MATAR MALAM

0
6110

FADAKARWA
Ban yi rubutun nan dan cin fuska ko wulakanci ga wasu
ba, illa dan fadakarwa, ilimantarwa gami da
Nishadantarwa. Dan haka duk wanda ya ga wannan
labarin yai kamanceceniya da rayuwarsa to akasi ne.

FARKON LABARIN
(matar malam)Karamin gida ne madaidaici, wanda ke dauke da dakunan kasa falle-falle guda biyu, ta barin gabar su na kallon yamma. yayin da ta barin kudu daf da kofar shiga cikin gida dakine falle daya wanda ke dauke da karamar baranda. ta bangaren arewa kuma, madafa ce
(dakin girki) wanda aka yi rufin kwana da tsarnu (dogayen itace) ba tare da an kare ba. sai jikin madafar
inda bayan gidansu yake (bandaki.) Sai dan karamin tsakar gida. Gidan Malam Musa Kalla kenan, wanda ke zaune da
matan aurensa biyu da yara guda bakwai. daya daga cikin matan nasa amarya ce bai dade da aurota ba, dan
dan ta guda daya ne mai shekaru biyu. sauran shidan duk na uwargida ne. Malam Musa Kalla ba shi da wata
kwakkwara sana’a da ta wuce yin tsubbu ko duba, a takaice dai Malamin Mata ne, har ma da mazan.
Gidansa dam ya ke cika kullum da baki. Ba dan komai ba sai yanda sunansa ya shahara a yankinsu har ma da makwabta. Dan cewa ake aikinsa kamar yankan wuka ne, dan kuwa da rohane ya ke aiki.
Kamar kullum yanda ya saba haka yau ma ya shigo cikin gidan. Kannensa ne a tsakar gida suna zaune su na cin ragowar tuwon daren jiya kafin a dora na rana. Nan ya sa kafa yai bal da abincin. Ta ke kwa yaran suka kama kuka. Kamar jira ya ke ya janyo karaminsu dan gidan amarya ya zabga masa mari. Lokaci daya suka fito daga cikin dakunansu. Da sauri amarya Batula tai kan danta da ya kife ya na ihun kuka. ba tare da tace komai ba ta ja shi su ka koma daki ta na rarrashinsa.
Nan ya hau zage-zage cikin murya irin ta ‘yan maye, daga ji kasan ba a hankalinsa ya ke ba. Mahaifiyarsa Aishatu ta dube sa ranta a matukar 6ace ta ce,
“To tabbatacce! Allah yai dare, garin kuma ya waye ko? kai tsabar baka da kunya fitsararka ta kai intaha idan ka shawo babu inda ta ke nuna maka ka sauke sai cikin gidanku. wallahi Nura matukar ba ka gyara halinka, ka shiryu ba, duniya sai ta koya maka darasi a
rayuwarka.” ta karashe maganar muryarta a dashe alamun bacin ran ya kai makura.
“Haba-haba Inna! Yo me na yi ni kumaa. kawai fa na shigo na hango yaran nan na buga kwallo shine na taya su. Dan sun rainani kuma sai su kama min dariya, kawai shi ne na ba su mahangurba. Bayan wannan kuma me nayi eyeee.” Nura ya fada cikin muryar mashaya ya na yi yana layi.
“Uwaka ka yi.” Malam Musa Kalla ya fada ya na daga kofar dakinsa bayan ya aiko masa da dakuwa hannu bibbiyu.
“Ah Pupsy ashe ka na daga getto, ai ban lura ba da na zo na kwashi albarkoki.” Nura ya fada har yanzu yana tangadi bayan ya jiyo maganar mahaifinsa.
“Na fasso ma ka, ja’iri dan nema. Ni kam Nura albasa ba tai halin ruwa ba wallahi. kwata-kwata babu wanda zai ce kai jinina ne. Na yi asarar haihuwarka turr da samun da irinka.” Malam Kallah ya fada cikin mummunan furuci.
Da sauri Aishatu ta katse mijinta ta ce,
“Haba Malam! Wannan wanne irin mummunan kalami ne haka, ka ke jifan dan cikinka da shi. Ai komai ya
samu Yaronan nan kai ne SANADI. Dan ba dan kai ba da yanzu ina morar da na kamar yanda kowacce uwake morar danta na gari…”
“Ke rufe min baki shashasha! Kullum da an fara magana ki ce nine sila. wallahi Aishatu matukar ba ki daina
jingina ni da lalacewar danki ba to tabbas igiyar aurenki ta na lilo a gidannan.” Malam Kallah ya fada cikin bacin rai, ya na zare idanu kamar tsohon zaki.
Cikin kuka Aishatu ta ce,
“Wanne aure kuma? tun yaushe igiyoyin suke tsinkewa kake mayarwa da kanka. Ni kam na kara fada maka lalle tsakaninmu akwai babban hisabi a gurin Allah. Dan ba yafe maka zan yi ba.” Ta karashe har yanzu tana zubar da hawaye.
Da sauri Malam Musa Kallah ya rarumo madoki yai kanta. a guje tai dakinta ta sakace. Nan ya huce akan Nura, yayi ta dukansa har sai da makota suka zo suka kar6e shi.

Aishatu ta na jin irin dukan da Malam Musa Kallah ke yi wa Nura, amma babu halin ceto a gareta, hasalima da ita ya riska ta san irin dukan da zai yi ma ta kenan.
Nan ta zauna tsakar dakin na ta, da ko ishashshiyar ledar arziki babu, ta fara na gadon, wato kuka. Dan a rayuwar aurensu, tun daga kan shekara daya na amarci har i zuwa yanzu da suka kwashe shekaru ashirin da daya, ba ta san ranar da ta zo ta wuce ma ta a gidan Malam Musa Kallah ba tare da bacin rai ko zubar da hawaye ba.
Da farko ta fara tuhumarsa da son sanin dalilin da yasa ya mayar da ita fursunar gidansa, dan kawai ya azabtar da zuciyarta hadi da gangar jikinta, duk kuwa da irin jajircewa gami da sadaukarwar jindadi da ma rayuwarta da dukiyarta da ta masa, a lokacin samartakarsu da bayan aurensu. Amma yanzu da hankali ya zo ma ta, nan ne ta gano amsar tambayarta da kanta. Ta gane ashe alhakin da ta kwasa a rayuwarta mai girma ne, dan haka dole tayi zaman dirshan gurin tattare abunta, tunda a lokacin ita tace ta ji-ta gani, sannan kuma ta amince.
Ba ta bar kukan ba har zuwa lokacin da abokiyar zamanta Batula ta fara bubbuga ma ta kofar dakin. A firgice ta wartsake dan ta shiga mai nisa (Duniyar tunani). A karo na ba adadi Batula ta kara bubbuga kofar ta na fadin, “Innar Nura ki bude ni ce.” Da alama Batulan na zaton Innar Nura ta dauko ko Malam Musa Kallah ne, shi ya sa ta yi shiru. Daga cikin dakin Aishatu ta amsa “To Batula ganin nan.” Nan ta gogge fuskarta wai duk dan kar a gane ta yi kuka. Wanda kallo daya za ka yiwa kumburarrun idanuwanta ka tabbatar da sun zubar da ruwan azabar zuciya mai radadi.
A sanyaye cikin tausayawa Batula ta bi abokiyar zamanta da kallo, fuskarta dauke da alhini. Ta ce, “Da ma lokacin dora sanwar rana ya fara kuracewa ne, shi ne nace bari na tambayeki me za a dafa?.”
Aishatu ta kalli Batula cike da tausayawa. Yarinya karama da ita Allah ya jarrabeta da shigowa gidan Malam Musa Kallah. Muryarta a dashe irin ta wadanda su ka ci kuka su ka gode Allah ta ce, “Ayya ban san rana ta tafi haka ba Batula. Je ki kama aikinki bari na dora.” Ta fara yin hanyar Madafa
“A’a Innar Nura. Dan Allah ki yi hakuri ki bar ni na dora. Na san yau zuciyarki babu dadi, ba iyawa za ki yi ba. Da a ce Lubah na gida ne ma ta dora. Dan Allah ki je ki huta, zan miki girkin.” Batula ta fada cike da girmamawa.
Aishatu ta kalleta har yanzu da tausayin yarinyar a zuciyarta, wacce a shekaru da kadan za ta dara Nura, amma ga rayuwarta na kasancewa a gidan jaraba.
Aishatu ba ta yarda ta bar Batula da aikin girkin ita kadai ba, dan rana ta yi sosai, dan haka ta kama ma ta, su na yi suna hira. Har zuwa lokacin da wata hadaddiyar mata ‘yar gayu ta yi sallama. Ka na kallonta za ka san farare bugun Abuja sun samu gindin zama zama a gurinta. A kiyasin shekaru ba za ta haura talatin ba, a takaice dai matashiyar mata ce, wacce naira ta samin gurin zama a gurinta.
Da fara’arta ta karaso inda suke bayan ta yi sallama. Fuskarsu babu yabo babu fallasa suka amsa. Dan ba tambaya sun san bakuwar Malam ce. Jikinta ya dan yi sanyi ba kamar yanda ta shigo da farko ba Ganin yànda MATAN MALAM suka amsa ma ta, ta san tabbas ba ta karbu a gurinsu ba. Gaisuwarta ma a yatsine suka amsa. Bayan ta
tambayesu Malam yana nan kuwa. Da baki Batula ta nuna ma ta inda dakinsa ya ke, su ka juyar da kai ba su kara bi ta kanta ba. jikinta a sanyaye zuciyarta cike da mamaki ta tashi ta yi hanyar dakin da suka nuna matan.
Batula cikin kasa da murya ta ce,
“Innar Nura ki fara kirga lokaci, wannan matar sai ta fi awa uku kafin ta fito daga dakin Malam. Dan ya fi bukatar zuwan irin wadannan matan. Amma wallahi yau za’a yi bala’i a gidannan. Dan na gaji, ba zan iya irin hakurinki ba. Shi kenan dan muna MATAN MALAM zuciyarmu ba ta kishi.” Batula ta fada tana hararar hanyar dakin Malam da tuni bakuwar ta shige.
Aishatu ta kalli Batula fuskarta dauke da murmushin ya’ke. Ita ma cikin kasa da muryar ta ce, “Babu ruwanki da shiga sabgar Malam da matan da ke zuwa gurinsa da sunan neman taimako. Dan ba yau
kika fara ba, balle ki ce gwaji za ki yi. Dan haka ki fita sabgarsu su je can su kare.”
“Haba Innar Nura! Yanzu sai a ce muna ji muna kuma gani sai mu kyale mijinmu na lalata da mata a cikin gidanmu da sunan Malanta sai kuma mu kyale. Ai ko babu alhaki akwai kishi.” Batula ta fada.
Aishatu ta dube ta fuskarta dauke da murmushin takaici. Bayan ta cije baki ta jinjina kai ta ce,
“Batula kenan! Na tabbata za ki lafa ne kamar yanda na lafa. Uhmm!” Ta yi kwafa har yanzu ta na sakin murmushin takaicin. ta ajiye shinkafar da ta ke tsinta a kasa daga cinyarta, ta gyara zaman zanin, kafin ta ci gaba.
“Idan na ce duk duniya babu wanda ya so Malam yai kishi a kansa kamar ni, na tabbata ban yi karya ba. Amma tunda kika ga na bar komai na kyale na tabbata dole ke ma wataran za ki saki. Son da na yiwa Malam ba na tunanin a wannan duniyar za a samu wata mace da ta taba yin irinsa, na tabbata ko akwai to a bayana ne. Amma a yanzu ne da lokaci ya kure min, dama ta subuce min, na san ce wa, bayan So akwai wauta cikin al’amarina.” Ta dan tsagaita.
Yayin da Batula ta bar jajjagen kayan miyar da ta ke, ta mika dukkan hankalinta kan Innar Nura.
Ta dubi Batula ta ci gaba da ce wa,, “Ni na san Malam na kuma san waye shi. Dan haka idan kina neman zaman lafiya da dorewar zaman aurenki to ki fitar da kanki daga sabgarsa.
Ci gaba da jajjagenki mana.” Aishatu ta fada bayan ta karashe maganar ta na kallon Batula da ta kura ma ta idanu ta na sauraronta.
Batula ta saukar da nannauyar ajiyar zuciya kafin a sanyaye ta ce,
“Innar Nura na dade ina mamakinki, a duniya ina ji ba za a samu mace mai hakurin zaman aure da juriya irinki ba.
Na dade ina mamakin yanda kike zaune gidan Malam duk kuwa da irin bakin cikin da kike kunsa. Sai dai kafin aurena da zuwa shigowata gidannan, na tsinci labaruruka na rayuwarku da Malam daban-daban.
Sai dai ni a ganina, ta wa matsalar ta fi ta ki. A kullum kwanan duniya ina bakin ciki da takaicin kasancewata cikin wannan gidan. Duk kuwa da ce wa na san laifina
ne, kuskurena. Da ace ban bi irin wannan hanyar gurin cimma burina na ba, da yanzu ban kasance anan ba. Wallahi! A yanzu ba ni da wani fata ko buri, da ya wuce na ga na bar gidannan da sunan aure na har abada, amma har yanzu ban cimma ba.” Batula tana fadin haka ta dora kanta kan tabaryar da ta ke daka ta fara rusar kukan dana-sani da nadama. Wanda hausawa ke ce wa ‘Ba’a sa ma sa rana.”
★★
“Kawata wai ya har yanzu na jiki shiru?” Khadija ta fada ta cikin waya. Daga daya bangaren aka amsa ma ta. Sai ta kara ce wa,
“To dan Allah ki yi sauri ki zo ina jiranki, dan tuntuni na kammala shiryawa ke na ke jira. Abban Sultan na hanya ya kusa karasowa. Kinsan kuma da ya dawo weekend
(hutun karshen mako) No more kara fita again. Dan haka ki hanzarta.”
Aka sake ba ta amsa ta daya bangaren. Sannan ita ma ta amsa da “To yi sauri.” Sannan ta kashe wayar. Daga cikin dakin na ta, tana hango tsakar gidanta cikin
labulen kofar Net din da aka sa ma ta dan maganin shigar sauro da sauran kwaruka cikin d’akin. ‘Yarta ce Salma wacce ba ta wuce shekara takwas zuwa tara ba, ke ta fafutukar girkin abincin da za’a sauki mahaifinta da shi. Dan kuwa mahaifiyarta a rayuwarta ba ta da
wannan lokacin na zama ta girkawa mijinta ko yaranta abincin da za su ci su ji dadi a ransu. Dan sabgar da ke gabanta ta wuce ta 6atawa gurin zaman gida balle ta girka a ci.
“Salma!.” Ta kwallawa yarinyar kira daga dakin. Ba ta ji ba har sai da ta maimaita kusan sau uku.
Da hanzari yarinyar ta taho cikin dakin. “Dan tsabar iskanci kina ji ina kiranki ki ka min shiru.” Ta
fada cikin bacin rai ta na hararar yarinyar. “Wallahi ban ji ba Umma.” Salma ta fada. “To na ji. Ki na ji na ko.” Khadija ta fara magana cikin rada kamar tana zargin akwai wanda zai jiyo su. Hakan ya ba yarinyar damar sake nutsuwa dan jin mai Umman nata za ta ce ma ta. Ta ci gaba, “Maman Mubarak za ta zo yanzu zan rakata unguwa,
ba dadewa zan yi ba. Dan haka ki yi hanzari ki kammala girkin nan kafin Abbanku ya karaso dan ya kusa. Ki jera komai ki kai
masa dakinsa. Idan Faruq ya tashi daga barci ku hadu ku sharo dakin ku goge yanzu nima zan dawo.
Saura kuma idan wancan dan tsurkun ya zo ya tambayeki ina na ke ki ce masa na fita…” Salma ta katse ta da tambayar,
“Umma wa?”
“Adamu mana. Iyayen zalama da kwadayi. Ai sun san yau ranar zuwan Abbanki ne, na san yau za su ci ka min gida. Dangin miji ko jaraba mtsww.” Ta fada ta na tsaki. “Dan haka ko ya zo ki ce masa ina zuwa na zagaya makota gidan Inna Ladi.” Salma ta amsa da “To” Duk da yarintarta, a zuciyarta ta na mamakin yanda Dangin Abbanta da Ummanta ba a jituwa.
Su na cikin maganar ne Maman Mubarak ta shigo da sauri da guntuwar sallamarta. Ko falon ba ta karasa ba Khadija ta jayo mayafinta a gefen kujera ta na fadin,
“Mu hanzarta mu je.”
Maman Mubarak tai dariyar keta ta ce, “Yau fa oga zai dawo duk kin bi kin kideme.” Ba ta ce komai ba, illa dan tura ta da ta yi tana murmushi ta ce, “Ke dai mu je.”
Har sun kai bakin kofa ta juyo ta ce, “Salma idan an dawo da Sultan ki masa wanka kafin na dawo. Kar kuma na dawo na ji kun yi fada da Faruq fa.” Ba ta jira amsar ‘yarta ta ba su kà fice daga gidan, mai
Napep din da ya sauke Maman Mubarak ya daukesu su ka shilla.

Nura ne zaune a dakin Mahaifiyarsu bayan sallar isha’i. Yayin da Innarsa Aishatu ke zaune akan sallaya tana karasa laziminta.
Duk a takure ya ke, kallo daya za ka masa ka tabbatar ba shi da gaskiya. Ta na idar da lazimin ta daga hannu tana addu’arta a bayyane. Yayin da shi ma Nura ya
daga hannu yana amsawa da “Amin.” “Ya Allah! Ya arrahaman! Ya arrahimu! Dan karfin ikonka da jin kanka, dan alfarmar fiyayyen halitta
annabi Muhammad (SAW) Allah ka shiryamin iyalaina, ka gyara musu halayensu su zamo yara na gari a duk inda su ke a fadin duniya. Allah na tuba!!! Ka yafe min kuskurena, ka yafe min. Ya Allah kar ka jarrabeni akan kuskuren da na aikata a rayuwata ya Allah!!!…”
Tausayin kanta da nadama gami da dana-sani ya sa ta kasa karasa addu’ar da ta ke, ta kama kuka.
Shi ma Nura cikin raunin murya ya fara magana.
“Dan Allah Inna ki daina kuka ki yi shiru. Ki yi hakuri ki yafe min. Ni kaina ba a son raina na ke aikata abinda na ke yi ba, illa jarraba.”
Ta dago runannun idanuwanta da suka saba da zubar da hawaye ta na kallonsa, murya a dashe ta ce,
“Haba Nura! ya kuke son na yi da rayuwata ne? Kai yaro ne ko mahaukaci da za ka aikata abu mara kyau sannan ka ce ba’a son ranka ba. Kawai dai farin cikina ne ba kwa so ku gani a duniya, idan kun kashe ni kwa huta.” Ta fada cikin muryar tausayi ta na ci gaba da goge azababben hawayenta da ha6ar hijabi. Tamkar karamin yaro haka Nura ya fara rusar kuka. Da sauri ta dago tana kallonsa.
“Dan Allah Nura yi min shiru, wannan ai idan an jiyo sai a zaci yankaka na ke. Ku dai da mahaifinku ku yi duk abinda ranku ya so a rayuwa. Na san farin cikina ne ba kwa bukatar gani kwatata, ku kwantar da hankalinku,
akwai ranar da za ta zo babu Aishatu babu dalilinta. A wannan lokacin sai ku ci duniyarku da tsinke, yanda ranku ya ke so.”
“Dan Allah Inna ki daina min irin wannan maganar. Wallahi Inna ina sonki ina tausayinki. Rayuwa ce ta
shashanci na tsinci kaina a ciki, amma ki ci gaba da min addu’a Allah ya yaye min. Ni kaina bana jin dadin halin da na ke ciki.” Nura ya fada a nutse tamkar ba shi ba, har yanzu ya na zubar da hawayen.
Aishatu ta dubi danta cikin tsanaki ta na nazarinsa. A kalla yanzu Nura ya kai shekara ashirin da yan
watannin. A wannan shekarun na sa, ya ci ace yanzu ya ci moriyar kansa, har wasu ma na morarsa. Amma sama-ta-ka, ya jefa kansa cikin masifaffiyar rayuwar da ke gurbata tunani da hankalin matashi. Sannan ta zubar masa da kima da mutunci a idanuwan mutane, har hakan ya shafi danginsa da zuri’arsa.
A farkon Rayuwar Nura yaro ne mai tausayi da jin kai, musamman ga mahaifiyarsa, amma lokaci daya
mahaifinsa ya jayo abinda ya gurbata ma ta rayuwar yaro ya rikirkita shi. Shi kuma ya zame hannunsa ya koma gefe ya na jin dadin rayuwarsa ya bar su da kunar zuciya.
Ta saukar da nannauyar ajiyar zuciya ta ce,
“Ina yi maka addu’a Nura, Allah ya shiryeka ya gyara maka halinka. Amma ina son na kara tabbatar maka, addu’ar baki kadai ba za ta yi tasiri a kan ka ba, har sai
ka sa a zuciyarka kai ma kana son gyara halinka. A da Nura kai yaro ne mai hankali, daga mutanen unguwa har dangi kowa yabon halinka ya ke, amma lokaci daya Nura ka lalace, ka bi hanyar banza ta abokanan banza suka illa ta min kai. Lokacin da ka fara wayo a duniya hankalina a ya kwanta. A zuciyata ina jin Allah ya bani wanda zai kwantar min da hankali, na sami abokin shawara wanda
zai ji kaina da tausayina. Dan kuwa tun karaminka ka taso a yaro mai tausayi. Amma a lokacin da ya dace sai kake aikata abinda bai dace ba.”
Nura yayi shiru yana sauraronta, tausayin mahaifiyarsa da dana sanin halin da ya ke ciki na kara baibaye shi.
“Ku Shida na haifa a duniya, amma yanzu ku uku ne kadai a gabana. A cikin ukun kai ma ga halin da kake
ciki. Lubah ce kadai abokiyar shawarata, mai tausayina, To Liman karami shi me ya sani, yaron da bai wuce shekara uku ba. Uhmm!” Ta saki kwafar takaici.
“Ina ji ina kallo Malam ya kwashe yarana guda uku ya tura su almajiranci. Duk makarantun da ke fadin garinnan ba su ishesu karatu ba sai an tura su can wata nahiya mai nisa. Uhmmmm! Ni na tabbata ba dan komai Malam Kallah ke min hakan ba, sai dan ya tusa min bakin ciki, amma ba komai rayuwa ce.”
Ta fada cikin kunar rai. yanzu har hawayen sun kafe, amma yanda ta ke ji a zuciyarta gara ace ruwan hawayen ne ke ta satata da yanda zuciyarta ke tafarfasa.
Idanun Nura yai jajir, fuskarsa ta sauya alamun mummunan bacin rai. Tun yana yaro baya bukatar ganin bacin ran mahaifiyarsa balle yanzu da ya girma ya gane komai. Daya daga cikin dalilan da suka hana shi daina shaye-shaye kenan har yanzu, wato bacin rai, idan ya shigo gida ya gani ko ya ji an taba mahaifiyarsa to shikenan anan gurin ya ke burkicewa kafin ya fita
waje ya warjance.
Yanzun ma hakance ta faru. Bai san lokacin da ya tashi ya fice daga dakin a fusace ba. Innarsa na kwala masa kira, amma ina yayi gaba. Shi kadai ya san abinda zuciyarsa ke kissima masa.
Har kofar daki ta fito tana hangosa yai ball da wata fanteka da ke tsakar gidan yai waje. A fili ta furta,
“Duk inda ka nufa Allah ya tsare min kai, ya kare ka, ya shiryeka da dukkan yaran musulmai.”.
Lubah ce ta shigo cikin gidan da sauri. Nan ta ga Inna a bakin kofar daki.
“Inna lafiya kuwa na ga Ya Nura ya fita a fusace, ga ki ke kuma a tsaye?”
Aishatu ta juya zuwa cikin daki tana cewa, “Ba komai ke dai bani sakon da na aike ki.”

Khadija ce zaune a falon Baban Sultan, bayan ya aika an kira ta. Yayin da Adamu kaninsa, shi ma ke zaune a kujerar da ke fuskantarsu. Shi kuma Garba (Baban
Sultan) ke zaune dirshan a tsakar falon ya mimmike
kafa da rimot a hannunsa ya na canja tashoshi.
“Ki ji fa wai Khadija, Adamu da samun guri. Bayan na
biya masa sadaki wai kuma yanzu akwatin lefe yake
son na kara siya masa.” Baban Sultan ya fada yana
canja tasha har yanzu. Fuskarsa babu yabo babu
fallasa.
Fuskarta a sake ba tare da wata damuwa ba, ta dubi
mijinnata ta na murmushi, sannan ta kalli Adamu da yai
tsuru-tsuru ya na kallonta, sannan ya na aika ma ta da
sakon ta taimake shi ta idonsa.
“Haba Abban Sultan. To yanzu dan Adamu ya ce ka sai
masa akwatin lefe wani abu ne? Idan ba ka masa ba
duk duniya wa za ka yiwa.”
Garba ya juyo yana kallonta ya ce,
“Ke ma fa wani lokacin kamar tunaninki gudawa ya ke.
Yanzu kamar Adamu fisabilallahi dan zai yi aure komai
ni zan yi masa? Kenan idan yai auren ma, matar ni zan
rike masa ita shi ba zai iya ba?.”
Adamu cikin kasa da murya mai dauke da son biyan
bukata ya ce,
“A’a Alhaji. Wallahi ka min komai na kuma gode Allah
ya saka da alkhairi.Ka tallafa min a karatu, ka tallafa
min gurin samun aiki, ka gama min komai.Wallahi
wannan din ma komai ne ya rikice min. Adashen da
muke yi a gurin aiki ni nawan da na zo dauka sai ya
rincabe, kusan mutum hudu ne ba su min zubi ba.
Kuma lokacin da suka min alkawarin kawo kudin, zuwa
lokacin ya kure na shirye-shiryen bikina.
Shi ne na ke son ka taimaka min da akwatin, yanzu ita
kadai ce babbar matsalata, sauran kuma ko da buga-
buga a hada..Dan Allah babban Yayaa!.” Adamu ya
karashe da magiya har da saukowa kasa kusa da
kafafuwansa.
Khadija cikin kwarewa a kissa ta ce,
“To ka ma ji uzurinsa Abban Sultan. Dan Allah ka siya
masa. Duk duniya idan ba ka yiwa dan uwanka ba wa
za ka ma? Kuma fa aure ka taimaka ayi, sunnar
ma’aiki..Please Dan Allah ka taimaka.” Ta fada cikin
karamar murya har tana kashe idanu.
Ya kallesu baki daya, yai tsim ya na tunani, kafin ya ce,
“Ni fa ba wai siyan ne matsalar ba, kunsan halin da
kasarnan ta ke ciki na matsin tattalin arziki. Musamman
ma ni da bana wata sana’ar banda wannan aikin
gwamnatin. Ga hidimar gida da ta yara. Ga mahaifiya
da ku kanku matsalolin ‘yan uwa, banda mutanen waje.
Kowa ya ga gidanka da dan Get dinnan ka gyara shi
kama hawa mota shikenan kallon mai kudi ake maka.
Nan kuwa kai kàsan halin da kake ciki kawai.
Ga Khadija nan, wataran kudin da zan sa katin waya ko
shan man mota a gurinta na ke ara, amma ba’a
ganewa.”
Ya fada cike da damuwa.
“Wallahi Alhaji kowa yasan kana kokari, sai dai kawai
Allah ya saka maka da alkhairi ya kara budi.” Adamu ya
fada a sanyaye, da alama shi ma ya yarda da batun
dan uwan nasa.
“Wacce irin akwati ce kake so ne Adamu?”
Khadija ta tambaya.
Adamu ya kalleta ya kallin Yayansa, kafin ya ce,
“Ko wacce ma Umman yara, indai an samu wacce za’a
zuba kayan ciki ai shikenan.”
Ta dubi Baban Sultan ka na ta kai kallonta kan Adamun
ta ce,
“To ka bari gobe ka dawo, duk yanda magana ta tsaya
za ka ji.”
Adamu fuskarsa da fara’a, dan ya san tabbas tunda
Madam ta sa baki to akwatinsa ta tabbata.
“Dan Allah Umman yara a taimaka. Kin fa san abin nan
sai kara matsowa ya ke.”
“Kar ka damu. Insha Allahu zai samu, ko ni da ina da
halin sai maka zan siya maka wallahi. Ai ba ka da
matsala Adamu, ka cancanta ai maka komai.”
Shi dai Garba bai kara bi ta kansu ba, ya ci gaba da
kallonsa. Dan daman shi mutum ne mara hayaniya,
sannan bai son matsawa kansa.
Su na cikin tattaunawa da Adamu ne game da ranar
bikin da abubuwan da ba’a kammala ba, Faruq danta na
biyu ya shigo dakin. Ya ce,
“Umma kin yi bakuwa.”
Ta dago ta na kallonsa da mamaki,
“Bakuwa kuma da isha’in nan, wacece?”
Yaron sai da ya taka kafar Adamu ya tsallaka kusa da
Abbansa ya na ‘yan tabe-tabe, sannan ya ce,
“Aunty Iyagana ce.”
Fuskarta babu walwala, a zuciyarta kuma ta na ce wa,
“`’Jaraba! Ai sai da na ayyana. Ta ga an kunna
jannareto ta kwaso min gayyar ‘ya’yanta marasa ji, sun
xo kallo..Ni sai na san yanda na yi aka cire AREWA24
dinnan a dakina, mtsww.’“`
Tsakin da ta ja har sai da ya janyo hankalin mijinta. Ya
dube ta cikin kula ya ce,
“Lafiya?”
Da sauri ta waske ta na murmushi ta ce, “Ba komai.”
Ta juya gurin Adamu ta ce, “Yauwa ina jinka. Yanzu ran
yaushe kenan za mu tafi Kanon siyo sauran kayan…”
Garba ya katseta da ce wa, “Ba na ji an ce kin yi
bakuwa ba?”
Ta yatsina fuska ta ce, “Bari mu gama zan je.”
Nan suka ci gaba da tattaunawa da Adamu.Sai da suka
kwashe kusan tsawon minti talatim, kafin ta tashi ta
koma bangarenta, a zuciyarta tana zagin Kawarta, kuma
makociyarta Iyagana.
Amma ta na shiga falon ta saki fuskarta, da fara’arta ta
sami gurin zama ta zauna ta na ce wa,
“Yi hakuri dan Allah Iyagana. Dan banzan yaron nan
ashe tun shigarsa dakin ke kika tura shi, ya sami guri
ya zauna, sai yanzu ya ke fada min kin zo.”
Iyagana fuskarta da fara’a ta ce,
“Allah sarki, wallahi kuwa mun dan dade ma. Ai Salma
ta kamo mana ma AREWA.”
Yaran Iyaganan guda biyu duk suka gaishe da Khadijan,
ta amsa da fara’arta.
“Uhmm! Ina can dakin Abban Sultan iyayen zalamarcan
da rashin godiyar Allah sun sa shi a gaba.” Khadija ta
ke fadawa Iyagana cikin rada.
Fuskar Iyagana da mamaki ta ce, “Su wa fa?”
Khadija ta tabe baki har yanzu cikin kasa da murya ta
ce, “Adamu mana. Ka san ba ka da halin aure menene
na rarumo shi. Tunda ya fara zancen auren nan suka
sako Abban Sultan a gaba, kama daga sadaki, kayan
lefe, hatta gidan haya nasan shi za su ce ya kama
masa,dan ga shi akwatin zuba kayan lefen ma ta
gagare shi ya zo ya na karamar murya.
Shi kuma Yayan ya turje ya ce ya gaji. Yanzu dole ni
din da ba sa so suka tsana zan sa ya sai mu su. Ya
bayar da ko rabi ne ni zan cika rabin.”
Iyagana ta kalleta da mamaki ta ce,
“To ke da ba sa sonki, ko kin yi basa gani, meye na ki
na cika masa kudin akwati?.”
Khadija tai murmushin kasaita tana gyada kai ta ce,,
“Iyagana kenan! Ba za ki gane ba ne. Idan ya hana
kudin akwatin ma, ni da kaina zan cire kudina na je na
siya masa.”
Cike da mamaki da ta’ajibi Iyagana ta jinjina kai ta na
ce wa, “Hu’umm!.”

See u next post…

labarin da ya wuceYadda Za ki Kare Kanki Daga Ciwon Sanyi (Toilet Infection)
Labarin na GabaYadda Ake Maraba Da Mai Gida