Falalar Sallar Walaha

0
1029

a) An karɓo daga Buraidah (R.A) Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam)Ya ce: “A jikin ɗan Adam akwai gaɓoɓi ɗari uku da sittin (360) wajibi ya yi sadaka a kan kowace gaɓa” sai suka ce wane ne zai iya wannan ya Manzon Allah? (sallallahu alaihi wasallam) Sai ya ce: Binne majina a masallaci (Wato in ka ga wani ya yi kaki ya kwamɓala ta a masallaci ka binne ta) ko ka kawar da abu mai cutarwa daga hanya, in ba ka sami iko ba, raka’a biyu ta walaha ta wadatar”. (Abu Dawud 2/524).

b) An karɓo daga Abu zarr (R.A) ya ce: ” Sadaka tana hawa kan kowace gaɓa ta ɗayanku kowace safiya, kowane tasbihi daidai yake da sadaka, kowace hamdala (Alhmdulillahi) daidai take da sadaka, kowace hailala daidai take da sadaka, kowacce kabbara daidai take da sadaka, umarni da kyakkywan aiki daidai yake da sadaka, hani ga mummunan aiki daidai yake da sadaka, raka’a biyu ta walaha tana wadatarwa ga wannan.” (Muslim 720)
Wannan hadisi yana nuna mana cewar Sallar walaha raka’a biyu daidai take da sadaka ɗari uku da sittin (360).

Domin karanta cikakken bayani a kan Sallar Istahara danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceSallar Walaha
Labarin na GabaYadda Ake Sallar Istihara