Ma’anar Sallar Tuba Da Falalarta

0
1061

Duk lokacin da tsautsayi ya ɗauki mutum ya aikata wani saɓo, to sai ya yi gaggawar tuba da koma wa ga Allah Ta’ala. Ana so ya yi alwala ya yi nafila gwargadon iko sannan ya yi istigfari. wannan sallar ita ce sallar tuba.

Falalar Sallar Tuba

An karɓo da ga Sayyadina Abubakar (Radiyallahu anhu) ya ce: “Na ji Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) yana cewa: “Duk mutumin da ya aikata wani zunubi sannan ya tashi ya yi alwala ya yi salla. Ya yi istigfari, haƙiƙa Allah zai gafarta masa sai ya karanta wannan ayar: “Kuma su ne waɗanda idan suka aikata alfasha ko suka zalunci kawunansu, sai su tuna Allah su nemi gafara ga zunubansu” (Al-Imran 135) (Tirimizi 406, Abu Dawud 1521. Iban Majah 1395).

Domin karanta cikakken bayani a kan Raka’o’in Ɗawafi danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceSallar Alwala Da Falalarta
Labarin na GabaRaka’o’in Ɗawafi