Kalmomi Guda Biyar Masu Amfani A Duniya Da Lahira

0
626

Wannan addu’ar; ana so a dunga karanta ta a duk lokacin da mutum ya tashi daga barci, da kuma lokacin da zai kwanta barci. Insha Allah, Allah zai tsare shi Duniya da Lahira.

Idan ka karanta, Allah (Subahanahu Wata’ala) ba zai ba da dama wani ɗan Adam ya yi nasara a kanka ba; zai tsare ka daga sharrin dukkan maƙiya da mahassada; Duniya Da Lahira. Sannan Allah (Subahanahu Wata’ala) zai sa ka yi kyakkyawan ƙarshe a rayuwarka.

Ga Addu’ar Kamar Haka;

Na Duniya

1. Hasbiyallahu lidini
2. Hasbiyallahu liman ahammani
3. Hasbiyallahu liman baga alayya
4. Hasbiyallahu liman hasadani
5. Hasbiyallahu liman kadaniy bisu’in.

Na Lahira

1. Hasbiyallahu indal mawt
2. Hasbiyallahu indal mas’alatu fil ƙabar
3. Hasbiyallahu indal mizan
4. Hasbiyallahu indas siraɗi
5. Hasbiyallahu la’ilaha illallahu alaihi tawakkaltu wa’ilahi unib.

Wannan addu’ar an samo tane daga cikin littafin MAƘALIDUS SAMAWATI WAL ARDI MA’A HUSNUL MU’MIN.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’a Idan Mutum Yana So Allah Ya Biya Masa Buƙata Cikin Gaggawa danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Addu’a Idan Mutum Yana So Allah Ya Biya Masa Buƙata Cikin Gaggawa
Labarin na GabaYadda Ake Addu’ar Samun Nutsuwa Da Kwanciyar Hankali Da Wadatar Zuciya