Su Wane ne Mu?

0
444

Mu halitta ce ta jinsin mutane, kuma muna daga cikin waɗanda Allah bai halicce su domin komai ba, sai domin su bauta masa kawai, saboda haka Ya ba mu hankali don mu yi ilmi, da shi ne za mu san daidai, kuma mu san abin da ba daidai ba. Mu san gaskiya daga ƙarya, mu gane bambanci shiriya da ɓata. Da haka za mu yin aiki nagari mu kuma nesanci miyagun ayyuka.

Mutum cikakke shi ne wanda ya yi imani da Allah da Manzonsa, kuma ba ya rabuwa da yin managarcin aiki, idan aka samu saɓani, ya yi tuntuɓe, ya aikata kuskure, sai ya yi sauri ya tuba ya koma ga Allah, sabo da shi mai imani ne da Allah, kuma mai yin koyi da Manzon Allah (S.A.W).
Wannan ita ce siffa ta cikikken mutum, a mahangar Musulunci. Ba kawai kasancewar sa mai ɗauke da kai da ƙafa da iya magana, da dariya ba, ya zama dole sai ya haɗa waɗannan siffofi sannan zai amsa sunansa Ɗan’Adam. Daga nan ne idan an yi tambaya: “Su wane mu” Za mu cancanci bayar da amsar: “Mu mutane ne.”
Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ɗan’Adam kamar yadda Allah Yaee Son sa. wanda M. Aminu Isma’il Sagagi ya wallafa domin karanta cikekken littafin nan DANNA KOREN RUBUTUNNAN

labarin da ya wuceƊabi’ar Lokaci, Saurin Wucewa
Labarin na GabaYadda Ake Haɗa Kwalacca
Dr. Aminu Isma'il Sagagi
An haifi Dr. Sagagi a Unguwar Sagagi cikin birnin Kano a 1968 Ya yi PhD a IUA Khartoum 2012 Ya yi aikin koyarwa a Makarantar Munazzama Kura. Ya yi koyarwa a Makarantar koyon Sharia ta Malam Aminu Kano. Ya taba rike Mukamin Mai ba wa Gwamna Shawara a kan Ilimi 2009-2011 A yanzu Malami ne a Sashin Nazarin Addinin Musulinci a Jami'ar Bayero.