Yadda Ake Yin Kabbarar Harama

0
674

Bayan gama iƙama a sallar jam’i ko sallar mutum shi kaɗai; mace ce ko namiji, sai ya yi kabbarar harama wacce ita ce mabuɗin sallah.

Yadda ake yin ta shi ne, furta kalmar (Allahu Akbar) tare da ɗaga hannuwa biyu daidai kafaɗu biyu; ko kuma daidai kunnuwa biyu; ko kuma saman ‘yan yatsun, su kawo daidai kunnuwa.

Shi kuma mahaɗar tafin hannu da tsintsiyar hannu ya zo daidai kafaɗu; wannan kabbarar haramar ita ce da zarar mai sallah ya furta ta, ta haramta masa duk wani aiki da ba shi da alaƙa da sallar; kamar yin magana, ko waiwaiye, ko cin wani abu, ko tauna, ko dariya, ko sauraren wani abu can daban, da bai shafi karatun liman ba.

Sai ɗan abin da yin sa babu laifi, kamar yin kuka saboda jin abin da Ƙur’ani yake faɗa; na rahama, ko azaba, ko daɗin karatun ko sosa jiki, ko yin ɗan motsi kaɗan, ko gyaran murya. Yin wannan kabbara ta harama, wajibi ne a sallah ga bin jam’i ko yin sallah; shi kaɗai mace ce ko namiji ne, mamu ne ko limami ne, wanda duk bai yi ta ba, ba shi da sallah, saboda da ita ce ake fara buɗe sallar, kamar yadda bayani ya gabata.

Ana so mai sallar ya yi (du’aa’ul istiftah) wato addu’ar buɗe karatun sallah wacce yin ta (mustahabi) ne; ma’ana abin da aikata shi lada ne, rashin aikata shi kuma ba laifi ba ne; a taƙaice dai an ba ka zaɓi na idan kana so ka yi; idan ba ka so kuma ka bari.

Ga yadda ake furta wannan addu’ar:

(Allahumma baa’id baini wa baina kaɗayaya kama ba adta bainal mashriqi wal magribi, Allahummag silni bil ma’i wal salji wal bardi wa nakkini minaz zunubi wal kaɗayaya kama yunaƙƙal saubul abyad minal danas).

Fasarar wannan addu’a shi ne; Allah ka nisanta tsakanina da zunubaina kamar yadda ka nisanta tsakanin mahudar rana da mafaɗar ta; Allah ka wanke ni da ruwa da kankara da ruwan sanyi, ka wanke ni daga zunubaina da kurakuraina; kamar yadda ake wanke fararen tufafi daga cikin datti.

Bayanin da Ibnu taimayyah ya yi a kan wannan addu’ar a lokacin da ɗalibinsa; Ibnul Ƙayyim ya tambaye shi ma’anar wannan addu’a ga mai yin sallah, shi ne ya ce; “Idan mutum yana aikata saɓo zuciyarshi bushewa take yi, har ta kai matakin da za ta yi tauri, yadda hasken imani ba zai iya shiga ba, sai ya wayi gari imaninsa ba ya ƙaruwa.

Idan ya aikata wani babban saɓon, sai zuciyarsa ta kama da wuta tana cinye ragowar imanin da ke zuciyar. Ga shi kuma babu abin da ke kashe wuta sai ruwa, shi Kuma ruwan sanyi shi ne zai ƙarasa murkushe ragowar ɓurɓushin wutar, bayan an kashe asalin wutar da ruwa, ita kuma ƙanƙara ita ce za ta mayar da zuciyar ta koma mai laushi, kamar yadda take kafin ta aikata manyan saɓo. Wannan shi ne dalilin da yasa ake so mumini ya dinga yin wannan addu’ar.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Buɗe Karatun Alƙur’ani da Bismillah A Cikin Sallah Danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Buɗe Karatun Alƙur’ani Da Bismillah A Cikin Sallah
Labarin na GabaYadda Za Ki Ja Hankalin Mijinki 02
Lawan Bello
Abu muzaffar Malami ne masanin ilimin zamani da na addini bisa tsaren Ƙur'ani da tafarkin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, mai hangen nisa a addini da kuma alummma, shugaban Abu Muzaffar foundation.