Tag: Aikin

  • Haƙƙin Da Suke Kan Mahaifiya.

    Haƙƙin Da Suke Kan Mahaifiya.

    Tabbas uwa tana da nata ayyukan masu yawa da muhimmanci waɗanda in ta kula da su za a samu ‘ya’ya nagari insha Allahu, daga cikinsu akwai:

    1. Zaɓen miji na gari, ta zaɓa ko a zaɓa mata.
    2. Kaucewa saɓon Allah Ta’ala a lokacin neman aure da lokacin biki, da kula da haƙƙoƙin da miji yake da su a kanta
    3. A yayin da kika samu ciki, ki yawaita addu’ar Allah ya tsare ki da abin da yake cikinki daga sharrin shaiɗanu.
    4. Ki kula da bin Allah Ta’ala da kaucewa saɓa masa.
    5. Ki kula da cin abinci mai gina jiki da ƙara lafiya. musamman irin abincin da likitoci suke bai wa mai ciki shawara ta rinƙa ci ki rinƙa bin shawarwarin likitoci na kula da lafiya.
    6. Ki yi ƙoƙarın iya yinki. wajen kaucewa ɓacin rai da janyo wa kai fitina. da tashin hankali tsakaninki da mijinki ko abokan zamanki.
    7. Ki guji shan tsami  da ɗaci da magunguna barkatai, ba tare da umarnin likita ba.
    8. Zubar da ciki haramun ne, ahir ɗinki!.
    9. Ki kula da tsaftar jikinki da mahallinki da abincinki
    10. Ki rinƙa daurewa kina motsawa kina yin aikace-aikacen gida kada ki lafke ki daina komai sai kwanciya.
    11. Ki guji shan taba da sauran shaye-shayen kayan maye saboda illarsu da cutarsu har abin da yake cikinki yake shafa.
    12. Da zarar kin ji ba daidai ba a jikinki,  maza ki tuntuɓi likita.
    13. Ki guji yawan yin Scanning yana da illa. Sai da umarnin ƙwararren likita.
    14. Kada ki mayar da ciki da haihuwa wata hanyar gallazawa miji da cusguna masa da ɗora masa lalurori da tsarabe-tsarabe na ba gaira ba dalili, ta yadda samun ciki zai zamo wani abin ɓacin rai da damuwa ga mijinki.
    15. Ki tabbatar kuna bin shawarwarin likitoci wajen shayar da jariri, ki ƙara kula da cin abinci mai gina jiki a lokacin da kike shayarwa.
    16. Ki kula da lafiyar jaririnki, ki yi ta yi masa addu’a.
    17. Ki kula da ƙa’idojin tarbiyya tun daga goyon ciki har zuwa girma da balagar ‘ya’yanki.
    18. Tarbiyya aiki ne na uwa da uba, duk wani wanda zai shigo taimaka musu kawai zai yi. Saboda haka a ɗaura ɗamara, mu dage mu nemi taimakon Allah kar mu yi sakaci. A kula a yi hattara.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Haƙƙoƙin Ƙananan Yara A Musulunci danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Tarbiyar ‘Ya’Ya Daga Neman Aure Zuwa Girmansu wanda Shehu Usman Abubakar (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Aikin Uba

    Aikin Uba

    Babban nauyi a wajen tarbiyya yana kan uba, kuma duk Kulawar uwa in uba bai yi nasa aikin ba to sai an samu matsala a tarbiyyar ‘ya’ya.

    A dunƙule ga wasu daga Cikin nauye-nauye da suke kan uba:

    1. Zaɓen mace managarciya mai addini.
    2. Kaucewa saɓon Allah a lokacin neman auren,
    3. Kaucewa saɓon Allah a lokacin biki.
    4. Kula da haƙƙoƙin da matarsa take da su a kansa.
    5. Kula da ladaban ma’amalar aure a ranar farko,
    6. Cikakkiyar kulawa da matar a lokacin da take da ciki. kula da lafiyarta da tausaya mata da taimaka mata da kwantar mata da hankali. Haka a lokacin da take naƙuda, da lokacin da ta haihu.
    7. Nuna farin ciki da godiya ga Allah kan duk abinda ta Haifa mace ko namiji
    8. Cikakkiyar kulawa da lafiyarta da faranta mata da taimakonta da ciyar da ita a lokacin da take shayarwa.
    9. Yin hidinmomin jariri waɗanda suka haɗa da sa masa suna mai kyau. yi masa aski, yi masa kaciya, yanka masa ragon suna, da al’adu masu kyau na nuna farin ciki waɗanda ba su ci karo da shari’a ba.
    10. Daga nan kuma sai a duƙufa wajen tarbiyyar jiki. hankali, tunani, ilimi, zamantakewa, ƙwaƙwalwa, siyasa da sauransu tun daga wannan lokaci har zuwa balagar ɗa namiji da aurar da ‘ya mace kamar yadda Za’a a yi bayani a nan gaba da kuma sauran maƙaloli da za su zo in sha Allahu.

    Domin karanta cikakken bayani akan Aikin Uwa danna nan.

    Wannan bayani anciro shine daga littafin Tarbiyyar ‘Ya’Ya Daga Neman Aure Zuwa Girmansu wanda Shehu Usman Abubakar ( Shehu Mansur Dala ) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.