Muhimmacin Sanin Kamannin Annabi:

0
765

 Domin abin da mutum yake so ya kamata ya san shi. Kuma ma ai mukan ce: “Allah ya sa mu ga Annabi” watau a lahira. Kai ba ma sai a lahira ba.

Babu shakka ganin Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) a mafarki abu ne mai yiwuwa. Amma yaya za a yi mutum ya san shi ya gani. Babu shakka sai mutum ya san kamanninsa sannan zai san, shi ɗin ya gani a mafarki. Ga dai yadda lamarin yake a hadisin Abu Huraira (R.A):
“Daga Abu Huraira (R.A) ya ce: “Na ji Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) yana cewa: “Wanda duk ya gan ni a mafarki, to zai gan ni a farke. Shaiɗan ba ya kamantuwa da ni”, (Bukhari da Muslim suka ruwaito). Imamul Bukhari ya ce: Malam Ibnu sirina ya ƙara da bayanin cewa: “Idan ya gan shi a kamanninsa”. Ka ga kenan dole sai mutum ya san kamanninsa. Idan ba haka, ba sai Shaiɗan ya zo wa mutum a kamar da ba ta Annabi ba.
A wata ruwayar ta Muslim: “Wanda ya gan ni a mafarki to zai gan ni a farke, ko kamar ya gan ni ne a farke. Shaiɗan ba ya kamantuwa da ni”.
Wannan ya nuna cewa, lallai ne duk Musulmi ya san kamannin Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam). Malamai sun yi ƙarin bayani game da jimlar: (To da sannu zai gan ni a farke), inda suka ce, wannan jimilar ta zo a ɗayan ruwayoyin Muslim tare da nuna shakka daga mai ruwaya kan ɗayan biyu: Watau da ƙari kamar haka: “Ko kamar ya gan ni a faɗake”.
Haka kuma ya zo a wata ruwaya kamar haka (haƙiƙa ya gan ni a farke)2. Watau, “Ni ya gani, gani na haƙiƙa”
Abin nufi a nan shi ne, kada ka wahalar da kanka da fassarar masu cewa idan mutun ya gan shi a mafarki to zai gan shi a duniya, kuma a farke. Wannan ɓatacciyar fassara ce. Ba ta da tushe a addini. Abin da za ka fahimta shi ne, sauran ruwayoyin biyu ƙarfafa ganin suka yi. Wannan ya sa malamai suka ɗauka ta farkon ma haka take nufi, wato ƙarfafa ganin take nufi. Ba wai tana nufin za a gan shi a farke a wannan duniyar tamu ba.

Domin karanta cikakken bayani a kan Suffar Jikin Annabi (Sallallahu alaihi wassallam) danna wannan koren rubutun.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Kamannin Annabi (Sallallahu alaihi wassallam) Ɗabi’unsa Da Halayensa Domin Koyi Da Shi wanda Dr Yahaya Tanko ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna koren rubutun nan.

labarin da ya wuceSiffar Jikin Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam)
Labarin na GabaRaya Daren Lailatul Ƙadari
Dr. Yahaya Tanko
A yanzu Dr. Yahaya Tanko Yana Bayar da darasai na littafai huɗu a mako, a masallacin Umar bin Khaɗɗab da da littafan Sahihul Bukhari da Fathul Majid a masallatan Nana A’isha da na Khalid binil Walid a unguwar Dukawuya FCE. A yanzu Allah ya azurta Yahaya Tanko da zuryya mai yawa, ‘ya’ya da jikoki. Ya yi ritaya a watan Febreru na shekara 2015 daga Jami’ar Bayero ta kano. Amma ya kama aikin kwantiragi da jami’ar Yusuf Maitama sule ta Kano.