Mene Ne Shafin Blog

0
367

Blog wani shafi ne da ake buÉ—ewa domin ilmantar da al’umma wani ilmi na daga mai shi wannan shafin; ko kuma tunasarwa a kan abubuwan da suke faruwa a tsakanin al’umma, hakan nan kuma yana a matsayin wata kafa ta yaÉ—a labarai da tallace-tallace.

Abubuwan Da Za a Tattauna:-

A. Menene Blog.
B. Matakan da ake bi wajen samar da shafin na Blog
C. Muhimmancin shafin Blog.
D. Yadda ake amfani da shafin Blog.

A. Ma’anar Blog:

Blog wani shafi ne da ake buÉ—ewa domin ilmantar da al’umma wani ilmi na daga mai shi wannan shafin; ko kuma tuna sarwa a kan abubuwan da suke faruwa a tsakanin al’umma, hakan nan kuma Blog na matsayin wata kafa ta yaÉ—a labarai da tallace-tallace.

B. Matakan Da Ake Bi Wajen BuÉ—e Shafin Blog

Matakin Farko: Zuwa Shafin Domin Yin Rijistar (create your Blog now)

Ka shiga adireshin samar da shafin na http://www.Blogger.com sai ka je inda aka ce create your Blog now; ma’ana ka bude shafinka na Blog yanzu. Sai ka cike sunan da kake son Blog naka ya zama, amma ya zama babu mai irin shi. Haka kuma wannan suna shi ne sunan da zai ba ka damar shiga shafin naka duk san da kake so.

Mataki Na Biyu: Zaɓar Kalmar Sirri (select a password)

Sai ka zaÉ“i lambar sirrinka wato password wanda kake buÆ™atar ya zama, wanda wannan lambar sirrin ”password” yana kamawa daga alamomi guda shida zuwa sama da haka; amma akwai buÆ™atar wajen sanya lambar sirrin ”password” ya zama haÉ—akar baÆ™aÆ™e: lambobi, da kuma wani abin da ba kowane zai iya ganowa ba.

Haka kuma ya zama ka sanya lambar sirrin da za ta yi wahalar ganowa ga wasu, amma mafi sauki a gare ka wajen tunawa.

Mataki Na Uku: (Select a Display Name)

Sai sunan da zai zama na Blog naka, ma’ana DISPLAY NAME; wanda da wannan sunan ne za ka iya amfani da shi wajen shiga ka yi rubutunka domin Æ™aruwar waÉ—anda kake so su amfana.

Abin Lura:

Wajen zaɓar sunan, yana da kyau ka zaɓi sunan da zai kare mutuncin kanka, kuma ya zama babu mai irin sa; domin yin rijista a shafin internet idan da wanda ya riga ka buɗewa da irin wannan sunan; kai sai dai ka nemi wani sunan ko kuma bayan kasanya sunan sai ka sanya wata alama da za ta nuna kai ne ba wancen na farkon ba.

Haka kuma, wannan suna shi ne sunan da zai ba ka damar shiga shafin naka duk san da ka so. Sannan yana da kyau ka sanya sunan da ba zai yi wahalar nema ba.

Mataki Na HuÉ—u : (enter an email address)

Sai ka sanya email address naka, wanda yana da matuÆ™ar muhimmancin sa shi, kasancewar ma idan babu shi rijista ba ta yiwuwa, wanda daga baya ma za ka iya canja wannan email din; domin idan ya zama ya lalace ko ya sami matsala. Haka kuma wannan email, ba zai nuna ba a shafinka na Blog, sai in ka so; domin boyewar zai taimaka maka ka sami tsaro daga masu kutse/mafasa. Bayan ka kamala wannan sai ka karanta dukkanin tsare-tsaren da suke bada damar buÉ—e shafin Blog; ”read terms of services” kafin ka danna zuwa gida na gaba, wato “continue”.

Mataki Na Biyar: Bawa Blog Naka Tittle (Give your blog a tittle)

Wannan shi ne wani suna ko alama da zai ba ka damar ya fito a saman dukkanin wani rubutu da za ka yi; a kan kowanne shafi, sai dai ya danganta da rubutun da za ka yi, kuma ya zama ka canja.

Mataki Na Shida Zaɓar Adireshinka Na Blog: (choose a web address to your blog)

A wannan guri zai ba ka damar zaÉ“ar adireshin da zai yi sauÆ™i wajen samun ka a shafin Blog; wanda kuma zai bayyana ga ma’abota shiga shafin.

Misali http://yourblogspacename.blogspot.com, da ga wannan sai zaÉ“ar tsarin da blog naka zai zama domin kayatarwa wato “template” kada a zaÉ“i dukkan abun da aka gani wajen zaÉ“e a nutsu wajen zaÉ“in; domin samar da kalar da masu bibiyar shafin za ta Æ™ayatar da su. Domin zai iya ba ka damar canjawa daga baya a cikin jerin saiti na shafin. Da zarar ka kamala wannan to shafin ka na blog ya buÉ—u.

C. Muhimmancin Shafin Blog

Dangane da bayannan da ya gabata, a kan mene ne Blog kuma ya ake buÉ—e shi, ku san dai yana da matuÆ™ar muhimmanci musammam ga, masu san su yaÉ—a wasu bayanai da jama’a za su amfana, haka kuma yana da matuÆ™ar muhimmanci ga ‘yan Kasuwa da kuma É—aliban ilmi dama sauran al’umma masu san ci gaba ta hanyar amfani da yanar gizo wato “internet” a Turance.

D. Yadda Ake Amfani Da Shafin Blog

Da zarar ka samar da wannan shafi na blog domin watsa rubututtukanka. Shi kenan sai farawa, yadda ko za ka fara shi ne :
Bayan ka buÉ—e shafin naka, sai ka shiga “start posting” inda a nan ne za ka sami damar tsara rubutunka da kuma watsa shi. Shirya tsari mai Æ™ayatarwa domin jan hankali wato “tittle”; sai ka rubuta rubutun ka haÉ—i da cika ka’idojin rubutu domin mai karatu ya fahimta.

Sannan bayan ka kamala sai ka dannan kan “publish post” da hakan shi zai ba ka damar rubutunka ya tafi duniya kuma ya zama duk wanda ya bi cikin internet a kan abu makamancin naka; to zai ba shi damar ganin rubutun tare da saÆ™on da kake son isarwa.

Haka kuma, idan kana buÆ™atar wani ya je ya karanta sai ka gaya masa “tittle” na saÆ™onka; ko rubutunka wanda da zarar ya bincika zai samu.

Duk lokacin da ka sanya sabon rubutu a kan Blog naka, yana da kyau ka watsa shi domin amfanuwar mutanen da kake so su amfana, saboda haka wasu ma idan suka nemi makamancin abin da ka sanya za su gani su ƙaru .

Domin neman Karin bayani za ku iya samu na a 08087633060.

Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Ya Kamata Ka Sani Dangane Da Twitter danna nan