Tag: kimiya da fasaha

  • Ilimin Fisiyoloji (Physiology ) Cikin Harshen Hausa Kashi na Farko Masaitin jiki (Homeostasis)

    Ilimin Fisiyoloji (Physiology ) Cikin Harshen Hausa Kashi na Farko Masaitin jiki (Homeostasis)

    Fisiyoloji (Physiology) Ilmin sanin yadda jikin ɗan Adam yake aiki da kuma aiwatar da dukkan al’amura na jiki. 

    Darasi na farko da ake fara yi a Jami’a shi ne Homeostasis (HO-MI-YOS-TE-SIS) wato masaitin jikin ɗan Adam yana nuni da cewa: kowane sashe na jiki na da hadafi guda ɗaya, shi ne su tabbatar da daidaito a cikin jiki ta hanyar amfani da ruwan dake;

    Kowanne jiki na ɗauke da ƙwayoyin halittu wanda ake ke kira da “cells”. 

    Waɗannan ƙwayoyin halittu su ne suke haɗuwa da wasu su samar da sashe wato na jiki (organ system) . 

    Sannan waɗannan sassa su haɗu suke samar da ɓangaren jiki wato system. 

    Saboda haka, gaba ɗaya jikin ɗan Adam na da ƙwayar halitta wato cells.

    Kowacce ƙwayar halitta na ɗauke da ruwa, sannan a wajen su akwai ruwa kuma suna zagaye da ruwa. Ma’ana ruwan dake waje da ruwan dake ciki (ciki ko wajen ƙwayoyin hallitta). 

    Ruwan dake wajen ƙwayoyin halitta su ne mahadar jikin ɗan Adam da wajen duniya. Domin shi ne yake isar da abincin da aka gama sarrafa shi, wato nutrients zuwa ga ƙwayar halitta sannan ya fitar datti ko abinda ciki bai buƙata daga ciki.

    Saboda haka, yana gudana a cikin jikin ɗan Adam a ko’ina domin aiwatar da aiki yadda ya kamata.

    Homeostasis:

    Wato masaitin jikin ɗan Adam yana nuni da cewa: kowane sashe na jiki na da hadafi guda ɗaya, shi ne su tabbatar da daidaito a cikin jiki ta hanyar amfani da ruwan dake waje ko a zagaye da ko wani sashi ko ƙwayar hallitta ta jiki.

    Bisa haka ne kowane sashe na jikinmu na aiwatar da daidaito ko saiti a yayin buƙatar hakan, misali canjin yanayi.

    Ga wasu abubuwa da zan lissafo wanda da su jiki yake amfani wajen saiti.

    Adadin  ruwa dake jikinmu, Abubuwan da ruwan ya ƙunsa, PH wato , Karfin gudanar sa da kuma ɗumin sa.

    Misalai;

    Sashin numfashi na tabbatar da daidaiton ruwan dake wajen ƙwayoyin halitta ta hanyar

    sassaita PH. 

    Sashin Endocrine na tabbatar da daidaiton ruwan dake wajen ƙwayoyin halitta ta hanyarsassaita Dumin jiki. 

    su kuma Sashin zuciya da jijiyoyi na tabbatar da daidaiton ruwan dake wajen ƙwayoyin halitta ta hanyar sassaita ƙarfin gudanar jini. 

    Sashin sarrafa fitsari na tabbatar da daidaiton ruwan dake wajen ƙwayoyin halitta ta hanyar sassaita adadin gishirin da abinda za a tace yake ɗauke da wato Osmolarity.

    Homeostasis wato masaiti na bamu dama a yanayi daban-daban (misali a lokacin zafi ko lokacin sanyi) tare da tabbatar da cikin jikinmu ya kasance a sassaite.

    Ta yaya Masaiti wato homeostasis ke aiwayar da aiki? 

    Hakan yana yiwuwa ne ta hanyar tsari da jiki yake da shi, wajen yin yunƙuri ko amsawa idan ya ji canjin yanayi iri biyu kamar haka:

    1. Yunƙurin ƙari

    2. Yunƙurin ragi

    -A yunƙurin ƙari jiki kan yunƙura domin ƙari a kan wani amshi da jikin mutum ya yi a yayin canjin yanayi. 

    Misali idan mutum ya  ji rauni (ciwo), jijiya ta ɓarke jini ya rinƙa zuba, saboda haka, domin tsayar da wannnan zubar jini, wasu ƙwayoyin halitta dake cikin jini wanda ake kira da platelets za su yi jami, su taru a inda jinin ke zuba, amma adadinsu kaɗan ne. 

    A wannan lokacin ne tsarin yunƙurin na ƙari zai sa a ƙaro platelets a wajen zubar jini sai zubar jinin ya tsaya. Daga nan an samu daidaito kenan.

    -A yunƙuri na ragi kuma, jiki ya ruga ya yunƙura domin daidaito da canjin yanayi amma cikin jiki na buƙatar rage wannan yunƙurin domin saiti.

    Misali idan muka fita cikin zafi ko rana, 

    jikinmu yakan ɗauki zafi, a wannan lokacin ne sai yunƙuri na ragi ya sa mu yi gumi domin ruwa mai ɗumi dake cikin jiki, sai jikinmu ya huce ya sanyaya, daga nan samu daidaito kenan.

    Danna koren rubutun nan domin bibiyar mu a shafin mu na youtube idan mun Dora sababbin bidiyo ko shafin mu na facebook ko Instagram 

    Kalmomi

    • Physiology 
    • Homeostasis 
    • Cell
    • Organ
    • Endocrine
    • Osmosis

    Inda aka samo wannan bayani

    Dr Tariq Hakim. THE CORE OF MEDICAL PHYSIOLOGY.3rd ed.Khartoum university pp;2010.

  • Yadda Ake Dawo Da Transfer Pin Na MTN Network Da Aka Manta

    Yadda Ake Dawo Da Transfer Pin Na MTN Network Da Aka Manta

    Wasu daga cikin masu son amfani da tsarin transfer na kuɗi a kan layinsu; amma hakan ba ya yiwuwa, sakamakon ka manta PIN ɗinka na transfer; ko ka manta, tunda watakila da kana yi amma kuma yanzu ka manta PIN.

    To ga yadda za ka yi ka dawo da Transfer Pin na MTN naka cikin sauƙi;


    Kawai tura sako da kalmar ”YES” zuwa 556 a kan layin da kake da buƙatar PIN na transfer naka, sai ka jira na ɗan wani lokaci kaɗan, za su dawo maka da reply da cewar;

    ”Welcome to share & Sell, your default PIN is 0000. Wato wannan ya nuna cewar setin da ka yi na da na transfer yanzu an wargatsa shi, sai ka sake sabon rijista, wato sun ba ka dama ka canza PIN zuwa wanda kake da buƙata, tunda ba sa transfer da ”Default PIN 0000”.

    Domin ka canza PIN nan take saika tura da sabon PIN wanda suka ba ka, da kuma kalar wanda kake da buƙata wato text ”Old PIN>New PIN>New PIN” zuwa 556.
    Old PIN naka shi ne 0000. New PIN kuma shi ne wanda kake so, ana bayar da tazara a tsakani.

    Misali:

    Text “0000 2326 2326” zuwa “556”.
    Kana turawa ɗan wani lokaci za ka karɓi saƙo da cewar
    ”Your PIN has been reset”. Thank you!!

    Da bin duk matakan nan, shi ke nan, ka dawo da MTN Transfer Pin naka wanda ka manta.

    Domin Karanta Cikakken Bayani A kan Yadda Ake Amfani Da Kafar Sadarwa Ta Whatsapp danna nan

  • Yadda Ake Amfani Da Kafar Sadarwa Ta Whatsapp

    Yadda Ake Amfani Da Kafar Sadarwa Ta Whatsapp

    Sau da yawa mutane na mu’amala da kafar social media ta whatsapp; amma akwai tarin abubuwa da ba su san yadda ake amfani da su ba yadda ya dace; ko kuma ba su san yadda za su aiwatar da wasu abubuwa ba.

    Waɗannan wasu kadan ne daga cikin irin abubuwan da ake iya aiwatarwa da ba kowa ya sani ba:

    TURA SAƙO GUDA ƊAYA GA MUTANE DA YAWA (BROADCASTING)

    Wannan wata hanya ce da ake tura saƙo guda ɗaya zuwa ga mutane da yawa; da zarar ana son a yi wannan; sai a tafi kan MENU inda ke da wasu alamomi guda uku.

    Sai mutum ya zaɓi Broadcast wanda a nan ne zai ba ka damar tura saƙon zuwa ga mutane da yawa

    SAUYA NAU’IN RUBUTU

    Wanna ma wata alama ce da za ka iya sauya nau’in rubutu, misali ya tafi a kwance ko kuma ya yi kauri ko ya zama a cikin alamar sokewa.


     Domin tafiyar da rubutu a kwance sai a rubuta _rubutu_ sai a tura.
     Idan kana so ka sanya rubutu ya yi kauri, sai a yi amfani da *rubutu* sai a tura.
     Haka ma idan kana son alamar sokewa sai a yi amfani da ~rubutu~ sai a tura.

    Domin Karanta Cikakken bayani a kan Yadda Ake Amfani Da MyMTN App Domin Gano Wasu Muhimman Bayanai Akan Layin Ka Na MTN danna nan

  • Shin Me Ake Iya Yi Da Komfiyuta?

    Shin Me Ake Iya Yi Da Komfiyuta?

    Mutane da dama suna amfani da Komfiyuta wurin samun sauƙin aikinsu na yau da kullum. Misali idan muka duba; mutum zai iya ɗauko aiki daga ofishinsa zuwa gida domin ƙarasa aikin da ya fara a can.

    Haka ɗalibai suna iya ci gaba da nazari ko binciken da suka fara a Komfiyutar makaranta idan sun dawo gida, wannan aiki kuwa mutum zai iya yin amfani da safe ko da rana ko cikin dare;

    Haka mutum zai iya amfani da wannan kwamfutar domin tafiyar da harkokin kasuwancinsa ta hanyar rubuta wasiƙa; ko waɗansu bayanai masu muhimmanci na kasuwancinsa, ko kuma shirya kasafin kuɗi.

    A taƙaice dai duk wani irin aiki da za ka iya yi da Komfiyutar wurin aiki; za ka iya yin shi da kwamfutar da ita a cikin gida.

    Lura Da Hada-Hadar Kuɗaɗe Da Kasuwanci

    Ba ka buƙatar zama ƙwararren masanin harkokin kuɗi wurin kula da kuɗaɗenka da kasuwancinka idan aka zo maganar Komfiyuta.

    Akwai waɗansu manhajoji a cikin Komfiyuta waɗanda da su za ka iya lura da kuɗaɗe kamar irin su Microsoft money ko kuma Quicken wanda da waɗannan za ka iya shirya kasafin kuɗi.

    Ko kuma rubuta takardun karɓar kuɗi ko kuma bincikar labarin ragowar kuɗaɗen da suke asusunka; da ke bankinka take daga jikin kwamfutarka ba tare da kana da ilmin a kanta ba.

    Haka zalika, za ka iya sanya kwamfutarka ta ɗauki ragamar biyan kuɗaɗe ta banki da kanta na haƙƙoƙin jama’a ko biyan kuɗaɗen harajin gwamnati, wanda ba sai ka je banki don gabatarwa ba.

    Ƙulla Alaka Tsakanin Mutane

    Da kwafuta ana iya aikawa da wasiƙa wacce ake kira da imel [email] ga ‘yan uwa da abokan arziƙi ba ka buƙatar jiran lokaci mai tsawo kafin wannan saƙo ya kai ga wurin daka aika shi.

    Haka ana amfani da kwamfuta wurin yin magana ko muhawara da jama’a kai tsaye ta hanyar amfani da intanet.

    Ko kuma kiran kwamfuta da wata kwamfuta wanda aka fi sani da pc to pc call; wannan duk wani sauƙi ne ake samu a wurin kwamfuta.

    Yin Hada-Hada A Intanet

    Kamar yadda muka faɗi, amfani da fasahar email ya kawo sauƙi wurin aikawa da saƙonni haka ma intanet.

    Internet wata kafa ce da mutane ke amfani da ita wurin gabatar da abubuwa masu muhimmanci da kuma aikace-aikacen da suka saba yi a zahiri da jama’ a.

    Kamar gabatar da harkokin kasuwanci wanda ya haɗa da sayarwa, yin karatu da manyan jami’o’i na duniya, karanta jaridu da mujallu duk a kan intanet, alhali mutum na zaune a gida ko ofishinsa waɗannan kaɗan ne daga cikin irin aikace-aikacen da ita komfiyuta take iya yi da kuma sauƙin gabatar da al’amura.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Komfiyuta (Computer) danna nan

  • Yadda Hashtag Yake

    Yadda Hashtag Yake

    Hashtag wani abu ne da aka samar da shi domin ƙulla alaƙa tsakanin rubutu masu alaƙa da juna.

    Ana amfani da Hashtag wajen neman rubutu masu alaƙa da juna a shafukan yanar gizo.

    Ko kuma, wani abu ne da ake amfani da shi a twitter da sauran kafafan sadarwa kamar facebook da makamantan sa;

    Wanda zai ba ka damar yin post ko kuma tattaunawa da shi.

    Misali wani kan iya yin amfani da #computer hashtag domin ya sanar da wasu ko kuma masu harkar computer. Da ma wani wanda yayi rubutu akan abun da ya shafi ita kan ta computer din.

    Hakan nan kuma dukkanin #Hashtag yana farawa ne da wannan alamar “#” kafin kalmar da za a sanya.

    Sannan wannan alamar ana iya nemo ta a kan computer keyboard ta hanyar danna madannin Shift haɗi da inda hoton # din yake. Misali shift +

    Domin Karanta cikakken bayani a kan Amfani Da Haɗurran Shafukan Sada Zumunta danna nan

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Dawo Da Abun Da Aka Goge Akan Komfiyuta danna nan

  • Yadda Ake Buɗe Modem Ya Yi Aiki Da Kowanne Irin Layi

    Yadda Ake Buɗe Modem Ya Yi Aiki Da Kowanne Irin Layi

    Modem: Barkan ku da warhaka, ‘yan uwa daliban ilimin fasaha, yau na zo muku da sabon bayani a kan yadda ake buɗe modem ya yi aiki da kowanne irin layi(sim).

    Wanda bayan ka buɗe shi kana da damar sanya dukkanin layin daka ga dama a ciki, domin yin aiki da shi.

    Haka kuma, da yawa wasu sukan bada kuɗaɗe masu yawa wajen ganin sun aiwatar da wannan aiki.

    Amma a wasu lokutan ba a da buƙatar sai an buɗe shi da mabuɗin lambar buɗewa, sai dai a ɗan yi wasu saite-saite kamar yadda zai zo a ƙasa, misali wajen chanja setin na APN, misali idan kana da modem na kamfanin Airtel, sai ka bi wadannan matakai domin saita shi ya yi aiki da layin MTN ko wani layin.

    • A buɗe cikin Airtel Setting wizard.
    • A je cikin Configuration Setting sai ka zaɓi APN.
    • Sannan a chanja sunan APN (misali idan kana son ka sanya layin da ba na Airtel ɗin ba sai ka chanja airtelgprs.com zuwa ga mtngprs, ko makamantan sa).
    • Sai a ajiye Settings ɗin.

    Yanzu sai mutum ya yi connecting ɗin modem nasa zai ga ya yi connecting (wanda wannan yana aiki a cikin modem na Airtel ne kawai – Huawei E1731).

    Hanya Ta Biyu Da Ake Amfani Da Ita Wajen Bude Modem

    Yadda ake yi shi ne, a sami masarrafin (software) na UNIVERSAL MASTER CODE GENERATOR, wanda da yin amfani da wannan za a iya buɗe ZTE, NEC, LGkg110, Nokia, Huawei, VK ne kaɗai.

    Idan ana son a bude daya daga cikin wadannna modem din, sai a bi matakan da zasu zo, a kasa.

    1. Ɗauko Universal Master Code Software.(za ka iya sauke wanann masarrafin daga kan wannan link din. http://www.opendrive.com/files/12363728_miv7O_b84d/UniversalMasterCode.zip ).

    2. Mataki na 2 -> Bayan an ɗauko wannan software ɗin sai a danna kansa sau biyu, wanda ba ya buƙatar wani installation. A duba hoton dake kasa za a ga yazo kamar yadda yake a hoton nan.

    3. Shigar da nambar IMEI number, wacce tazo a jikin modem din.

    4. Yanzu sai ka dannan kan Calculate; zata kirga maka nambar budewar UNLOCK code da kuma nambar sharewa FLASH code.

    Abin Lura:

    Bayan an ƙirga nambar buɗewar Unlock code da kuma nambar sharewa flash code; sai ka sanya wani layin da ba na wannan modem ɗin ba, misali idan modem ɗin na MTN ne sai ka sanya layin GLO ko wani layin daban; bayan ka jona moden ɗinka da computer naka ka sanya shi, zai tambaye ka, ka sanya nambar buɗewar kodai Unlock code ko Flash code, sai ka sanya ɗaya daga cikin abun da ya tambaya, sai ka yi connecting da yanar gizo-gizo, wasu lokutan kuma wasu modem ɗin ba sa buɗuwa da wannan tsarin, sai dai da wata hanyar ta daban.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Menene Shafin Blog danna nan

  • MyMTN APP: Yadda Ake Amfani Da MyMTN App Domin Gano Wasu Muhimman Bayanai A Kan Layinka Na MTN

    MyMTN APP: Yadda Ake Amfani Da MyMTN App Domin Gano Wasu Muhimman Bayanai A Kan Layinka Na MTN

    Wannan wani masarrafi ne wanda kamfanin sadarwa na MTN ya samar wa abokan hurɗarsa domin aiwatar da wasu ayyuka na musamman, domin daɗa ba su damar sani da fahimtar bayanai a kan layukansu na sadarwa. Yana da amfani matuƙa, bayan ka san bayanai a kan layinsu na sadarwa, a ce ka san yadda masarrafin MyMTN App yake. Ga bayanin nan daki-daki a ƙasa a sauƙaƙe:

    Yadda Masarrafin Yake:

    Shi dai wannan masarrafi sunansa shi ne MyMTN App kuma ana iya sauke shi daga kasuwar hada-hadar masarrafai ta kamfanin Google wato Google Playstore wanda da zarar ka ɗauko shi (MyMTN App) sai ka sanya shi a wayarka, ma’ana ka yi (installing), bayan ka yi installing ne zai ba ka damar ka sanya lambar wayarka don yin rijista (register).

    Sai ka sanya lambar wayarka domin tabbatar da buƙatarka, wanda da zarar ka sanya lambar wayar taka, wani saƙo nan take mai suna (OTP=One Time Password) lambar sirri ta lokaci guda, zai shiga cikin wayar da aka sanya lambar ta a cikin wannan masarrafi, sai a ɗauko wannan lambar a sanya ta a cikin gurin da shi wannan masarrafin ya bukata kamar yadda yake a hoton da yake ƙasa.

    Da zarar ka gama da rijista, sukan bayar da kyautar 500MB.

    Da zarar an sanya cewa, an amince da ya buɗe, wanda hakan zai bayar da damar ka ga abubuwa kamar haka:

    1. Cikakken sunan da aka yi rijistar layin da shi.
    2. Tsarin da layin ka yake kai.
    3. Yawan adadin kudin kiranka.
    4. Tarihin kiraye-kirayen layi.
    5. PUK lambarka ta layi.
    6. Bayar da damar shigar da akwatin sako na Email.
    7. Bada damar sayen kati ko data daga bankinka, sannan suna ba da damar saka wa wani kati a layinsa.
    8. Sanya hoto domin daɗa tabbatarwa.

    Wannan shi ne cikakken bayani a kan yadda ake amfani da MyMTN App a sauƙaƙe.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Amfani Da Status Saver Na Whatsapp danna nan