An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu anhu ) ya ce: wata rana bayan sallar Asuba, sai Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: da Bilal:
“Ya kai Bilal , faɗa min aikin da ka fi sa rai da shi a Musulunci; saboda na ji ƙarar takalminka a gabana a Aljanna (Ma’ana yana yi wa Annabi zagi a Aljanna) sai ya ce, “Babu aikin da na fi sa rai da shi fiye da sallar da nake yi gwargwadon hali a duk lokacin da na yi alwala ko dare ko rana” .(Bukhari 1149, Muslim 910)
Wannan ya nuna cewa Bilal ya sami matsayin zagin Annabi a Aljanna ne, Saboda sallar alwala da yake yi sai mu dage ‘yan uwa.
Domin karanta cikakken bayani akan Sallar Tahiyyatul Masjid danna nan.
Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.