Haƙƙin Da Suke Kan Mahaifiya.

0
561

Tabbas uwa tana da nata ayyukan masu yawa da muhimmanci waɗanda in ta kula da su za a samu ‘ya’ya nagari insha Allahu, daga cikinsu akwai:

1. Zaɓen miji na gari, ta zaɓa ko a zaɓa mata.
2. Kaucewa saɓon Allah Ta’ala a lokacin neman aure da lokacin biki, da kula da haƙƙoƙin da miji yake da su a kanta
3. A yayin da kika samu ciki, ki yawaita addu’ar Allah ya tsare ki da abin da yake cikinki daga sharrin shaiɗanu.
4. Ki kula da bin Allah Ta’ala da kaucewa saɓa masa.
5. Ki kula da cin abinci mai gina jiki da ƙara lafiya. musamman irin abincin da likitoci suke bai wa mai ciki shawara ta rinƙa ci ki rinƙa bin shawarwarin likitoci na kula da lafiya.
6. Ki yi ƙoƙarın iya yinki. wajen kaucewa ɓacin rai da janyo wa kai fitina. da tashin hankali tsakaninki da mijinki ko abokan zamanki.
7. Ki guji shan tsami  da ɗaci da magunguna barkatai, ba tare da umarnin likita ba.
8. Zubar da ciki haramun ne, ahir ɗinki!.
9. Ki kula da tsaftar jikinki da mahallinki da abincinki
10. Ki rinƙa daurewa kina motsawa kina yin aikace-aikacen gida kada ki lafke ki daina komai sai kwanciya.
11. Ki guji shan taba da sauran shaye-shayen kayan maye saboda illarsu da cutarsu har abin da yake cikinki yake shafa.
12. Da zarar kin ji ba daidai ba a jikinki,  maza ki tuntuɓi likita.
13. Ki guji yawan yin Scanning yana da illa. Sai da umarnin ƙwararren likita.
14. Kada ki mayar da ciki da haihuwa wata hanyar gallazawa miji da cusguna masa da ɗora masa lalurori da tsarabe-tsarabe na ba gaira ba dalili, ta yadda samun ciki zai zamo wani abin ɓacin rai da damuwa ga mijinki.
15. Ki tabbatar kuna bin shawarwarin likitoci wajen shayar da jariri, ki ƙara kula da cin abinci mai gina jiki a lokacin da kike shayarwa.
16. Ki kula da lafiyar jaririnki, ki yi ta yi masa addu’a.
17. Ki kula da ƙa’idojin tarbiyya tun daga goyon ciki har zuwa girma da balagar ‘ya’yanki.
18. Tarbiyya aiki ne na uwa da uba, duk wani wanda zai shigo taimaka musu kawai zai yi. Saboda haka a ɗaura ɗamara, mu dage mu nemi taimakon Allah kar mu yi sakaci. A kula a yi hattara.

Domin karanta cikakken bayani a kan Haƙƙoƙin Ƙananan Yara A Musulunci danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Tarbiyar ‘Ya’Ya Daga Neman Aure Zuwa Girmansu wanda Shehu Usman Abubakar (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceAikin Uba
Labarin na GabaHaƙƙoƙin Ƙananan Yara A Musulunci