Mahangar Siyasa A Musulunce

0
1333

Mahangar Musulunci a kan tsarin daula da siyasa a zamanance

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban Manzanni, da ‘yan gidanSa da sahabbanSa gaba ɗaya,

(قَالُوا سُبْحَانَكَ لَا عِلْمَ لَنَا إِلَّا مَا عَلَّمْتَنَا إِنَّكَ أَنْتَ الْعَلِيمُ الْحَكِيمُ)

(tsarki ya tabbata gare ka, babu wani ilmi a gare mu face abin da ka sanar da mu. Lallai kai ne Masani Mai hikima) (Al-bakara: 32).

Bayan haka:

Alkur’ani mai tsarki dai wani littafi ne na shiriya da shiryarwa, don haka ya zama dole ga Musulmi ya nemi hasken shiriyarsa daga cikinsa; saboda littafi ne mai tsarki, babu wani ruɗani dake zuwa masa ta gabansa balle bayansa, saukarwa ne daga Mai hikima kuma wanda ake godewa.

HaƙiKa Allah Mai girma da ɗaukaka ya tara mana ilimomin farko da na ƙarshe a cikin Alkur’ani, ya kuma cika shi da sirruka da hikimomi. Don shi ne littafin da Ubangiji Allah ke ba mu bayani a kan tarihin ɗan Adam, tun daga halittar Annabi Adam (AS) har zuwa ranar da ɗan Aljannah zai shiga Aljannah, ɗan wuta ya shiga wuta, Allah ya tsare mu.

Shi ne littafin dake bayyana mana al’amuran addininmu, da siyasarmu ta Musulunci, da duniyarmu, da ibadarmu, da mu’amalolinmu, da sha’anin auratayyarmu, da alaƙoƙinmu na Dauloli, kamar yadda Allah Madaukaki ya ce:

“Kuma mun saukar maka da Alkur’ani mai bayyana dukkan komi”.

(Suratun Nahl: 89),

kuma Allah ya ce:

“Lallai wannan Alkur’anin yana shiryarwa zuwa ga abin da yake mafi tabbatuwa”.(Al-Isra’i: 9).

Ya kamata ga dukkan musulmi ya sanya Al’ƙur’ani ya zam mahangar rayuwarsa ta kowane fanni, da yawan binciken taskokin haskensa, musamman a wannan zamanin da falsafofi suka yi yawa a cikinsa, nau’ikan ilimomi suka yawaita, wanda mafi yawansu, ba a gina su don tsoron Allah ko neman yardarsa ba,

Kuma mafi yawan mutane na cikin jahilci da ɓata, musamman ga mas’alolin da suka shafi hukunce-hukuncen Musulunci ga shar’antattar siyasa, to Allah Ta’ala ya nufe ni da in ɗauki wasu daga cikin waɗannan mas’aloli in yi bayanin su, musamman waɗanda aka fi yin kuskure a cikinsu, kuma aka yawaita tambayoyi a kansu, saboda dalilai masu zuwa:

1- Al’adar musulman wannan zamanin ta cuɗanya rudani mai yawa cikin mas’alar hukunci da siyasa, ba ina nufin gama-garin su ba kaɗai, kai harma da manyan malamai, har ma wasunsu na keɓance siyasa ga sha’anin duniya kawai, ban da ɓangaren addini, har aka wayi gari, masu gudun siyasa su ne masu addini da zuhudu.

2- Wasu daga cikin shuwagabanni  daga cikin waɗanda ba su fatan yardar Allah, suna aiki tuƙuru don tabbatar da mummunar fahimta ga ƙwaƙwalen musulmai a kan abin da ya shafi siyasa da hukunci, har wasun su na yawan faɗin cewa; ba ruwan Addini da siyasa, kuma ba ruwan siyasa da Addini.

3- Da yawan mutane sun nisanci addini da koyarwar Manzon Allah (SAW), ga abin da ya shafi harkokin siyasa da hukunci, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya ce:

“Lallai ne za a riƙa kwance maɗauren Musulunci ɗaya bayan ɗaya, na farkon kwancewa kuwa shi ne hukunci, na ƙarshe kuwa ita ce sallah“.

(Imam Ahmad ya ruwaito shi daga Abi Umama: 5/251)

4- Mafi yawan wasu shugabannin musulmai na wannan zamanin, suna iƙirarin cewa Daular su ta Musulunci ce, kuma wai su suna shari’ar Musulunci, addininsu shi ne Musulunci kuma shiriyarsu shi ne Alkur’ani, kai har ma suna ganin masu yi musu nasiha da wa’azi sun fita daga addini kuma ba su kan tafarkin muminai.

Manufata a wannan ɗan ƙaramin bincike ita ce; share waccen ƙurar da ta lulluɓe shugabanci da siyasa cikin bayanai masu zuwa:

Na ɗaya: Musulunci ya yarda da tsaftatacciyar siyasa, kai asali ma siyasa na daga addini, wanda kuma ke aƙidanta saɓanin wannan, to akwai alamar tambaya ga addininsa, saboda wannan shi ne abin da Alkur’ani ya zo da shi ya ce,

“Ka ce lallai sallahta da yankana da rayuwata da mutuwata na ga Allah Ubangijin talikai. Ba shi da wani abokin tarayya) (Al-am:162-163)

Na biyu: Alkur’ani ya bayar da muhimmanci da kulawa a kan mas’alar tsarin hukunci, Musulunci kuwa ya yi bayani a kan haka filla-filla,

kuma malamai sun rubuta littattafai kundi-kundi a kan haka, don haka ashe siyasa ba wata sabuwar mas’ala ba ce ko bidi’a wurinmu ‘yan uwa musulmi.

Na uku: Komawar musulmai zuwa ga shari’ar Musulunci, da shiryarwar Alkur’ani ta ɓangaren hukunci, ba wai kawai abin rayawa ga zukata ba ne, sai dai abin tsammanin aukuwarsa ne da izinin Allah, kamar yadda manzon tsira (SAW) ya ba mu labari:

“Khalifanci bayana shekaru talatin ne, sannan ya zamo mulkin kama karya, sannan khalifanci a bisa hanyar Annabta}

(Imam Ahmad ya ruwaito shi cikin silsilatis sahihah: 4/273)

Na hudu: Daular Musulunci na ɗauke da kyawawan halaye irin na Alkur’ani, da kuma ma’aunai waɗanda za a iya auna nisanta da kusancinta ga Musuluncin, sha’aninta ba wai kawai iƙirari ba ne da hargowa. Sai dai akwai haƙƙoƙin dake ga mai hukunci, kamar yadda shi kuma akwai wajibansa ga mabiyansa.

Bayan haka, daga nan za ni fara bayanan abin da nai nufi kamar yadda ya sauwaka gare ni, ina fata Allah Ta’ala ya gudanar da gaskiya a bisa harshena da alƙalamina, ya yi min muwafaƙa da ƙyaƙƙyawan bayani, kuma ya zamo hujja ce gare ni ba a kaina ba, godiya ta tabbata ga Allah a farko da ƙarshe.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Hattara Dai ‘Yan Siyasar Musulmai wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin Danna nan.

labarin da ya wuceYadda Za Ki Yi Mu’amala Da Uwar Mijinki
Labarin na GabaMatakan Bunƙasa Ƙudurar Ɗan’adam