Yadda ake maraba da mai gida

0
1970

Maraba da mai gida da Rakiya dai ‘yar Kwarya-kwarya karba ce, ko tattaki da ake wa mazaje domin Samar Da natsuwa, soyayya , shakuwa da girmamawa tsakani ma’aurata . Da shi mai gida da matar gida su na kasancewa cikin farin ciki. Sai dai ya na da matukar muhimmacin gaske, Mace ta yi kokari ta dinga kimtsawa.

Annabi (S. A. W) ya kan dawo gida daga tafiya lokacin walha ( da hantsi) kuma ya kan sanar da iyalansa ce wa gashi nan tafe, tun kafin ya iso gida.

Ashe sanar da iyali, dama ce ta su kimtsa , ga mai gida na isowa. Tabbas haka na nuna mana ba’a so Mai gida ya tarar da matarsa a wani yanayi mara kyau.

Annabi (S. A. W) ya ce :”Idan daya daga cikinku ya tsawaita tafiya ka da ya kwankwasawa iyalinsa kofa da Dare. ( Bukhari).

Zan yi bayani ne akan wadannan :

1 – Hanyoyin da ake janyo hankali Mai gida.

2 – Abubuwa da ake yi Lokacin Rakiyar Mai gida.

3 – Abubuwa da ake yi yayin Maraba da Mai gida.

4 – Tambayoyi ga mazaje.

5 – Ra’ayoyin mazaje .

Da farko mu fahimci cewa Mazaje na bambamta a yanayin ayyukansu. Wani aikinsa ba wahala, kuma ya na da isasshe Lokaci. Ya na tashi aiki da wuri. Wani Kuma dole ya wuni cur, ga wahala, ga bashi da lokacin kansa.

Wani dan kasuwa ne, wani ma’aikaci gwamnati ne. Dole ne asamu bambamci a yadda wadannan su ke shiga da fita a gidajensu.

Wasu Kuma Hali, dabi’a ko ince Sabo da yadda su ka ta so tun kuruciya. Za ka ga wani na son zama a gida. Wani dama mai nacewa abokanai ne ( zama a majalisa).

Wasu kyakkyawar manufa ta Kulawa da hakkoki iyalai ke sa su Yawaita waiwayar iyalansu.

Wa su domin irin kwalliyar mata, da yadda ake gyara gida ke kwadaitar da su juyowa gida.

Wasu maza fa duk ba haka ba ne. Illa su na da sa ido. Son gani me ke gudana a gida, ke sa su yawan shiga gida.

Wasu Kuma kazanta , masifa da yadda yara ke hayaniya ce sa ba sa iya waiwayar gidajensu.

Ko ma dai Menene dalili. Ya na da muhimmanci mu yi nazari sosai. Mu ga ne bakin zare da yiwa juna uzuri. Tare da Kawo gyara domin inganta rayuwa Aurenmu.

Wato mu dinga bibiyar hanyoyi tarairaya, soyayya da hikima domin Mai gida ya dinga waiwayowa gidansa.

Idan Mai gida aikinsa mai sauki ne . Ya tashi aiki da yamma. To, asamu ya leko gida kafin ya wuce majalisa hira. Ka da ya zama daga aiki sai majalisa, sai kuma kwanciya bacci. Ki tabbata ki na gyara kan ki da gidanki, domin jawo hankalinsa zuwa gidansa.

HANYOYIN DA AKE JANYO HANKALI MAI GIDA :

Wadansu daga cikin wadannan abubuwa za ki Yawaita yinsu. Har su zama Dabiarki akodayaushe. Wadansu za ki aiwatar da su tun kafin ya iso gida. Wasu Kuma dai-dai lokacin shigowarsa.

1 – Tabbatar da gidanki ya zama akan tsafta Babu wani abinda zai ba ta ma sa rai.

2 – Kasancewa cikin tsafta, da sutura Mai kyau , da kwalliya , da kamshi .

3 – Tanadi abinci da aka kyautata shi. Da Lemo ,da kayan marmari.

4 – Tsaftace baki akodayaushe.

5 – Sakin fuska da yin hakuri. Banda riko ko mita.

6 – Tura sako na soyayya, addu’a, ( text message ) .

7 – Sabarwa kanki da kalmomin soyayya da za ki dinga dukan kunnuwansa da su.

8 – Sabarwa ‘ya’yanki natsuwa. Ka da ya zama koyaushe ba su da aiki sai guje-guje.

9 – Kammala ayyuka na gida akan Lokaci kafin ya shigo. Katse kowanne aiki ya yin da ya shigo.

10 – Tattara hankalinki, tunaninki gareshi. Takaita hira a waya, kallo yayin da ku ke zaune tare.

ABUBUWAN DA AKE YI LOKACIN RAKIYAR MAI GIDA :

1 – Za ki bi shi ki tattaka masa, rakiya har soro ko bakin kofa.
2 – Ki tabbata kin sa turare, ku rabu ya na sheka kamshi turarenki.
3 – Yayin rakiya hada jikinki da nashi ko rike hannunsa na da muhimmanci.
4 – Yanayin kallonki ya zama cikin kauna da tarairaya.
5 – Murmushi a fuskarki.
6 – Adduoi kariya, da nasara, da fatan alkhairi. Addu’ar ki na da tasiri sosai ga mijinki.
7 – Sumba ci Mijinki yayin rakiya.
8 – Rike ma sa abin da zai fita da shi.
9 – Ambato mijinki da suna na soyayya ko girmamawa lokacin rakiya.
10 – Kula masa da adonsa da irin shigarsa. Gyara ma sa hula, kwalar riga Da Sauransu .
11 – Yabawa tsabtarsa, irin kamshin turarensa, da yadda shigarsa tai kyau.

Za ki hada wasu a Lokaci guda. Wasu abubuwa kuwa ki dinga caccajawa.

ABUBUWA DA AKE YI YAYI MARABA DA MAI GIDA :

1 – Ka’idar Maraba da Mai gida sai ki zama wayayyiya ce ba bagidajiya ba. Kar ki Kalli yawan shekarunki, ko yawan yara. A koyaushe Mace awajen mijinta ba ta da wani iyaka na tarairayarsa.
2 – Karanta Lokaci da ya fi shigowa gida. Da irin sauti abin hawa na mai gida .
3 – Duk shigowarsa ki karbi abin hannunsa. Leda ce, jarida, ko ma Menene. Haka girmamawa ce.
4 – Babban abin da za ki mayar da hankalinki daga shigowarsa. Ya fahimci ya shigo wajen iyalinsa. Ki fara bashi magani natsuwa da kwanciyar hankali , ki hada jikinki da shi , ki Sumba ce shi .
5 – Dukkan Miji na da tsanani bukatar soyayya. Ba babba ba Matashi a nan. Ki tarye shi da kalmomin soyayya.
6 – A wani Lokaci ki shirya yadda tun daga maraba za ki shayar da shi bammi na soyayya. Ki bugar da shi Ammafa ba da kayan Maye ba. Ki shayar da shi soyayya ta hanyar shagwaba.
7 – Godiya da jinjina ma sa irin kokarinsa alokacin taryarsa. Wato bayan karba abin da ya shigo dashi. Za ki yi ta godiya komai kankanta abin da ya kawo.
8 – Hakuri da yanayi da ya shigo acikinsa. Cikin gumi, gajiya ko fushi.
9 – Kaucewa tuhuma ayayin maraba. Da ga Ina ka ke? Tuhuma ce. Amma Masoyina duk na shiga damuwa, na jika shiru ne, ina ta jimami ko lafiya kuwa? To wannan zai gane damuwa ce ta kauna, kewa, da Begensa.
10 – Domin samu yiwa Mai gida Maraba da dare. Ki sabawa kanki shan shayi bayan sallar isha. Ki shagalta da nafilfili ko karatun Qur’ani. Shayi zai ba ki karsashi, ya hana ki bacci. Maza dayawa sun fi daukar maraba ta dare da muhimmaci. A dare ake gane zunzurutu kauna, da tausayi. Irin wanda Uwa ce ta fi yinsa. Saboda Uwace ba ta iya bacci komai dare. Sai ta ga danta ya dawo gida lafiya. Kinga ya na da kyau ki sabawarwa kan ki da jiranshi ya dawo kafin ki yi bacci.

11 – Nunawa ‘ya’yanki muhimmaci maraba da mahaifinsu. Da iyaka dai-dai inda za su kauce su ba ku waje. Wato ku samu natsuwa da kula da juna.

12 – Ki zama mai canja salon maraba. Da karance-karance domin ki goge da yadda za ki mu’amalanci mijinki.

A takaice Burinki kullum shine dirsawa mijinki farin ciki ta masa Maraba da Rakiya ta Musamman. Wannan zai Kara miki Kima da daraja . Mijinki ba zai dinga Bari ki na nesa da shi ba. Sai dai fa inda uzuri .

TAMBAYOYI GA MAZAJE
1 – Me maza su ka fi bukata, Matar mutum ta gabatar yayin da zai fita gida?

2 – Menene su ka fi bukata yayin isowarsu gida.

3 – Menene ya sa wasu mazaje ke kokari waiwayowa gidajensu?

4 – Menene ya sa wasu Maza ba su so komawa gida?
5 – Menene abin da ake ma ka da ya fi burgeka Idan za ka fita gida?
6 – Wane abu ya fi burgeka idan ka dawo gida?

7 – Ka na ga rakiyar Mai gida da taryarsa na da muhimmanci?
8 – Ka na iya yabawa rakiya da tarya da ake ma ka? Ta wacce hanya ka ke haka?

RA’AYOYIN MAZAJE :
Na harhade wadanda amsoshinsu ya zo iri daya.

RUKUNI SABBIN AURE
Mu gaskiya munfi bukata ace sumbata tai yawa acikin mu’amalarmu ta Aure. Shi mu ka fi sha’awar samu a duk lokacin da za mu fita gida bayan anrako mu.

Kuma lalle Muna son rakiya har soro. A ganinmu haka na daga cikin Kulawa, da nuna damuwa akalla.

RUKUNI MATASA MASU AURE
1 – Yayin fita gida lalle ayi mana addu’ar neman halak, aje lafiya adawo lafiya. Ta tabbata ka fita cikin tsafta da natsuwa.
2 – Yayin dawowarmu tarfa mai kyau. A barka ka huta. Akaima ruwa ka yi wanka. A baka abinci.
3 – Muna kokari dawowa gida saboda kulawar da ake bamu.
4 – Wasu maza ba sa son dawowa gida ne, saboda rashin zaman Lafiya da iyalinsu.
5 – Abinda ya fi burgemu yayin fita gida, addu’a da ake ma na.
6 – Yayin dawowa fuskantar halin da muke ciki da tausaya mana.
7 – Tabbas rakiya da maraba na da muhimmanci domin tsantsar soyayya ce aciki.
8 – Muna yabawa matayenmu :Muna amsa gaisuwa , da yabon kwalliya.

RUKUNI MATASA MARASA AURE

Na farko duk da cewa bamu da Aure. Abinda mutum zai fi bukata Idan zai fita gida. Matarsa ta duba shi tsaf. Duk wani abu da zai gyara shi ya zama fes. Ta shirya ma sa jikinsa yakamata ace ta riga ta masa. Domin fa Matar mutum tabbas ita ce mudubinsa.

Sai kuma ya zama in zai fita karshen abinda zai kalla(last memory) . Ya zama ita ce acikin siffa ta soyayya. In dai tai haka ma Shikenan , yin haka zai taimaka sosai.

Ataqaice har ma da bayanai sosai daga shugabanni da dattijai masu matukar amfani. Tare da nuni da yadda maza ke tsanani bukata Rakiya da Maraba.

Litattafai da aka duba
Aure A Musulunci

Lacca Aure a Garin Katsina . Satimba 2019.

Men are from Mars Women are from Venus . John Gray, Ph.D.