fbpx
Gida Ilimin Addini Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu

Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu

0
722

Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya faɗa a cikin Hadisin da ya ruwaito daga Allah Tabaraka wata’ala (Hadisi ƙudsi) ya ce:

Allah Tabaraka wata’ala ya ce: “Duk wanda ya yi gaba da masoyi na haƙiƙa ina sanar da shi da ɗaura yaƙi (da ni) bawana bai kusance ni ba da wani abu da na fi so fiye da abin da na wajabta masa, bawa ba zai gushe ba yana kusanta ta da nafiloli har sai na so shi, idan na so shi, sai na zama ganinsa da yake gani da shi, na zama hannunsa da yake riƙo da shi, na zama ƙafarsa da yake tafiya da ita, in ya roƙe ni zan ba shi , in ya nemi tsari daga gare ni, zan tsare shi, ban taɓa kai kawo ba cikin wani abu da zan yi kamar yadda nake kai kawo kan karɓar ran mumini, yana ƙin mutuwa ni kuma ina ƙin ɓata masa rai”.
Wannan hadisi ne babba, sananne, ingantacce kuma mutawatiri, Imamu Buhari da Ahmad da sauransu sun ruwaito shi.

Sannan kuma wannan hadisi yana cike da ɗimbin fa’idoji da darussa masu yawa kaɗan daga cikinsu su ne:

1- Hanyar samun walittaka ita ce kula da aikata farillai sannan kuma nafiloli.
2- Waliyyi na gaskiya ba ya amfani da gabobinsa wajen aikata abin da Allah ba ya so. Wannan shi ne ma’anar Allah zai zama jinsa, da ganinsa da hannunsa da ƙafarsa.
3- Duk mai gaba da waliyyai yana yaƙi ne  da allah.
4- Allah yana girmama waliyyansa da karamomi.
5- Duk musulmi mai aikata farillai da nafiloli yana da rabo na walittaka, sai dai walittakar matsayi-matsayi ce kuma kowa ya san gaba da gabanta.
Waliyyai masu daraja ta farko su ne manzanni da annabawa, sai sahabbai, sai tabi’ai dai har zuwa yau har gobe gwargwadon imanin mutum da tsoron Allah da ya ke da shi gwargwadon matsayinsa a walittaka.
A wannan littafi zan ɗauki ɓangaren dake maganar nafilolin a wannan hadisi domin mu yi ƙoƙarin samun ƙauna da kulawa da kariya daga Allah Ta’ala.
Yana daga rahamar Allah da falalarsa ga bayinsa da ya shar’anta nafiloli ga dukkan farillai. Saboda haka, zan ɗauki rukanan musulunci guda biyar, na kawo abin da ya sauwaƙa na nafilolin kowanne rukuni da bayanin falalarsu.

Domin karanta cikakken bayani a kan Fa’idojin Sallar Nafila danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad ( Shehu Mansur Dala ) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

×

Maraba!

Yi magana da mu kai tsayi ta WhatApps ko a shiga group din mu.

×