SHAN RUBUTU DA NUFIN SAMUN MIJIN AURE

0
3342

Tambaya

Assalamu Alaikum warahmatullah. Malam don Allah ina neman fatawa ce.

Wata ce take neman miji kasancewar duk masu zuwar mata ba da gaske suke yi ba, to shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure, yake ba ta tana shan rubutu da niyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya a nan shi ne, shin mece ce makomar abin da ta aikata, shin Malam ta yi shirka ne ko kuwa ta yi ba daidai ba? nagode.

Amsa

Da farko game da shan rubutu, muddin ayar QUR’ANI ce tsantsa, babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta,  IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU’UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbatar da hakan a SARIMUL BATTAR,
Amma in akasin haka ne haramun ne, don yakan zama shirka ce da surkulle,
Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya, to galibi irin na shirkan suke yi, don haka ki tuba tsakaninki da Allah da alkawarin ba za ki sake zuwa wurin su ba, don kare addininki da mutuncinki.
Don samun biyan bukatunki sai ki zage da addu’a da kiyamul laili da azumi da istigfari, kuma kina iya lazimtar wannan adu’ar domin ita  Annabi Musa ya yi, ya sami aikin yi da matar aure a ranar, ga adu’ar👉🏼
رب إني لما أنزلت إلي من خير فقير
Allah ya yafe mana kuma ya ba ki miji nagari,
ALLAHU A’ALAM.

Amsawa Sheikh Abubakar BN Mustafa Biu
05/10/2019

Daga : ZAUREN ISLAMIC SUNNAH

labarin da ya wuceSHAN RUBUTU DA NUFIN SAMUN MIJIN AURE
Labarin na GabaLAIFIN WAYE???
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.