Koyi Da Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam)

0
529

Wajibcin koyin da Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam):

Ita masa’alar koyi abu ne wanda yake haɗe da halittar ɗan Adam. A farkon rayuwar ɗan Adam yakan fara koyi da duk abin da ya ga ana yi, ko daga wajen wa ya ga abin. Yayin da ya bude ido ya gane iyayensa, to sai kuma ya koma koyi da su. To shi kansa wannan matakin akwai matsalarsa, idan ya zama su iyayen ba a kan shiriya suke ba. Shi ya sa Alƙur’ani ya yi ta fama da masu maƙalƙale wa iyayensu wajen koyi da su a mummunar hanya. Misali, inda Allah (Subahanahu wata ala) yake cewa:

“Idan aka ce da su: “Ku bi abin da Allah ya saukar. Sai su ce “A’a, mu kawai za mu bi abin da muka saba iyayenmu suke kai ne. (Allah Subahana wata ala ya ce: “Yanzu za su riƙa bin iyayen nasu) Ko da iyayen nasu ba su da hankalin fahimtar abubuwa, kuma ba sa kan shiriya?” (Suratul Baƙarah, aya ta:170).
Wani lokaci kuma mutum yakan ga wani wanda ya burge shi a wata ƙwarewa ta rayuwa, misali: ƙwararren mai tunani wanda ya ƙirƙiri wata hanya ta rayuwa. (kamar kwamanisanci, ko jari hujja. Ko wanda ya ƙirƙiro wani tsari na shugabanci. (kamar damakwaraɗiyya) ko ƙwararren ɗan siyasa wanda ya yi shuhura. Ko ma ƙwararren ɗan wasa ko ƙwararren jarimi a wani fim ko wasannin kwaikwayo. Idan ba a yi sa’a ba, sai mutum ya kama ɗaya daga cikin waɗannan ya zama abin koyinsa a rayuwa. Ka ga an shiga cikin ɓata marar iyaka.
Wannan ya sa Allah (Subahanahu wata ala) ya yi ta aiko da manzanni domin a yi koyi da su, Allah (Subahanahu wata ala) yana cewa:
“Waɗannan su ne waɗanda Allah ya shiryar. Ka yi koyi da shiriyarsu” (Suratul An’am aya ta:90).
To kasancewar Annabinmu (Sallallahu alaihi wa sallam), shi ne na ƙarshe a cikin manzannin Allah, sai ya zama shi Allah ya sanya mana ya zama abin koyinmu. Allah (Subahanahu wata ala) yana cewa:
“Haƙiƙa kyakkyawan koyi ya tabbata a gare ku, daga Manzon Allah, ga wanda yake ƙaunar Allah da (kyakkyawar makoma daga) Allah da ranar lahira, kuma, ya ambaci Allah da yawa” (Suratul ahzabi, aya ta:21).
Wannan ya nuna wajibcin sanya shi abin koyi a dukkanin hanyoyin rayuwa.
Koyi da Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) a dukkanin tsare-tsaren rayuwa:
Duk wanda ya ce shi musulmi ne, to lallai ne abin koyin sa ya zamo Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam), a dukkanin tsare-tsare na rayuwarsa. Misali: Tsarin Ilmi, tsarin zamantakewa, tsarin Tattalin arziƙi, tsarin siyasa (shugabanci) da tsarin shari’ah. Abin nufi a nan shi ne, duk waɗannan tsare-tsare na rayuwa su zamo a kan tsarin Alƙur’ani da sunnah, bisa fahimtar magabata na ƙwarai. Kada mutum ya zama sai a sallah, Azumi, aikin Haji kaɗai, yake musulmi. Watau ya zama yana bin tsarin da ya saɓawa na Allah. Allah (Subahanahu wata ala) Yana cewa:
“Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku shiga Musulunci gaba ɗaya (watau ku miƙa wuya gaba ɗaya). Kada ku bi takun sheɗan, ba na Allah ba). Shi abokin gaba ne a gare ku, bayyananne” (suratul BAƙarah, Aya ta: 208).
Abin taƙaici shi ne, a halin da muke ciki a yanzu, za mu ga cewa a dukkanin tsare-tsare nan na rayuwa babu wanda muke tafiyar da shi a kan tsarin da Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) ya zo da shi. Misali: Tsarin Ilminmu ba ya koya mana tauhidi da tsoron Allah da ranar lahira da tarbiyyar Musulunci. A tsarin zamantakewa. Idan muka ɗauki zamantakewarmu ta aure da zaman iyali, ba a kan Alƙur’ani da sunnah take ba. Tsarin tattalin arzikinmu cike yake da cin hanci da rashawa, cin riba, gululi’ (Watau satar dukiyar jama’a) da sauransu. Tsarin siyasarmu (shugabanci) tsari ne na Damakwaraɗiiyya, wanda babu Allah a cikinsa. Shi kuwa tsarinmu na shari’ah kowa ya san dokokin ‘yan Adam muke fifitawa a kan dokokin Allah (Subahanahu wata ala). Abin nufi a nan shi ne, son Annabinmu na baka ne kawai. Ba a aikace yake ba. Ga shi kuwa Allah (Subahanahu wata ala) yana cewa:
“Gaya musu, idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, sai Allah ya so ku, ya gafarta muku zunubanku. Allah mai gafara ne, mai rahama” (Suratu Ali Imrana, Aya ta:31)
Allah (Subahanahu wata ala) yana cewa :“Ka ce musu Idan iyayenku da ‘ya’yanku da ‘yan’uwanku, da matanku, da danginku da dukiyoyinku da kuka nema da hanyar samunku da kuke gudun kada ya yi tasgaro da gidajen da kuke jin daɗinsu, su suka fi soyuwa a gare ku, maimakon Allah da Manzonsa, da ƙoƙarin tabbatar da tsarinsa, to ku zauna, har sai Allah ya zo da lamarinsa (Mutuwa ko halakarwa). Allah ba ya shiryar da mutane fasiƙai” (suratul Taubah, Aya ta:24).

Wannan duka yana nuna cewa ba za mu zama musulmi ba, sai mun gudanar da kowane ɓangare na rayuwarmu bisa tsarin Allah. Wannan kuma ba zai samu ba sai ta hanyar koyi da Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam), watau ta hanyar ruƙo da alƙur’ani da Sunnah. Annabi(S.A.W) ya ce:
“Na bar muku nauyaya guda biyu, ba za ku ɓata ba, matuƙar kun yi ruƙo da su: Littafin Allah da sunnata”
Yadda Sahabbai Suka Yi koyi Da Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam):
Sahabban Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassal) sun yi koyi da shi a cikin dukkanin harkokin rayuwarsu. Ba kawai sai a salla, Zakka, Azumi da Hajji kaɗai ba. Ga wasu misalai ‘yan kaɗan da za su nuna mana haka.
Dab da Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) zai yi wafati ya zartar da wata rundina ta yaƙi, ƙarƙashin shugabancin Usamatu bin Zaid. Bayan wafatin Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) sai wasu suke ganin ya kamata a dakatar da wannan runduna tukuna, kasancewar an sami wasu suna ƙin bayar da zakka. Har ma aka zama cikin tsoron kawo hari cikin Madina. Me Abubakar ya yi a matsayinsa na shugaba? Abubakar bai yarda a dakatar da wannan runduna ba. Cewa ya yi:
“Ba za ta yiwu ba a gare ni na kwance tutar da Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) ya ƙulla”.

Haka nan sauran sahabbai suka goyi bayan Abubakar, Usamatu ya shugabanci wannan yaƙi kuma aka yi gagarumar nasara. Game da Madina kuwa, abin da Abubakar ya yi shi ne, sai ya sanya wasu daga cikin manyan sahabbai suka shugabanci wata runduna domin ba ta kariya, kamar su: Aliyu bin Abi Ɗalib, Zubairu bin Auwam, Sa’adu bin Abi Waƙƙas, Abdullahi bin Mas’ud da Abdur Rahman bin Aufin12.
Wani abin da Sayyidina Abubakar ya yi (na ruƙo da tsarin Annabi) bayan wafatinsa (Sallallahu alaihi wassallam), wanda yake nuna dagewarsa, shi da sauran sahaban
Sunnar Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) (watau tsarin sa na rayuwa) shi ne, wasu Larabawan ƙauye sun ƙi bayar da zakka bayan wafatin Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam). A wannan lokacin cewa ya yi:
“Wallahi! Idan da za su hana ni dabaibayi, wanda suka kawo wa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam), da sai na yaƙe su”.
Wani abin da za mu sake lura da shi shi ne, yanayin da Nana faɗimah ‘yar Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) ta nemi gadon Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam), a nan ma sai ya ce mata ya ji Manzon Allah ya ce:
“Mu jama’ar Annabawa ba a gadon mu. Abin da muka bari, sadaka ne” (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito).
Wani misali shi ne, wata rana sayyidina Umar ya zo zai sumbaci Hajarul Aswadi sai ya tsaya ya ce:
“Ni na san kai dutse ne. Ba ka cutarwa, ba ka amfanarwa. In ba domin na ga Annabi (Subahanahu wata ala) ya sumbace ka ba, da ba zan sumbace ka ba”. (Bukhari ne ya ruwaito).
Wata rana Abdullahi bin Mas’ud ya zo zai shiga masallaci, sai ya ji Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) yana cewa: “A zauna”. Sai ya zauna a kan dokin ƙofar masallaci. Bai ƙara yin gaba ba ko kaɗan, sabo da cika umarni.
Haka nan sahabbai suka yi ta koyi da Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam), a dukanin tsare-tsaren rayuwa. Wata rana Abdullahi bin Mugaffal ya ga wani mutum (ko wani ɗan ɗan uwansa), yana yin jifan da ake kira ‘Hazfu (wadda akan sa tsakuwa a tsakanin babban danyatsa da ɗab ali, awulla ta). Sai ya ce da shi: “Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) ya hana yin hazfu. Da ya sake ganinsa yana yi sai ya ce: “Ina gaya maka Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) ya hana yin hazfu kana sake yi. Ba zan sake yin magana da kai ba, har abada” (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito).
Har ma ta kai cewa wasu daga cikin sahabbai suna koyi da Annabi, hatta a abubuwan da Annabi yakan yi ba da nufin lallai sai an yi koyi da shi ba.
Abdullahi bin Umar ya shahara game da haka.
Abdullahi bin Umar ya kasance yana zuwa ƙarƙashin wata bishiya a Madina, ya yi baccin rana. Da aka tambaye shi game da haka, sai ya ce shi kawai ya ga Annabi yana yin baccin rana a ƙarƙashinta.
Wata rana Abdullahi bin Umar yana cikin tafiya tare da mutane, sai aka ga ya kewaye wani wuri, bai bi ta wurin ba, (Alhali babu komai a wurin), da aka tambaye, shi sai ya ce ya ga Annabi wata rana suna tafiya ya kewaye wurin.
Haka nan wata rana an ga ya sauka a wani wuri tsakanin Makka da Madina, ya yi salla a daidai wannan wurin suna halin tafiya. Duk da kasancewar a lokacin mutane sun yi masallaci a kusa da wurin shi sai ya ƙi yin salla a masallacin, ya je ya yi a daidai inda Annabi ya yi (Sallallahu alaihi wassallam).

Domin karanta cikakken bayani akan Muhimmacin Sanin Kamannin Annabi: danna koren rubutu.

Wannan bayani an ciro shi ne daga litttafin Mu San Kamannin Annabi (Sallallahu alaihi wassallam) Ɗabi’unsa Da Halayensa Domin Koyi Da shi wanda Dr Yahaya Tanko ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceHarsashin Gina Al’umma (Iyaye)
Labarin na GabaƊabi’ar Lokaci, Saurin Wucewa
Dr. Yahaya Tanko
A yanzu Dr. Yahaya Tanko Yana Bayar da darasai na littafai huɗu a mako, a masallacin Umar bin Khaɗɗab da da littafan Sahihul Bukhari da Fathul Majid a masallatan Nana A’isha da na Khalid binil Walid a unguwar Dukawuya FCE. A yanzu Allah ya azurta Yahaya Tanko da zuryya mai yawa, ‘ya’ya da jikoki. Ya yi ritaya a watan Febreru na shekara 2015 daga Jami’ar Bayero ta kano. Amma ya kama aikin kwantiragi da jami’ar Yusuf Maitama sule ta Kano.