Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Iyaye Mata A kan ‘Ya’yansu Mata

0
1793

Ina farawa da sunan Allah mai rahma, kuma mai jinƙai, Wanda yake ara min iko da har dubun nan bayinsa suke karanta rubuce-rubucena a kafar sadarwa ta zamani.

Yakan ba ni iko ne ba wai don na isa ba, ko kuma na kai ba, sai domin ya nunawa al’umma ayarsa ta halittar ƙwaƙwalwa a kaina, mai fitar da abin da ake mamakin fitar sa, sarki ɗaya tilo wanda bashi da kishiya.

A karon farko wannan ne rubutuna da harshen Hausa a maimakon da can da nake yi da harshen Bature wato Ingilishi, na yi hakan ne domin iyayenmu mata su samu sauƙin fahimtar saƙon da nake son isarwa a kan ‘ya’yansu mata

Ina mai amfani da wannan dama, domin nusar da iyaye mata da su ƙara zage damtse a kan yadda suke, su saka ido a kan rayuwar ‘ya’yansu ta yau da gobe, abubuwa suna faruwa sosai wanda kuma wani lokacin ƙawayen ‘ya’yan ne sanadi.

Ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne, Kai a waye ya kamata ki kira ‘yarki, ku zauna daga ke sai ita, ki ci gaba da ba ta shawarwari a kan ta kiyaye mutuncinta da kuma mutuncin gidan da ta fito, saboda tarwatsewar tarbiyyarta daidai yake da taɓarɓarewar al’umma baki ɗaya, kamar yanda Annabi S.A.W ya faɗa a cikin hadisi “…Idan mace ɗaya ta lalace, to al’umma ce gaba ɗaya ta lalace”.
A matsayina na ɗalibi a Jami’ar Bayero ta Kano, a da can na ga yadda kowa yake tafiyar da rayuwarsa a kan tafarkin da iyayensa suka ɗora shi, kenan ya zamo babban nauyi ne, da Allah ya ɗora wa iyaye mata wanda ya kamata su jajirce domin ganin sun sauke wannan nauyi wanda ya rataya a wuyansu.
Akwai wani lokaci ba zan taɓa mantawa ba, ina zaune a makaranta wani bawan Allah wanda ba zan kama sunansa ba, ya zo ya same ni, ya ce, “Shi fa babu abin da ya tsana sama da ya ga ina rubutun fadakarwa a kan abubuwan dake faruwa a Jami’a”. Na kawo wannan magana ce ba wai don na ci masa mutunci ba sai dai domin na kafa hujja da cewar abubuwan dake faruwa a Jami’a sai an sa ido sosai kuma an dage da addu’a domin gudun da-na-sani)

Za ka ga yarinya ta taso daga gidan mutunci da kamala, amman a sanadin haɗuwa da ƙawa mai son abin duniya, za ka ga ta zubar da mutuncinta, wannan abin kunya ne kam, a maimakon kiyaye mutuncinta, saboda kunnen ƙashi sai kawai ta siyar da shi a kan farashi mai rahusa, sun manta da Suratul Maryam aya ta 86

Inda Allah (S.W.T) yake cewa “Kuma muna kora masu laifi zuwa jahannama, gargadawa {Wanasuqul majrimina ila jahannama wirda}”…Bayan wannan kuma akwai inda Allah S.W.T yake faɗa wa Annabi (S.A.W) a cikin Suratul Maryam Aya ta 83 cewar “Shin ba ka gani ba cewa mun saki shaiɗanu a kan kafirai suna susuta su ga masu zunubi, susutawa?
Ma’ana idan shaiɗanu sun ga mai wa’azin gaskiya, sai su dinga susuta mabiyansu domin su yi faɗa da mai wa’azin, domin kada su saurare shi, har su gane ɓatan su, Shaiɗan shi ne mai ɓatar da wani mutum ne ko aljan.
Shekara ɗaya da ta gabata, wani bawan Allah wanda ba zan kama sunan shi ba, ya zo har inda nake, ya zazzage ni, na tambaye shi ko mene ne dalilin zagina da ya yi? Kun san me yace min kuwa? Wai akwai wata yarinya wadda suka yi da ita cewar za su haɗu, su je yawon ashararanci tare, sai kawai ya ji ta kirasa a waya, ta ce masa “Ya hau WhatsApp”. Hawansa ke da wuya, sai kawai ta tura masa wani rubutuna da nake magana a kan hukuncin aikata zina, nan take ya kira ta a waya ya ce mata, “Na gani, sai akai yaya?” sai ta ce masa, “Sai mu daina aikata aikin haram”.
Ya ji haushin abin matuƙa a lokacin, amman cikin ikon Allah sai ban neme shi da rigima ba, na ba shi shawarwari a nutse, to yanzun haka dai bawan Allan nan shima, ya tuba ya daina abin da yake yi, Allah gafurur Raheem ne, ya kamata iyaye su zaunar da ‘ya’yansu mata, su tuba kafin su koma gare shi.

A game da rubuce-rubucen faɗakarwa, an sha zuwa har inda nake, an ci mun mutunci kawai, saboda faɗin gaskiya, amman ba na damuwa samsam idan na tuno da aya ta 84 a cikin dai Suratul Maryam:

Allah ya cewa Annabi S.A.W “Saboda haka kada ka yi gaggawa a kansu, muna yi musu ƙidayar ajali ne kawai, ƙidayawa {Fala ta’ajal alaihim innama na’uddu lahum addaa}”
Kowa da yanayin ƙarfin gidansu, wasu sun kasance masu kuɗi ne, wasu kuma talakawa wasu kuma akwai dai ɗan rufin asiri, rashin godiyar Allah ke saka wasu ƙawayen su ji suna sha’awar mallakar abin da ya fi ƙarfin aljihun iyayensu, ballanatana su da kansu, kin ga ƙawarki da babbar waya mai tsada, ki ce ke ma dole sai kin siya, shi kuma saurayi idan ya duba wannan, sai ya ce miki ya yi miki alƙawarin zai yi amfani da kuɗinsa ya biya miki buƙatarki, amman fa shi ma yana da sharaɗi wanda ba saina fada ba.
Ya ku iyayenmu mata, Ku ja musu kunne sosai, a kan su dinga kiyayewa, su yi taka tsantsan, su san da waɗanda za su dinga mu’amula musamman ma ƙawayensu na jami’a, nasan wasu ba za su ji daɗin karanta wannan saƙo nawa ba, saboda za su yi tunanin da su nake, masu kunnen ƙashi kenan, to amman idan ma mutum ya ji haushi to ya gyara, an ce dai gyara kayanka, ba ya zama sauke mu raba.
Wasu suna mantawa da rayuwar lahira, abin da ka shuka, shi za ka girba, ku tuba kafin ku mutu, kuna masu laifi, idan kuka tuba za ku zamo baƙin girma a Aljannah, saboda Allah (S.W.T) ya ce a cikin Suratul Maryam aya ta 85 “A ranar da muka tara masu taƙawa zuwa ga mai rahama suna baƙin girma {Yauma nahshuru almuttaqina ilalrahman wafda}”
Wasu matan suna jazawa wasu, ba duka ba ne aka taru aka zamo ɗaya ba, akwai nagari da yawa, tsiraru ne na banza. A matsayina na tsohon shugaban department ɗin Microbiology, Jami’ar Bayero wanda yake da masaniya a kan halayyar al’umma, na yi binciken mene ne silar gurɓacewar halin mata, ɗaya daga cikin sakamakon da na samu shi ne zuwa Club (Gidan Wasa) yana taka muhimmiyar rawa wajen kassara tarbiyyar mata
Mene ne fa’idar zuwa Club, wajen da zuwan sa ba zai amfana miki komai ba a duniya, ballantana a lahira. Allah ka sa mu fi ƙarfin zuciyarmu ka shiryar da zuri’armu ka sada mu da dukkan hanyoyin alkhairi, ka raba mu da na sharri, sannan ka haɗa mu da mutanen kirki a duk inda suke, ka nesanta mu da bara gurbi
A nan zan dasa aya, ba wai don abubuwan da zan faɗa sun ƙare ba, sai don kada na cinyewa masu karatu lokaci, a ƙarshe ina ƙara jan hankalin Iyayenmu mata da su yi hattara sosai a kan ‘ya’yansu, musamman a game da harkokin su na makarantar jami’a
Ku tura wannan muhimmin saƙon ga iyaye mata, Allah ne kaɗai ya san ladan da za ku samu idan kuka zamo silar shiriyar bayinsa.
labarin da ya wuceYadda Ake Buɗe Transfer A Layin MTN Cikin Sauƙi.
Labarin na GabaYadda Ake Ado Da Kwalliya Ta Musamman Ga Mata Da Maza