Karatun Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam)

0
413

Allah Madaukaki ya ce da Manzonsa (Sallallahu alaihi wassallam):
“Ka kyautata karatun Alkur’ani matukar kyautatawa”.Suratul Muzammil, aya ta 4.

Sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana yayyanka karatunsa, aya-aya, yana cewa: (alhamdulillahi rabbil alamin)
Sannan ya tsaya, sannan ya ce: (Arrahamanurrahim)
Sannan ya tsaya, kuma yana jan muryarsa da karatu ja sosai. Sannan kuma karatunsa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, karatu ne da za a iya fassara shi harafi-harafi

Suratul Fatiha, aya ta (1-2).

Domin karanta cikakken bayani a kan Kukan Manzon Allah (sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Manzon Allah Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) Kamar Ga Ka Ga Shi wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceHaƙƙin Uba.
Labarin na GabaHarsashin Gina Al’umma (Iyaye)