Yadda Ake Addu’ar Samun Nutsuwa Da Kwanciyar Hankali Da Wadatar Zuciya

0
1104

Addu’ar Samun Nutsuwa Da Kwanciyar Hankali – An ruwaito daga Shaddad Ibn Aws, Annabi (Sallallaahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Ya Shaddad, idan ka ga mutane suna tara azurfa, zinare ko kuma yaƙutu, to suna tarawa ne don kada su yi talauci “.

Sai ya ce; “Kai Shaddad, ka da ka tara komai, ka riƙe wannan addu’ar kawai, Allah (Subahanahu Wataa’ala) zai tsare mutuncinka ya rufa maka asiri, ka fi ƙarfin abin da za ka ci, kuma ka zauna lafiya, ni ma a duk lokacin da na yi sallah ina karanta wannan addu’ar;

“Allahumma inni as’alukath Sabbath fil amr, wal azimatu alar rushdi, wa as’aluka shukra ni’matika wa husna ibdatika, wa as’aluka ƙalban saliman wa lisaanan sadiƙan, wa as’aluka min khairi ma ta’alam, wa a’uzubika min sharri ma ta’lam, wa astgfruka lima ta’lam innaka anta allumul gayub”.

Wannan Addu’ar Samun Nutsuwa Da Kwanciyar Hankali; an samo ta ne daga WABILUS SAYYIBU MIN KALAMUD DAYYIB.

Domin karanta cikakken bayani a kan Kalmomi Guda Biyar Masu Amfani A Duniya Da Lahira danna nan

labarin da ya wuceKalmomi Guda Biyar Masu Amfani A Duniya Da Lahira
Labarin na GabaYadda Ake Addu’ar Samun Lafiya Ga Cututtuka