Nerves da tsoka su ne gaɓoɓin motsi, domin su suke dauke da signal mai nau’in lantarki wadda ake cewa action potential.
Resting Membrane potential Shi ne bambancin saƙon lantarki dake tsakanin ciki da wajen ƙwayoyin halitta a lokacin da ba a motsi. A yayin da ciki yake da fiye da waje.
Abubuwan dake jawo resting membrane potential
a.Fitowar potasiun wajen k h
b.Shige da fitar sinadaran Na da K
Action Potential Yana aukuwa ne a gaɓoɓin motsi kawai wato nerves da tsoka.
Shi ne sauyin da ke aukuwa a bakin ƙwayar halitta domin yin motsi wato depolarization and repolarization ta hanyar yunƙurin yin aiki, lantarki ko sinadarai.
Abubuwan da ya ƙunsa
A.Stimulus artifact: Yana faruwa ne a lokacin da aka zaburarar da wannan gaɓoɓi ma’ana wannan shi ne mafarin A.P
B.Latent Period: Tsaka-tsakin lokacin da ke zaburar da gaɓoɓi da kuma lokacin da za su fara motsi.
C.Threshold: Shi ne yanayin da ƙofofin dake ba wa sinadarin sodiyom damar shiga ke buɗewa. Idan ba a cika wannan threshold ɗin ba AP ba zai auku ba.
Domin karanta Ilimin Fisiyoloji (Physiology ) Cikin Harshen Hausa Kashi na Farko Masaitin jiki (Homeostasis) Shiga nan
Depolarization
Shi ne yanayin da sodiyom ya shiga cikin ƙwayar halitta, yunƙurin zai tafi a daidai har sai sinadarin potashiyom ya fara fita. Saboda haka idan ƙofar ta rufe, ba ta ƙara buɗewa har sai AP ya dawo farko domin a sake maimaitawa.
Repolarization
Saboda fitar sinadarin potashiyom. Ƙofar da sinadarin potashiyom ke fita tana buɗewa ne bayan ta sinadarin sofiyom ta buɗe, ma’ana ƙofar sinadarin sodiyom ta fi saurin buɗewa. Haka zalika, ƙofar fitar potashiyom ita ce ke rufewa, a ƙarshe bayan ta sinadarin sodiyom ta rufe.
Tsarin AP
All or none law
-Indai zaburar da gaɓoɓin motsi bai kai threshold ba, ba za a samu AP ba. Ma’ana kafin gaɓoɓi su motsa sai sinadarin sodiyom ya shiga yadda ya kamata ko kuma ba abinda zai faru.
-Refractory period
Dawowar jiki yadda yake kafin ya motsa: A wannan yanayin ne ƙofofin dake ba wa sinadarin sodiyom damar shiga ke rufewa ko ke daina aiki.
Conduction wato isarwa: Saƙon AP na zuwa ga inda ake so ya je ta hanyar lantarkin jiki wato neurons
Conduction: wato isar da saƙo ba ya canja saƙo a kan hanya.
Nerve wato ɗan aike na lantarki a jiki, yana baje burjuk a cikin CNS ƙwaƙwalwa da laka. Wanda a cikinsu sun ƙunshi ƙwayar halittarsu wanda ake kira da neurons.
Ya ƙushi gaɓoɓi guda uku: Kai da jiki da kuma jelat.
Yayin da kai yake ɗauke da dendrites da cell body wato inda ke sarrafa saƙo. Jiki kuma myelin sheath. Jelat kuma yayin da saƙo na shiga ne ta kan bi ta jikin, ya kuma fita ta jelat, wato ya miƙa zuwa ga neuron.
Synaptic junction
Shi ne mahaɗar Neurons guda biyu.
Yana ba da damar saƙo ya ci gaba da tafiya daga wannan neuron zuwa wancan. Wannan shi ake kira da Chemical transmission wato neuron na gaba na zabura ne ta hanyar amfani da wasu sinadarai da neuron na farko ke saki, sai na biyu ya ɗauka, sai ya zabura.
Ɗabi’un Synaptic junction
Transmission is uni-directional wato isar da saƙo na tafiya ne a hanya ɗaya, ma’ana daga presynaptic zuwa post synaptic neuron.
Synaptic delay. Adadin lokacin isar da sinadarin da zai zaburar da neuron na gaba ba ya wuce 0.5ms
Synaptic fatigue: Idan sinadarai suka shiga da yawa, ma’ana ɗaya na bin ɗaya, hakan zai sa ya gaji, a kasa isar da wannan saƙon.
Neuromuscular junction:
Mahaɗar neuron ne na musamman wanda ya ƙunshi neuron da tsoka. Saƙo na wanzuwa a wannan kamar yadda saƙo ke gudana ta hanyar yin amfani da sinadari. Sai dai a wannan lokacin tsoka na amfani da sinadarin Acetylcholine domin karɓar saƙo.
Ire-iren tsoka a jiki iri uku ce:
- Skeletal wato wadda ke tare da ƙashi.
- Cardiac wato wadda ke zuciya.
- Smoth.
Sannan yana da matukar muhimmanci ku karanta Physiology da Hausa kashi na biyu: Body Fluids (Ruwan Jiki) Ruwan dake jikin ɗan Adam
[…] Domin karanta Physiology da Hausa kashi na uku: Excitable Tissues (Sassan motsi na jiki) Danna nan […]