Siffar Jikin Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam)

0
784

Allah (Subhanahu wata’ala) ya fifita Manzonsa da kyan halitta, fiye da sauran bayinsa.

Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) mutum ne madaidaicin halitta. Ba dogo ba, ba kuma gajere ba. Watau shi matsakaici ne.
Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) fari ne mai surkawa da jaja-jaja. Watau ba fari gau ba. Allah ya halicce shi da fuska mai haske. Yadda fuskarsa take a tsakanin mutane, kai ka ce farin wata ne, irin yadda yake haskaka sauran halittu na duniya. Yana da yalwar goshi da karan hanci. Yana da gashin ido da na gira, masu duhu. Yana da tsagar baki mai ɗan tsayi, ba tsukakkiya ba. Haka nan yankan tsagar idanunsa su ma suna da ɗan tsayi. Ƙwayar idanunsa fara ce tas, baƙin kuma baƙi suɗuk. Wuyansa yana da ɗan tsayi. Yana da wushirya a tsakanin haƙoransa na gaba. Gashin kan Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) baƙi ne wuluk, kuma mai tsayi. Wani lokacin, Idan ya bar shi, yakan kai iya kunnuwansa, daga bayansa. Kuma yakan zuba a kan kafaɗunsa. Yana da gemanya mai duhu. Kuma yana barinta ta yi tsayi. A ƙarshen rayuwarsa ya yi furfura a kansa da gemanyarsa, wadda ba ta fi ƙidayawa ba.
Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) yana da faɗin ƙirji. Watau akwai faɗi a tsakanin kafaɗunsa. Cikinsa ba shi da tudu. Yana da gaɓoɓi watau ƙasusuwansa suna da girma. Akwai gashi daga tsakiyar ƙirjinsa zuwa cibiyarsa. Akwai hatimin annabta a gefan kafaɗarsa ta hagu, daga baya. Yana da tsayin hannaye madaidaita. Tafukan hannayensa suna da ɗan tudu da taushi. Ba a ƙarmashe suka ba. Haka nan kasangalalinsa da tafukan ƙafafuwansa. Amma ba shi da nama a agararsa. Watau agararsa a motse take. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi.
Daga is’haƙa ya ce:, na ji Barra’u yana cewa: “Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) ya kasance ya fi kowa kyan halitta. Ba kuma gajere ba”. (Muslim ne ya rawaito)
Daga Aliyyu bin Abi Ɗalibin (R.A), ya ce: “Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) fari ne, mai cizawa da jaja-jaja” (Albani ne ya ruwaito a cikin Aljami’us Sahih).
Daga Abdur Rahman ɗan Abdullahi ɗan Ka’abu (ya ce. “Abdullahi ɗan Ka’abu ya ce: “Na ji Ka’bu ɗan Maliku yana bayani game da abin da ya faru sanda Allah ya karɓi tubansu na rashin zuwa masallaci, ya ce: Na yi sallama ga Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam), alhali fuskarsa tana ƙyalƙyali saboda farin ciki ya kasance idan ya yi farin ciki sai fuskarsa ta yi haske, kai ka ce wani yanki ne na farin wata. Mun kasance muna gane haka game da shi “(Bukhari ne ya ruwaito).
Galibi ana siffata fuskar Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) da farin wata, saboda haske da walwala da fuskarsa takan yi (musamman) a yayin da yake cikin farin ciki. Wannan yana nufin cewa, kamar yadda farin wata yake a duniya, to haka Annabi yake a cikin mutane. Amma a wannan hadisin na Ka’abu bin Malik ya ware, wani kashi ne na wata, domin yin ishara da goshin Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam), inda hasken ya fi bayyana, a sanda yake cikin farin ciki. Shi ya sa ya keɓance shi da wani yanki na wata.
—————————-
Duba Fathul Bari 122\8
Daga Abu Is’hak ya ce: An tambayi Barra’u (R.A), shin fuskar Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) kamar (hasken) takobi take? Sai ya ce: “A’a”, kamar (hasken) wata take” (Bukhari ne ya ruwaito)
Daga Jabir ɗan Samuratu, ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) ya kasance mai faɗin baki, mai tsayin yankan idanu, Mai siraren maƙyangyama…” (Muslim ne ya ruwaito).

Domin karanta cikakken bayani a kan Ɗabi’un Annabi (Sallallahu alaihi wassallam) Da Halayensa danna koren rubutun nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mu San Kamannin Annabi (Sallallahu alaihi wassallam) Ɗabi’unsa Da Halayensa Domin Koyi Da Shi wanda Dr Yahaya Tanko ya wallafa shi, domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceƘiyamul Laili (Tahajjud)
Labarin na GabaMuhimmacin Sanin Kamannin Annabi:
Dr. Yahaya Tanko
A yanzu Dr. Yahaya Tanko Yana Bayar da darasai na littafai huɗu a mako, a masallacin Umar bin Khaɗɗab da da littafan Sahihul Bukhari da Fathul Majid a masallatan Nana A’isha da na Khalid binil Walid a unguwar Dukawuya FCE. A yanzu Allah ya azurta Yahaya Tanko da zuryya mai yawa, ‘ya’ya da jikoki. Ya yi ritaya a watan Febreru na shekara 2015 daga Jami’ar Bayero ta kano. Amma ya kama aikin kwantiragi da jami’ar Yusuf Maitama sule ta Kano.