana Barrister Mahammad Auwal lauya mai zaman kansa nine mai kare wacce take k’ara.Daga bangaren Alhaji muktar kuwa Barrister Musa Sharif ne ya tashi a matsayin mai kare shi. Barrister Mahammad Auwal ya k’ara tashi yace ya mai girma mai shari’a ina rokon wannan koto mai albarka da ta bani dama nad’an yiwa Malama Rukayyah wasu tambayoyi. Alk’ali ya dubeta yace koto ta baka dama.

Malama Rukayyah shin kisan Alhaji muktar ne daman? Eh nasan shi farin sani domin na tab’a aiki a k’ark’ashin sa a wata ma’aikita da ake kira NPI,wanda shine shugaban ma’aikatar a wannan lokaci. Shin akwai wata kyakkyawar alak’a dake tsakanin ki da shi? Rukayyah tace babu wata alak’a a tsakanina dashi bayan wacce na fada a baya. To tayaya kike tunanin shine ya sace miki yara? Ba tunani nake ba tabbatarwa nake domin yadad’e yana yimin bara zana akan hakan. To masha Allah zaki iya komawa wurin zamanki,Barrister Muhammad Auwal ya fad’amata bayan ya kammala tambayarta. Ya mai girma mai shari’a inason wannan kotu mai adalci da tayi duba ga maganganun wannan baiwar Allah da aka zalunta ta bimata kadu wajen karb’o mata ‘ya’yanta daga wurin wannan azzalumin mutumin.

Inada ja ya mai shari’a! Barrister Musa Sharif ya tashi cikin gaggawa.Bai kamata abokin aikina ya dunga daukan lefi yana dan ganashi ga Alhaji muktar ba,bayan zarginsa ake bashi da tabbacin shi mai laifine. Alk’ali yace Barrister Mahammad a kiyaye. Cikin girmamawa Barrister Mahammad Auwal yace ankiyaye ya mai shari’a,ina k’ara rokon wannan koto mai adalci da ta k’ara bani dama na tattauna da Alhaji muktar. Alk’ali ya k’ara bashi dama ta biyu domin tattaunawa dashi.

Alhaji muktar inason ka fad’awa kotu menene alak’arka da Rukayyah? Ni banida wata alak’a da ita kawai dai ta tab’a aiki a k’arkashina, Alhaji muktar ya fad’a cikin sanyin murya. To ko zaka iya fadawa kotu irin zaman da kukayi a baya tare da ita locin kuna aiki tare? Tabbas munyi zama na mutunci tare da ita domin duk wurin aikin mu babu wacce muka shak’u kuma take ganin girmana kamarta. Alhaji muktar ya k’ara bashi amsa. Barrister Mahammad Auwal ya girgiza kai yace da wannan damar kayi amfani kenan wajen sace mata yara? A’a ni bani nasace mata yara ba hasalima bansan kamannin yaranta ba ballema harna nasami damar sace su. To Alhaji muktar kana nufin bakada sa hannu kenan a sace yaran? Barrister Mahammad Auwal ya k’ara tambayarsa. Ni bansan komai game da hakan ba. Ya mai girma mai shari’a ina rok’on wannan kotu mai albarka da ta k’ara bani dama domin gabatar mata da shedata ta farko. Alk’ali yace kotu tabaka dama Barrister.

Malam Dan Asabe mtai gadin makarantar yaran shine wanda aka gabatar a matsayin sheda na farko a b’angaren Rukayyah,inda daga bisani ya bayyanawa kotu dukkannin abunda yasani bayan ransuwa da akasa shi yayi.Barrister Muhammad Auwal yak’ara bayyana wasu hujjoji masu k’arfi wanda shi kansa Alk’ali ya fara gamsuwa da su. Ko lauyan dake kare mai k’ara yana da bin fad’a? Alk’ali ya tambayi Barrister Musa Sharif. Banida abin fad’a ya mai girma mai shari’a sai dai inarok’on wannan kotu mai adalci data d’aga wannan shari’ar domun musami damar gabatar mata da shedun mu gami da k’wararan hujjoji. K’orafin Barrister Musa Sharif ya karb’u domin kuwa Alk’alin ya d’aga karar har zuwa ranar ashirin da d’aya ga watan ugusta.

Zuciyar Rukayyah da k’awarta Failusa cike take da farin ciki a yayin da suka fito daga kotun,suka kuma k’ara jinjinawa Barrister Muhammad Auwal ganin irin k’ok’ari da jajircewa da yayi akan shari’ar. Amma anya kuwa innayi haka nayiwa kaina adalci? Rukayyah ce keyiwa kanta wannan tambayar,ganin irin halin k’ak’a nakayin da Alhaji Muktar ke ciki.A ganina ko bakomai nima ya taimakamin a lokacin da nashiga mawuyacin hali,gaskiya bai cancanci wannan sakayyar daga gareni ba. To amma babu yanda na iya inbayi hakan ba,ko bakomai yarana zasu dawo wurina.Sautin sallamar da taji ana dokawa itace ta dawo da ita daga zancen zucin da takeyi.
Cikin sauri ta tashi don ganin Amina yayarta da tayi,Rukayyah tace Aunty sannu da zuwa bari na kawo miki ruwa. Zo ki zauna abinki ni banida kishi yanzun nan nasha ruwa a gida.Rukayyah daman zuwa nayi na tambayeki wanne daliline ya kai wannan shed’aniyar yarinyar kotu harma nagan ku tare da it’s? Rukayyah najin wannan bato na Amina yayarta tagane inda ta dosa domin tasan bawata take nufi ba illa Failusa,amman sai tanuna mata tamkar bata gane wacce yarinya take nufi ba.

Fuskarta Rukayyah cike da al’ajabi tace Aunty wacce yarinya kuma? Akwai wacce nake nufi ne da ya wuce yarinyar da mijinki ya hanaki mu’amala da ita Failusa.Rukayyah tayi dum jikinta a sanyaye tace wallahi Aunty ni ba wani abu bane ya hadani da ita ba kamar yadda kika ganta akotun nima haka naganta. Amina ta k’ara cewa to koma dai menene kisan halin da kike ciki ki fita daga harkar yarinyan nan,sanin kanki ne duk garinnan babu wanda baisan munanan d’abi’un yarinyar nan ba.Rukayyah ta yiwa Amina alk’awarin daina shiga duk wata safga data shafi Failusa.

A gefe guda kuma lauyansu wato Barrister Mahammad Auwal na cigaba da kai kawo wajen ganin yasami k’wararan hujjojin da zaijewa kotu dasu,dukkan nin abubuwan da suka shafi wannan k’ara ya koma hannun Failusa don gudun kadda iyayen Rukayyah su fahimci cewa haryanzu akwai alak’a a tsakanin su.Sun cigaba da tsara abubuwan su kamar yadda suka saba kuma komai yana tafiya dai-dai ba tare da kowa ya fahimci tsarin su ba.Sai dai Rukayyah tana zuwa wurin lauyan ba tare da kowa ya Sani ba, duk lokacin da ya buk’aci hakan.

Saura kwana ki biyu kacal ya rage su koma kotun Zayyad ya dawo daga garin potharcourt,ba tare da ita kanta Rukayyah tasan da dawowar tasa ba.Cikin mama ta mik’e tsaye don ganin sa da tayi kwatsam a cikin falo,tace Yaya kaine ko kuma dai idanuwa nane keyimin gizo? Zayyad yayi murmushi yace nine Maman Abdulmajeed ba gizo nake yi miki ba.Amma gaskiya ka shammace ni ya akayi bayan munyi waya dazu amma baka sanar dani cewa kana hanya ba? Rukayyah ta k’ara tambayar shi. Kwai nayi hakan ne donna yimiki zuwan bazata.Bayan yabata wannan amsar ya wuce d’aki inda tayi dagalau tana binsa da kallo.

Bayan Zayyad yayi wanka ya huta ya kuma yi sallar la’asar gami da cin abinci,ya nemi Rukayyah data had’ashi da lauyan dake karesu wato Barrister Mahammad Auwal.Ba tare da tsoro ko fargaba a zuciyar Rukayyah ba ta d’auki number Lauyan ta bawa mijinta,don tasan duk ta yanda yaje masa ta haka zai bida shi. Zayyad bai tsaya wani b’ata lokaci ba ya kira wayar lawyan,bayan yayi masa bayanin ko shi wanene sannan ya buk’aci su had’u don wata tattaunawa da zasuyi mai mahimmanci.

Ranar litinin wanda yayi dai-dai da ashirin da d’aya ga watan ugusta suka koma kotu don cigaba da sauraran k’ara.Tun da misalin karfe takwas na safe muka koma kotun,Alk’ali yace ina fatan dai Lauya maikare wanda yake k’ara yazowa kotu da kwararan hujjoji kamar yanda yayi wa k’otu alk’awari.Kwarai kuwa ya mai girma mai shari’a domin kuma yanzu ma intare da hujjata mai k’arfi izini nake buk’ata daga wurin kotu domin gabatar musu da ita.Alk’ali yace k’otu ta baka dama

Firgita Alhaji muktar yayi don ganin shedar da lauyan ke k’ok’arin gabatarwa da kotu ita.Barrister Mahammad Auwal yace bawan Allah ko zaka iya bayyanawa kotu sunan ka da kuma inda kafito? Sunana Hashim yarima kuma ni haifaffan garin Nguru ne.Barrister yace to ko kasan wannan mutumin? Ya nuna masa Alhaji muktar. Hashim yace eh nasan shi farin sani domin kuma maigidana ne,nine babban yaron sa duk wasu harkoki nasa a hannuna suke. Barrister ya k’ara cewa to bayan nan babu wata alak’a da ta k’ara shiga tsakanin ku? Hashim yayi dam ya dubi Alhaji muktar ya kuma juyawa ya kalli Barrister yayi shiru nawasu dakik’a baice komai ba. Barrister yace kayi magana mana yakayi shiru. Eh akwai alak’ar data shiga tsakanin mu. Ko zaka iya bayyanawa kotu wacce irin alak’a ce?

Hashim yace kamar yanda na bayyana a baya nine babban yaronsa,kuma nine amintaccensa ma’ana babu wani sirri nasa da bansani ba.Wanda hakan yasa ya kawomin a jiyar yaran sa guda biyu har tsawon watannani ina kulawa dasu. Ko zaka iya fadawa kotu inda yaran suke yanzu? Hashim ya k’ara cewa mun zauna da su a gidan gonar Alhaji muktar wanda yanzu hakan yaran suna tare da ni a cikin kotun. Bayan Alk’ali ya bada dama aka shigo da yaran cikin kotun,suka tafi da gudu suka rungumai mahaifiyarsu dukkannin su suna kuka.Bakin ciki ya turnuke Alhaji muktar ya kasa cewa komai.

Alk’ali ya yankewa Alhaji muktar hukunci dai-dai da yanda kotu ta tanadarwa mai laifi irin masa,ta kuma nemi da ya biya Rukayyah wasu kudade sanadiyyar wahalar da ita da yayi.

Har Alk’ali yana shirin tashi Rukayyah ta mike cikin kuka tace ina da magana ya mai shari’a. Wacce irin magana kike da ita Rukayyah? Alk’ali ya tambayeta.Tace tabbas wad’annan yaran ‘ya’yan Alhaji muktar ne,ba ‘ya’yan Zayyad bane cikin kuka mai tsanani Rukayyah ta shedawa Alk’ali. A take zuciyar kowa ta cika da mamaki wannan ya kalli wance wannan ya kalli wannan. Alk’ali yace kisan abinda kike fad’a kuwa Rukayyah? Tace nasani ya mai shari’a,domin kuwa ba ‘ya’yan zayyad bane,sai dai an samu akasi d’aya domin Abdulmajeed ba d’ansa bane d’an Zayyad ne Abdulwahab da sauran yaran sune nasa .

Maganganun da Rukayyah keyi sun d’aurewa dukkanin jama’ar dake kotun kai,har wasu sun fara tunanin Rukayyah ba’a hayyacinta take furta wa ba.Kinsan abunda kike fada kuwa Rukayyah? Alk’ali ya sake tambayarta. Rukayyah tace nasani ya mai Shari’a kuma ina cikin hankalina.To agarin ya haka ta kasan ce?

Mu’amala ta fara shiga tsakanina dashi ne tun shekarun da Zayyad ya fara tafiye -tafiye wanda hakan yasa nakasa jure damuwata tun ina boye mai harna fara nuna wa a fili,amma sai ya shashantar dani tamkar bai fahimci abinda nake nufi ba. Yana kwashe sama da wata takwas wani lokacin ma har shekara ba tare da ya waiwai cemu ba,shi aganin shi tunda yana ajiyemin kayan Cefane bani da wata buk’atar. Dana fuskan ci bazai saurare ni ba sai na yanke shawarar bayyana wa mahaifana halin da ake ciki don kub’utar da kaina daga shiga mugun hali,suma basu saurare niba kamar yadda basu bari na tsara abunda ya kawoni gida ba.

Hakuri kawai suke bani na nacigaba da hakuri a rayuwar aure na,bayan ni ba wannan matsalar ce ke cimin tuwo a kwarya ba.Na koma gidana narasa abunda yake yimin dadi ban hakura ba na sake kiran Zayyad a waya na nuna ina buk’atar sa kusa dani amma sai ya nuna min shi aiki yayi mai yawa bazai samu damar dawowa a kwana kusa ba, daga k’arshe dana matsa mai sai yace ni wacce irin Macece wai da bazan iya hakurin rashin sa na watanni ba.

A kwana a tashi rannan k’awata Failusa taxo ta tarar dani cikin muguwar damuwa,wanda hakan yasa na bayyana mata duk wani sirrina tare da abunda ke damu na.Anan ne ta bani shawarar tarayya tare da Alhaji Muktar nayi mamaki matuk’a don ganin mutumin kirki nake yi masa amma kuma naji akasin hakan. Duk da ya dade yana muna kauna da kyautayawa agare ni amma ban tab’a yin wani mugun tunani akan saba.Sama da kowa yake a wurin aikin mu hakan yasa nafara tunanin kadda shawarar da Failusa ta bani tasa nayi biyu babu,wato ina gudun kadda narasa aiki na. Amma sai ta nunamin mu’amala dashi sai dai tasa a k’aramin girma a wurin aikin,hakkan nan na yanke shawarar aikata abinda Failusa ta xomin dashi duk da nasan hanyar bamai kyau bace,babu yadda na iya ne domin ina cikin wani hali kuma nakasa jurewa.

Alhaji Muktar yaji dad’i matuk’a don ya dad’e yana neman hanyar da zaiyi mu’amala dani amma bai samu ba,sai gashi yau ya samu cikin sauk’i ba tare da ya sha wahala ba. Ya shedawa Failusa cewa mu had’u dashi a d’aya daga cikin gidajen da yake sauk’e bakin sa,ya kuma bani lokacin da xanje gidan.

Da misalin karfe 4:00pm na yamma Failusa tazo gidana muka shirya bamu tsaya a ko ina ba sai gidan da ya fadamana,nidai duk hankalina ya kasa kwanciya ji nakeyi tamkar wani zai iya gani na.Da kwarin gwiwar da Failusa tace gaba da bani na samu muka shige gidan ba tare da kowa ya ganmu ba, mun same shi cikin wani tafkeken falo wanda aka k’ayata shi da wasu kata faren kujeru na alfarma tare da kayayyaki na alatu.

Dudu-du bamu fi minti ashirin da zuwa ba Failusa tayimin sallama ta wuce gida,take naji wani iri duk jikina ya d’auki rawa ganin cewa ban saba ba. Daya fahimci halin da nake ciki yayi ta k’ok’arin kwantarmin da hankali har komai ya faru,wanda itace rana ta farko da muka fara mu’amala dashi.Yayimin kyauta mai girma tare da k’aramin matsayi a wurin aikina,muka cigaba da gudanar da mu’amala tare dashi a duk lokacin da Zayyad baya gani.Har muka haifi yara guda biyu wato Abdulwahab da k’anwar sa Fauziyyah, wannan shine takaitaccen labarin abinda ya faru.

Innalillahi wa inna’laihirrajuun! Itace kalmar da ta cigaba da fitowa daga bakin mahaifan Rukayyah.Nan da nan itama ta k’ara fashewa da kuka tare da cewa ku gafarta min Inna na cucer da rayuwar ku,na b’ata muku suna.Duk cikin kotun ta rude Alk’ali da ya ga haka ya bubbuga k’ararrawar sa tare da fadin kowa yayi shiru.Tsantsar bak’in cikin da ya turnik’e Zayyad bai ce uffan ba shi kadai yasan rad’adin zafin da zuciyar sa keyi na bak’in ciki.

Alk’ali ya sake yanke sabon hukunci kamar yadda shari’a ta tanadar wa mai laifi irin nasu,ma’ana dukannin su suna da aure sukayi zina wanda hakan yasa aka yanke musu hukun cin kisa ta hanyar jefe su.Sannan mijinta Zayyad aka kamashi da laifin kin sauk’e nauyi ga iyalin sa,wanda shine sila na farko na fad’awar Rukayyah cikin masifar data tsinci Kanta.Haka suma iyayenta sun taka babbar rawa wajen aikata abinda Allah ya haramta,sakamakon rashin sauraronta da suka kiyi a lokacin da taje musu da matsalarta.

Ranar jumma’a da misalin k’arfe takwas na safe itace ranar da kotu ta bayyana a matsayin ranar da za’a hukunta su, Rukayyah ta nemi yafiya daga wurin mijinta da iyayenta sannan ta rok’i ‘yar uwata Amina da ta kula mata da yaranta.Dukkannin su hankalin su yayi matuk’ar tashi musamman Zayyad don shine ya sanyata cikin wanna bala’i data Shiga,shima ya nemi yafi ya agareta haka suma iyayenta.Cikin kuka gaba d’ayan su ‘yan sanda suka sa su Rukayyah a mota aka wuce dasu gidan kaso kafin zuwa gobe jumma’a a jefe su.

Nice taku a kullum
Maryam Rabi’u Ado nake yi muku godiya da irin kaunar da kuke nuna min,ina alfahari daku a koda yaushe. Zaku iya samun littattafaina a wikihausa.com.ng books a yanar gizo kawai ku rubuta sunana zaku samu duk littafina da kuke buk’ata.tsakanin mu sai naji ku.

Hakkin mallaka(c):
Maryam Rabi’u Ado (‘yar autar marubuta)

labarin da ya wuceSHAN RUBUTU DA NUFIN SAMUN MIJIN AURE
Labarin na GabaHanyoyi 11 Da Ake Rage Ƙiba Ba Tare Da An Kashe Ko Sisi Ba.