Falalar Salati Ga Manzon Allah (S.A.W)

0
899

An karɓo daga Abdullahi Ibn Mas’ud (RA) haƙiƙa Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: “Haƙiƙa mutane da za su fi kusanci da ni rana alƙiyama su ne, waɗanda suka fi yawaita salati a gare ni” (Tirmizi 446).

An karɓo daga Abdullahi Ibn Malik (RA) ya ce: Manzon Allah (S. A. W.) ya ce: “Wanda ya yi min salati guda ɗaya, Allah zai yi salati goma, kuma za a kankare masa zunubi goma, kuma za a ɗaga darajojinsa” (Nisa’I 1280).

An karɓo daga Abdullahi Ibn Amr Ibnul As (RA) haƙiƙa ya ji Manzon Allah (S.A.W.) yana cewa: “Idan kuka ji mai kiran salla, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati, sabo da duk waɗanda ya yi min salati ɗaya, Allah zai yi masa goma, sannan ku roƙa min Allah ya ba ni matsayin wasila, saboda wasila wani matsayin ne da mutum ɗaya ne kaɗai a cikin bayin Allah zai cancance shi, ina fatan na kasance ni ne wannan bawan, Kuma duk wanda ya roƙa min wasila, cetona ya tabbata a gare shi” (Muslim 577).

Falala da fa’idodin salati ga Annabi (S.A.W.) suna da yawan gaske, yana haskaka zuciya da da kaifafa ƙwaƙwalwa, yana sanya a gafarta zunuban mutum, addu’ar da ake fara da shi karɓaɓɓiya ce, yana yaye baƙin ciki da ɓacin rai da suran fa’idoji masu yawa.
Haka kuma akwai wurare da ake son a yi wa Annabi (S.A.W.) salati kamar a ƙarshen kiran salla da tahiyar farko da ta biyu, a lokacin addu’a da duk lokacin da aka ambaci sunansa da sauransu.

Faɗakarwa

Ya kamata ‘yan uwa mu sai cewa babu wani salati mai falala da daraja in ba salatin da ya fito daga bakin fiyayyen haitta ba (S. A. W.) a ingantattun hadisansa. Saboda haka, mu riƙi irin waɗanna salalatai mu bar kame-kame.

Sigogin salati da suke da inganci da Manzon Allah (S.A.W.) za su kai goma sha bakwai, sai a tuntuɓi malaman sunna domin ƙarin bayani. Allah ya sa mu dace.

labarin da ya wuceYadda Ake Sallar Istihara
Labarin na GabaFalalar Lahaula Wala Ƙuwwata Illa Billahi