“Subhaana Rabbiyal a’alaa”.
{Tsarki ya tabbata ga Ubangijina mafi É—aukaka}. Sau uku (3).
“Subhaanakal laahumma rabbanaa wa bihamdika Allaahummagfir lii”.
{Tsarki ya tabbata gare ka, ya Allah! Ya Ubangijinmu! Tare da godiya gare ka. Ya Allah! Ka gafarta mini }.
“Subbuhun Æ™uddusuun Rabbul Mala’ikati war ruuhi”.
{(Ubangiji) abin tsarkakewa, mai kuÉ“uta daga dukkan abin da bai kamace shi ba, Ubangijin Mala’iku da Jabrilu}.
“Allaahumma laka sajadtu wa bika aamantu, walaka aslamtu sajada wajhii lillazii khalahu wa sauwarahu wa shaƙƙa sam’ahu wa basarahu tabaarakal laahu ahsanul khaaliÆ™iina”.
{Ya Allah! Gare ka na yi sujada, kuma da kai na yi imani, kuma gare ka na miƙa wuya. Fuskata ta yi sujada ga wanda ya halicce ta. Kuma ya yi mata sutura, kuma ya tsaga ji da gani a gare ta. Allah mafi gwanintar masu halitta, ya girma, kuma alherinsa ya yawaita}.
“Subhaana zil jabaruuti, wal malakuuti, wal kibriyaa’i, wal azamati”.
{Tsarki ya tabbata ga (Allah) Mai dole, da mulki, da ƙasaitar ɗaukaka da girma}.
“Allaahummagfil lii zanbii kullahu, diƙƙahu wa jillahu, wa auwalahu wa akhirahu wa alaaniyatahu wa sirrahu”.
{Ya Allah! Ka gafarta min zunubaina dukkanninsu, ƙanananansu da manyansu, na farkonsu da na ƙarshensu, bayyanannunsu da ɓoyayyunsu}.
“Allaahumma inni a’uzu bi ridhaaka min sakhaÉ—ika, wabi mu’aafaatika min uÆ™uubatika wa a’uzu bika minka, laa uhsii sanaa’an alaika anta kamaa asnaita alaa nafsika”.
{Ya Allah! Ina neman tsari da yardarka daga fushinka, da kuma rangwamanka daga uƙubarka, kuma ina neman tsari da kai daga gare ka. Ban isa na tuƙe ga yabo mai cancanta gare ka ba; kai dai kamar yadda ka yabi kanka ne}.
Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tahiyya danna nan.
Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Yin Ruku’u danna nan.
Wannan bayanin anciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga AlÆ™ur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.