ƘARSHEN ALEWA

0
1181
Halin da muke ciki a yanzun ya kai matakin innalillahI wainna ilairaji”un! Idan ka cire maganar addini gaba dayan ta ka dawo da lamuran rayuwar nan a kan mizanin hankali, sai ka ga babu wani sauran nishaɗi ko kuma jin daɗi da ya rage maka, indai a wannan duniyar da muke ciki kake.
Duk kuwa da irin damammakin da muka samu na ci gaban da ya zo mana, wadda yake sauƙaƙa mana rayuwa, ba kamar zamanin iyayenmu da kakanninmu da suka gabata ba, duba da cewa, a wannan zamanin inda ka ɗauke amana, tausayi da jinƙan juna babu, abun da suke da shi na more rayuwa, ba su da lantarki, ba su da ruwan famfo, kai hatta gine-ginen gidajensu ma indai ba na mai sarauta ko mai hannu da shuni ba ne, ba wani ƙawata shi ake ba, amma haka bai hana musu rayuwa cikin aminci da yalwatacciyar lafiyar jiki da ta ruhi ba, lafiya mai ɗorewa.
 ‘Yan uwana, akwai wani daga cikinmu da ya taɓa tunanin abin da ya sa iyayenmu suka fi mu ƙarko? Dalilan suna da yawa, amma kaɗan daga cikinsu, mutumin shekara sittin zuwa saba”in baya, ko da shi kafiri ne, za ka same shi da ingantacciyar zuciya, kamala, da wadatar zuci, ba za ka taɓa samun sa da ƙarya ba, ba za ka taɓa samun sa da cin amana ba, sannan jikin matayensu kullum lulluɓe yake kirif! Balle kuma musulmi idan ka lura cutuka da daman gaske shekarun baya babu su, yanzun me ya kawo su? Yawa-yawan alfasha, mutum bai jin tsoro ko kunyar wadda ya halicce shi ba ma, balle kuma abokin halittarsa.
Idan ka juya wani janibin kuma, mazaje sun kasa sauke nauyi da Allah ya ɗora musu, ba domin ba su dashi ba, a’a, sai domin tunanin a hakan dukiyar za ta taru. Kai subhanallhi, wa”iyazubillahi Allah ta”alah da kanshi ya ce, “Ya zare hannayensa ga duk magidanci da bai sauke nauyin dake kansa ba”.
Ɗan uwa wane ne ya ba ka ne? Allah ne fa Koh? To ya bar ka da wayonka, ta ya kake ganin samun dacewa? Wani matakin lalacewa da matasa muke a kai yanzu, wai neman auren ma za ai, Amma sai an sanya haramci cikinsa, ba zai taɓa yiwuwa a yi shi cikin tsafta ba.

Da yawan matsaloli da yara suke ba wa iyayensu, ya samo asali ne daga tushen yadda suka mallaki yaran.

A wata fuskar kuma, yaran nasu ne, amma ba halalinsu ba, kun san dalilina? Tun kafin a auri uwar, aka samu cikin yaron, kuma a kan cikin aka ɗaura auren bayan an haife cikin Kuma, ba a daddara ba, aka ci gaba da zaman zinar da ake, ɗan uwa ka saɓa wa Allah da ya halicce ka, ta ya kake tunanin ‘ya’yan da ka haife su ba ta hanyar halali ba za su yi maka biyayya? A irin haka ne za ka ji yaro ya kashe ubansa, a’a wani ya yi zina da uwarsa, da dai sauran bala’o’i iri- iri da muke fuskanta a wannan ƙarnin.
Wannan dalili da wasu daga cikin mazaje suka ginu a kai, ya jawo babbar musibar da take addabar al’ummarmu a yau.
Mai gida cikin kashi ɗari na nauyin da Allah ya ɗora maka, ba ka sauke kashi saba’in ba, Kuma kana da tabbacin babu wani wadda zai yi maka dole, sai kai ɗin ba ka tunanin halin da uwa za ta shiga? A ƙoƙarinta na neman mafita, har ta faɗa halaka, kuma kai kaine sanadin faruwar komai, Eh, to hallaka mana a cikin nauyin da Allah ya ɗora muku, babu wadda idan babu shi za ai haƙuri, ba zai taɓa yiwuwa a rayu babu abinci ba, ko babu sutura, ko wajen kwanciya, ko kuwa magani, a ciki duk babu wadda za ai haƙuri da shi, dukkaninsu lamura ne na dole.
Kana tunanin idan ta samu mai ba ta abinci ba za ta karɓa ba ne? Yau da gobe yana ba ta sau ɗaya, idan ya bijiro da buƙatarsa ko da wace iri ce, za ta amsa hannu bibiyu ko don gudun rashin wadda zai ba ta. Wane ne silar hakan?
Idan kai matashi ne a wannan ƙasar, ban san abin da ya yi maka daɗin da za ka ɓata lahirarka ba, bayan kuma ba ka mori duniyar ba. Eh mana. Kaso saba”in na matasanmu ba su da aikin yi, ba su da wani mafarki a kan gobensu, kuma ba mu da wata madogara da muka jingina rayuwarmu a jiki. Matasa kunnenku nawa? Wallahi wankin hula yana gab da kai mu dare idan har mu ba mu gyara ba, a haka yaranmu za su tashi, su ma haka nasu yaran abu ya zo ya zame mana al’ada.
Eh al’ada mana, ina jin dai ita ce ake yin ta yau da gobe? Kuma babban abin takaicin a ce wai mun sunnata wa ‘ya’yayenmu abin da ba zai kai su tudun mun tsira ba.

Eh kwarai da gaske da ni da ku, ai mun san abin da muke aikatawa ba tone-tone. ɗan uwa ko iyaye mahaifanmu kawai suka yi ba su da ikon tsara mana yadda gobenmu za ta kasance.

Mu ne muke da damar zama abin da muke so, kodai mu zama lalatattu ko kuma nagartattu. Ba mu da lokaci isasshen da za mu ɓata shi wajen saɓon Allah ta”ala, saboda komai ya zo ƙarshe mu muka zo, eh mana, alamomin tashin duniya babu wadda bai bayyana ba ɓaro-ɓaro.
Mu yi amfani da lafiyarmu, da lokacinmu da ilminmu da dukkanin damar da muka samu domin samar da tsabtatacciyar al’umma, ta haka ne duniya ba za ta manta da sunayenmu ba, ko ƙasa ta yi mana hijabi da ita.
Ɗan uwa ba ka da lokacin ɓatawa, kay i gaggawar miqa lamuranka ga Mahaliccinka, yi kokari ku rabu lafiya da iyayenka, hanzarta ka sauke nauyin iyalanka, duk azabar da za ka ci wajen yin hakan, domin ta haka ne kaɗai za mu sadu da mahaliccinmu cikin salama!
Don Allah muso juna, mu yi wa juna uzuri, kuma mu yafi juna, mu gina ingantacciyar rayuwa ko ba don komai ba ma, domin amfanin kawukanmu.

Fatana Allah ta”ala ya jiɓanci dukkanin lamuranmu..

Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga iyaye mata domin karanta wannan wasika danna kuren rubutun nan

labarin da ya wuceYadda Ake Wa Mai Gida A Lokacin Al’ada
Labarin na GabaNa Sha Ruwa Bayan Tayar Da Iƙama A Kan Kuskure, Ya Hukuncin Azumina?