Yadda Ake Yin Sallar Istihara

0
696

An karɓo da ga Jabir (R.A) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) Ya kasance yana koya mana istihara a cikin duk abin da za mu yi kamar yadda yake koya mana surar Alƙur’ani.

Yana cewa: “Idan ɗayanku ya himmatu da aikata wani abu, to ya yi sallar nafila raka’a biyu bayan sallama sai ya ce:
“Allahamma inni astakhiruka bi ilmika wa astakdiruka bi kudratika, wa as aluka min fadlika azim, fa innaka takdiru wala akdirun, wata’alamu wala’alamu wa anta allamul guyub.Allahumma in kunta ta’alamu anna hazalAmru (anan sai ka/ki faɗi bukatarka/ki) khairun lii fii dini wa ma’aashii wa aƙibatu amrii (aajilihi wa ajilihi fakaddirhu lii wa yassir hu lii summa barik lii fii hi, wa in kunta ta’alamu anna hazal amrii sharrun lii fii dinii wa ma’aashi wa aƙibatu amrii(aajilihi wa ajilihii) fasarrifi hu anni wasarif nii anhu waƙaddir liyal khaira haisu kaana summa ardinii bi hii. Bukhari 6382 Abu Dawud (1538)

Wannan ita ce Istihara ingantacciya, saboda haka ɗan uwa ka yi fatali da duk wata istihara wacce ta saɓawa wannan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Salatut Tasbihi danna nan wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceFalalar Azumin Watan Muharram
Labarin na GabaHaƙƙin Uba.