Mutum Da Son Zuciya.

0
638

    Zuciya ita ce matattarar buri da kwaɗayi da sha’awa a wajen mutum, kuma ita babu ruwanta da ba daidai ba, abin duk da ya ƙayatar da ita, za ta so shi, ko ya dace ko bai dace ba, kamar kare take, abin duk da ya so ya bi ,zai bi shi a guje don ya kama, ko ya yi gyara ko ya yi ɓarna, wata ran ya ciji ɓarawo, wata rana kuma ya ciji baƙon masu gida. Amma domin a amfana da gyaransa kuma, a tsira daga ɓarnarsa, shi ne uban gidansa yake tsawatar masa in ya ga zai ciji wanda bai kamata ba, ko ya saka masa sasari da sarƙa, don ya hana shi ɓarna, to haka zuciya ita ma sai da tsawatarwa.

Saboda haka, hankali shi ne linzamin zuciya, shi ne mai yi mata dabaibayi domin kada ta shige gona-da iri. Shi kuma imani shi ne alƙiblar hankali. Imani shi ne ya san lokacin da ya dace a saki ragamar zuciya, da kuma lokacin da ya dace a saka mata waigi.

Ashe, da za a ƙyale zuciya da abin da take so babu tsawatarwa, kuma babu kyakkyawan tunani, to da zuciya ta yi katoɓara marar misali, kuma ka bai wa mutum (marar lafiya) ruwan sikari da ruwan magani mai ɗaci, zuciyarsa sai ta fi son ruwan sukari, amma kyakkyawan tunani shi ne zai nuna masa cewa, magani duk da ɗacin da yake da shi, shi ne mafi amfani, ba ruwan sikari ba, komai zaƙinsa.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ɗan’Adam Kamar Yadda Allah Yake Son Sa. wanda M. Aminu Isma’l Sagagi ya wallafa Domin karanta Domin karanta cikakken littafin danna koren rubutunnan

 

 

labarin da ya wuceCututtukan Da Ba Su Da Magani
Labarin na GabaMa’anar Aure
Dr. Aminu Isma'il Sagagi
An haifi Dr. Sagagi a Unguwar Sagagi cikin birnin Kano a 1968 Ya yi PhD a IUA Khartoum 2012 Ya yi aikin koyarwa a Makarantar Munazzama Kura. Ya yi koyarwa a Makarantar koyon Sharia ta Malam Aminu Kano. Ya taba rike Mukamin Mai ba wa Gwamna Shawara a kan Ilimi 2009-2011 A yanzu Malami ne a Sashin Nazarin Addinin Musulinci a Jami'ar Bayero.