Za mu ɗauki kaɗan daga cikin jinnu mu bayyana alamominsa da kuma magungunansa.
Jinnul Gawas
Waɗannan jinnu sun yi zamani da Annabi Suleiman (Alaihis Salam). Kamar yadda Allah (Subahanahu Wata’ala) ya faɗa a cikin Al Ƙur’ani mai girma a cikin suratus Saad, aya ta 37:
“Wash shayaɗina kulla banna’in wa gawwas”
Akasarin wannan aljanun suna daɗewa a duniya kuma akasarinsu musulmai ne amma duk da yake akwai kafirai a cikinsu kaɗan. Kuma akasarinsu sun fi rayuwa a cikin ruwa ko cikin tafki ko kuma rijiya. Kuma sukan yawan shiga jikin yara.
Alamominsu Jinnul Gawas :
Mutum zai ji yana yawan zama a cikin bayi shi kaɗai, ko ka ga yana yawan wasa da ruwa ko kuma ya yi alwala sau da yawa ya ɗauka duk alwalar ba ta yi ba. Ko da tsananin sanyi ake yi shi zai iya yin wasa da ruwa ba tare da ya samu wata matsalar ba. Zai so ya rinƙa jiƙa jikinsa kuma za ka ga yana yawan wasa da dabbobi, ko kuma ya rinƙa yawan ganinsu a cikin mafarkinsa sannan a cikin barci zai dinga firgita ko ya rinƙa yawaita mafarkin kifi. Sannan wani lokacin idan ya yi tsanani, yakan kai da mutum yarinƙa faɗuwa.
Hanyar Da Ake Bi A Magance Su
Akan samu ruwa mai kyau tsaftatacce ko ruwan sama ko na rijiya sai a karanta surorin nan kamar haka, kowacce ƙafa ɗaya sai a tofa a cikin ruwan. Ga surorin kamar haka;
- Suratul baƙarah
- Suratul Yunus
- Suratu dukhan
- Ayatul azab wal ƙahar
- Ayatul garaƙ wal bahar
Waɗannan su za a tofa a cikin ruwa a ba shi ya sha da safe da yamma. Sannan akan so a ɗebi ruwan da aka yi wannan addu’ar ana dafa masa kifi da shi har sai ya samu lafiya. Sannan a karanta waɗannan ayoyin a cikin muski yana shafawa a ƙirjinsa da kansa. In Sha Allah zai samu lafiya.
Jinnul Ashiƙ
Wannan jinnu ya fi takurawa mutane, musamman mata, ko matan aure, ko bazawara, ‘yan mata ya hanasu aure, matan aure ya raba musu aure kuma bazawara ya daƙile duk abinda zai sa su yi aure.
Shi jinnu ne da yake auran mace ya zame mata tamkar mijinta, in kuma tana da miji ya haramta mata duk wani jin daɗin aure ta zama kurum gata nan kamar hoto a gidan mijin.
Duk da ana samun jinnul ashiƙa ta auri mutum, namiji ko da yana da aure ta cire masa son matarsa; zai iya shafe shekara da shekaru suna kwanciya ɗaki ɗaya, gado ɗaya amma ba tare da ya yi sha’awarta ba. Amma da ya kwanta sai wannan aljanar ta rinƙa zuwar mishi a cikin bacci yana mu’amalantarta ta zama tamkar matarsa.
In kuwa aka yi rashin sa’a ta auri wanda bai taɓa yin aure ba; to in ba an yi da gaske ba takan zama matarsa ce har lokacin da zai bar duniya. Ta cire masa duk ƙaunar aure ko kuma ƙaunar wata mace ya gwammace ya yi ta zama a haka har ya bar duniya; ba ya so wani ya yi masa maganan aure shi kuma ba zai yi ba.
Alamomin Jinnul Ashiƙ
Mace ta rinƙa yawan samun faɗuwar gaba, yawan fushi ba gaira babu dalili; mace ta ji ta tsani kowa ko mijinta ba ta son gani, ta rinƙa keɓe kanta daga cikin mutane ta ji ta fi so ta rinƙa zama ita kaɗai.
Ta rinƙa jin wasi-wasi a cikin zuciyarta ana raɗa mata mutuwa za ta yi; mace ta rinƙa ji kamar ta bar gidan da take zaune ko ta ƙwalla ihu, wata ma haka kawai za ka ga tana hawaye ko tana kuka ba tare da an mata laifi ba, ga yawan mafarkai daban-daban. Kamar mafarkin saduwa ko mafarkin taron biki ko mafarkin kin ɗau ciki; ko kuma ki yi mafarkin kin haihu ko ki yi mafarkin ga ki kina shayarwa.
Wata ma za ta ga mijin nata a mafarkin babanta ne wata kuma ta ga yayanta ko wani mutumin da take jin kunyarsa; sai ta gan shi yana saduwa da ita. Wata kuma sai ta ga ga mata ‘yan uwanta suna saduwa da junansu tana kallo tana jin daɗi; ko ta ga maza suna saduwa da junansu tana kallo tana jin daɗi.
Za ta ji daɗi a mafarkin in ana saduwa da ita amma in mijinta ya zo kusa da ita, sai ta ji kamar an sa mata wuta ta ji kamar an aiko mata mala’ikan mutuwa; duk yadda mijinki zai faranta miki ba ya burgeki, za ki ji ba kya son sa kwata-kwata, ba kya san ganinsa ko kaɗan. Abin lura a nan shi ne duk mafarkin da kika yi a gurin gaskiya ne.
Domin karanta cikakken bayani akan
Matakan Da Za A Bi Domin Rabuwa Da Jinnu danna koren rubutu.
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu