Matsayin Tsibbu Da ‘Yan Tsibbu A Wurin Shehu Usman Bn Fodiyo

0
283

Jagoran jaddada Musulunci a ƙasar Hausa, Shehu Usman Ɗanfodiyo a cikin rubuce-rubucensa da yawa, ya yi gargaɗi; ya tsoratar, ya kuma yanke hukunci ga ayyukan tsibbu na duba da hisabi da sihiri da siddabaru da layu.

Don ƙarin haske, za a iya duba littafan Shehu irin su Nurul-albab da Wasiƙatul Ikhwani da Sirajul Ikhwani; da Bayanil Bidi’i da Tabsiratul Mubtadi da kuma Tamyizil Ahlis Sunnu. A inda ya tabbatar da fitar su daga tafarkin tsira, zuwa ga tafarkin ɓata, tare da wajabcin yaƙar su.

Koda yake a ɓangare guda, akwai gunaguni da wasu ke yi game da rabuce-rubucen da wasu mataimakan Shehu suka yi, wanda ke marawa tsibbu baya.

Rubuce-rubucen sun haɗa da: Ƙirar Ahibba’i da Muhawwanatil Ikhwani ila Mubashshiratil Miswani da Kitabul Hisabi wal Asrari; da kuma Ma’awanatil Ahibba’i Fil Ilmil Adibb’i waɗanda Muhammad Bello da Muhammad Tukur; da Abdullahi da kuma Muhammad Buhari suka rubuta.

Amsa a nan ita ce, koda an danganta musu irin waɗannan ra’ayoyi, to lallai za a ga suna nuna irin maganin da ya halatta a yi da tsantsar Alƙur’ani da Hadisan Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ne. Kamar kuma yadda za a iya gani cikin babukan littafan Bukhari da Muslim da sauran Sittu sihah.

Ma’ana waɗanda ba a jirkita ayoyin Alƙur’ani ba, kuma ba a amsa umarnin aljanu da shaiɗanu ba. Don ƙarin gamsuwa sai a nemi waɗancan littafai don a nazarce su.

Domin karanta cikakken bayani a kan Ƙalubale Ga Makarantun Tsangaya danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Wasu Birane Da Garuruwa Da Makarantu Da KumaTsangayu A Arewacin Najeriya danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceNau’o’in Sihiri
Labarin na GabaYadda Neman Laƙani Da Asiri Ya Shiga Tsangayu