Physiology da Hausa Kashi na Bakwai: Respiratory System (Sashin Numfashi)

0
79

Ya ƙunshi wasu gaɓoɓi da suke haɗuwa su yi aiki a tare, domin a samar da numfashi.Wannan gaɓoɓi sun haɗa da: Hanci, maƙogaro, bututun numfashi da huhu.

Ta yaya iska ke shiga cikin huhu kuma ta fita?

Iska na shiga cikin huhu a sauƙaƙe ta cigaba da tafiya zuwa bututun numfashi. Bututun ya rabu zuwa matakai biyu. Akwai matakin isarwa da kuma matakin karba da bayarwa na sinadaran iska. Matakin isarwa ya kasu kashi 16. Matakin karɓa da bayarwa ya kasu kashi 7

Mene ne fa’idar sashen numfashi?

1.Samar da iskar oksijin zuwa cikin jiki, yayin da ake buƙata. 

2.Fitarda iskar kabon dai okzaid (CO2)

Daga jiki zuwa wajen duniya. 

3.Sassaita Ph wato adadin asid na jiki. 

4.Sassaita dumin jiki. 

5.Samarda sinadarin Sofaktant (Surfactant). 

6.Ba da kariya daga ƙwayoyin cuta. 

Mene Numfashi.

Shi ake kira da ventilation a Ingilishi. Wato shiga da fitar iska a jiki.

Yana dakyau ka/ki karanta Physiology da Hausa kashi na hudu: Autonomous nervous system (Sashin Bada Umarni Da Amsa Saƙo)

Ƙarfin talewar huhu( Elastic properties):

Akwai ɓangarori a ckin hunhu da suke ɗauke da kayan ba wa huhu damar talewa. Ana kiransu da Elastic fibers. Sannan akwai surfactant wanda amfanin shi ya ba wa iska damar ratsa wannan buhun numfashin. Kuma ana samar da surfactant ne yayin da  ya cika sati 32 a cikin mahaifiya. Shi yasa bakwaini yawanci suke zuwa da matsalar numfashi, saboda babu sinadarin surfactant da zai sauƙaƙe shiga da fitar iska.

Haɗin kai na huhu (Lung Compliance):

Shi ne haɗin kan da huhu ke bayarwa yayin da iska ta shiga ta hanyar talewa da tsukewa.

Karɓa da bayarwa na iska tsakanin buhun numfashi da jijiyoyin dake zagaye da shi. Da kuma tsakanin ƙwayar halitta (Cell) da kuma jijiyoyin da suke bakinsa: 

Jini mai ɗauke da iskar oksijin (oxygen) yana dira zuwa buhun numfashi(alveoli) domin ya bawa jijiyoyinda suke zagaye da shi. Shi kuma jini na ɗauke da Sinadarin hemoglobin da mukai bayani a baya, wanda ke da ɗakuna da suke ɗauke da wannan iskar domin tafiya a kai su zuwa ka ƙwayoyin haluttu. Hakan na faruwa ne saboda ƙarfin haɗuwa, homoglobin da oksijin ya fi ƙarfi a bakin buhun numfashi sannan ƙarfin na raguwa ne yayin da hemoglobin ya isa bakin ƙwayar halitta, inda zai buɗe domin ba wa ƙwayar halitta oksijin (oxygen) ya kuma karɓi iskar kabon dai okzaid( carbon dioxide) domin ƙarfin haɗuwarsu ya fi ƙarfi a bakin ƙwayar halitta, sannan ya fi rauni a bakin buhun numfashi, ta haka ne iska ke yawa a cikin jiki.

Domin karanta Physiology da Hausa kashi na biyu: Body Fluids (Ruwan Jiki) Ruwan dake jikin ɗan Adam Danna nan

Masaitin numfashi

Sashin ƙwaƙwalwa na cerebral cortex shike kula da numfashin da muke da iko a kai. 

Sashin ƙwaƙwalwa na respiratory center wanda ke ɗauke da Medulla oblongata da pons suke kula da numfashi wands ba mu da iko a kai.

Mene ne Hypoxia da cyanosis.

Hypoxia: Asalin kalmar ta zo ne daga kalmomi guda biyu. Hypo yana nufin ƙaranci. Oxia yana nufin oxygen. Saboda haka, ma’anarsa shi ne ƙarancin sinadarin iskar oksojin (oxygen) a cikin jiki wanda kan iya ba wa ciki matsaloli da dama.

Cyanosis: Alama ce dake nuna cewa babu isasshen sinadarin iskar oksijin a jini. Alamar kuwa ita ce, mutum zai zama shuɗi a kamanni. 

Domin karanta Physiology da Hausa Kashi na Shida: Hematology (Jini da Abun da ya Ƙunsa) Danna nan

labarin da ya wucePhysiology da Hausa Kashi na Shida: Hematology (Jini da Abun da ya Ƙunsa)
Labarin na GabaPhysiology da Hausa Kashi na Takwas: Gastrointestinal System(Sashin Sarrafa Abinci)
Dr. Yasir Aminu Ado
Ni dalibin likitanci ne nayi karatun likitanci a Kasar Sudan, Ina koyar da daliban jami'a masu tasowa ilimin karutun likitaci a saukake cikin harshen Hausa