Tatsuniyar Yarinya Da Dodanni

0
954

Ga ta nan ga ta nan ku.

Tatsuniya : Wata yarinya ce dai mai tsananin kyau, duk garinsu babu mai kyanta, ta ce ba ta son kowa sai marar tabo. Sai dodanni suka ji labari.

Sai suka yi wanka a gidan tururuwa. sai suka zama samari kyawawa da su.
Da ta gan su, sai ta ce, “Ta sami mazajen aure”. sai duk ta duba jikinsu, sai ta ga jikin wannan da ɗan tabo ɗan mitsitsi, sai ta ce, “Ba ta son sa”. Da ta duba jikin ɗayan ta gan shi sumul, ba ko ɗigon tabo a jikinsa, sai ta ce, “Shi take so”.
Shi ke nan, sai aka shirya aka yi biki.

Sai suka ce, “Za su tafi da ita garinsu, su ba mazauna ba ne”, sai aka ce; “To za a ba ta ƙanwarta ta taya ta zaman ɗaki”. Sai ta ce, “Ita ba ta so, ta zauna ita kaɗai”. Shi ke nan, aka yi aka yi su tafi da ƙanwarta ta ƙi; sai ƙanwar ta zama ƙuda ta maƙale mata.

Shi ke nan, da suka je gidan dodanni; sai dare ya yi suka shiga ɗaka suka rufe ƙofa, sai ta ga ƙanwarta, sai ta rufe ta da faɗa, ta ce, “Ke wa ya kawo ki nan?”

Ita kuwa ƙanwar sai ta yi shiru.
Shi ke nan sai yar ta ƙyale ta.
Ita yar kamar sokuwa take. In dare ya yi, sai ta yi ta shirgar barci. Ita kuwa ƙanwar, sai ta zauna tangar har gari ya waye.

Sai uwar mijinta ta zo da tsakar dare ta ce:
“Sarma-sarma duf-duf”.
Sai ƙanwar ta ce:
“Wane ne nan ya ke mana
Sarma-sarma duf-duf?”
Sai uwar mijin ta ce:
“Uwar miji ce take muku
Sarma-Sarma duf-duf”.
Sai yarinya ta ce:
“Me kike so kike mana
Sarma-sarma duf-duf?”
Sai ta ce:”Wuta nake so nake muku
Sarma-sarma duf-duf”.
Sai yarinya ta ce:
“Iya ga wuta nan.
Ki bar mana
Sarma-sarma duf-duf”

Sannan yarinya ta watso mata wutar. Tsohuwa ta je ta kashe wutar ta kuma dawo musu. Nan kuwa ashe ba wuta take so ba. So take yi ta cinye su idan ta tarar sun yi barci.
Kullun haka, kullum haka. Duk sa’ad da yarinyar ta gaya wa yayarta game da uwar mijin mai zuwa ɗiban wuta da daddare, sai yayar ta ce, “Ƙarya take yi”.
Ana nan a haka sai, ran nan yarinya ta ce da yayarta, “To, yau dai ki zauna kada ki yi barci don ki ji yadda muke yi da tsohuwar da kunnenki”.

Shi ke nan, yayar ta zauna.
Sai ita uwar mijin ta zo ta yi musu irin yadda take yi kullum.
Shi ke nan, sai ya ta ji da kunnenta.
Shi kuma mijin nata yana wani ɗaki suna kwance tare da abokansa. Idan an yi abinci na aikin gona an kai musu, sai su yi haƙa su bunne. Sai su yi ta cin kwaɗi. Ita kuwa ƙanwar, wadda ta kai musu abincin, sai ta ce da su:
Mijin yayata, ci kwaɗi.
Mijin yayata, ci kwaɗi.
Mazan-wazata, ci kwaɗi
Sha da kwaɗi, ci kwaɗi
Sha da kwaɗi, ci kwaɗi.

Su kuma idan sun ji wannan waƙar, sai su yi ta rawa suna cin kwaɗi.
Shi ke nan. Da sun ga ƙanwar ta dawo daga gida, sai su zama mutane su ce, “Ga kwanukanki nan. ki ce muna yi mata sannu da aiki”.
Shi ke nan, sai yarinya ta ɗebi kwanuka ta tafi da su gida.
Kullum haka, kullum haka.
Sai rannan yayar ta yi shawara da ƙanwarta don su gudu gida.
Sai suka yi ta haƙa rami, tun daga nan gidan har ya zuwa hanyar ƙofar garinsu. Suna ta bin rami da ita da ƙanwarta har suka je gida.
Iyayenta suka ce da ita, “Lafiya?”.
Sai ta ce wa iyayenta, “Ashe dodanni ne? Ni zato nake mutane ne”.
Shi ke nan.
Ƙurunƙus kan ɗan ɓera.
Ba don ƙarya ce ba, wa zai zuba ruwa a jallo, jallo ya fashe kuma ruwan bai zube ba?

Domin karanta tasuniyar gizo da giwa danna nan

Domin karanta bayani akan Ra’in Bincike Hausawa danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Horon Masu Yi Maka Flashing (ɗungushen kira) A Waya
Labarin na GabaWuraren Da Ake Kiɗan Fiyano (Situdiyo)
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.