Hani Akan Yin Gori

1
42

Gori: shi ne yin isgili, shaguɓe, habaici akan wani mutum, wanda yake da kashi a gindinsa, ko kuma wanda yake da wata matsala kamar sata ko zina.

Saboda haka, addinin musulunci ya hana yi wa wani mutum gori akan wani abu, saboda haka ne ma Allah (Subhanahu wata’ala) ya hana yin gori akan wata kyauta da wani mutum ya yi wa wani mutum, idan kuma mutum ya yi wa wani kyauta, sai kuma wata rana kwatsam ya goranta masa, to kyautarsa ta ɓace, ma’ana ba shi da ladan kyautar da ya yi har abada.

Haka kuma, an hana yin gori ga wani mutum wanda yake aikata wani laifi a baya, ko dai ta hanyar daina  aikata laifin ko kuma ta hanyar tuba, misali idan wani mutum yana yin zina ko sata a baya, sai kuma yanzu ya gane kuskuren aikata haka, sai ya tuba. To addinin musulunci ya hana kowane musulmi ya yi masa gori akan irin abin da yake aikatawa a baya, idan wani abu  ya haɗa su na cacar  baki ko faɗa kamar “him! aikin banza ai daman can shi ɓarawo ne ko mazinaci” da dai sauran su.

Saboda haka, akwai wata mace kirista ta musulunta, to sai wani abu ya haɗa su da wata mace musulma, to kuma ita wannan ita ce ba ta da gaskiya (musulmar), sai ta kalli wancan macen, sai tace da ita “Um! ki rufewa mutane baki tubabbiya kawai, kin gama iskancinki yanzu kin zo za ki faɗawa mutane maganganun banza”. Sai ita waccan macen ta yi kamar ta fita daga musulunci, saboda irin waɗancan maganganun da ake faɗa mata, amma da yake addinin ya shiga cikin zuciyarta, sai ta kau da kai.

Har ila yau, idan wani mutum yana aikata saɓon Allah kamar su ƙarya, ha’inci, gori, shirka, algus, bokanci ko dabo, gulma, da dai sauran su, to idan wani mutum ya musulunta akan irin waɗancan abubuwan da yake aikatawa ko ya tuba daga aikata haka, to shari’ar musulunci ta hana kowane mutum ya faɗawa wani mutum baƙaƙen maganganu kamar su cewa ai maƙaryaci ne, mushriki ne, boka ne, magulmaci ne, maha’inci ne, mazinaci ne da dai sauran su.

Saboda haka, ya kamata  musulmin da yake aikata haka, ya yi gaggawar daina aikatawa, saboda samun damar tserata daga fushin Allah (Subhanahu wata’ala) da manzon Allah (Salldlahu alaihi wasallam).

Saboda dukkanin wanda yake yi wa wani mutum gori akan wani abu da ya ba shi ko kuma wani abu wanda wani mutum yake aikatawa mara kyau, sai kuma ya tuba ya daina aikatawa, to wanda yake yi musu gori akan haka, to zai iya shiga cikin fushin Allah (Subhanahu wata’ala) matuƙar bai daina aikata haka ba.

Saboda haka gori ba shi da wani amfani ga musulmi mai hankali da tunani, saboda addinin musulunci ya yi hani akan aikata haka. Sa’annan kuma ko a a hankalce da tunani, to gori ba shi da wani amfani, saboda a wani lokacin gori yana kamanceceniya da tonon silili, wanda shi ma aikata haka ba shi da amfani ga musulmi.

Haka kuma tonon silili da wasu mutane suke yi wa junan su, wannan kuskure ne, haka kuma ba shi da amfani ga addinin musulunci. Har ila yau, yunƙurin binciken laifin wani mutum wanda yake aikatawa ko kuma wanda ya daina aikatawa, to yin hakan kuskure ne, saboda idan wani mutum ya shagala da binciken laifin wani mutum, sai kuma ya manta da laifin kansa, to zai yi mutuwar biyu babu ko kuma kamun gafiyar ɓaidu.

Saboda haka, yana da matuƙar mahimmanci akan musulmi dukkanin abin da zai aikata, to ya yi ƙoƙarin sanin hukuncin aikata haka da fatan Allah ya sa mu dace, sannan kuma mu nisanci aikata haka, haka kuma yana da matuƙar amfani ga mahukunta su ɗauki wani mataki ko tsari ga masu aikata haka, don samun ci gaban addinin musulunci baki ɗaya.

Danna nan don karanta sauro halittar Allah mai ban Al’ajabi

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceFassarar Huɗuba Daga Masallaci Mai Alfarma 10 Rajab 1446 AH 10 January 2025
Labarin na GabaHani Akan Yin Gulma

SHARHI ƊAYA