Kura-kuran Masu Bayar Da Tarbiyya.

0
601

lyaye da malamai da sauran waɗanda nauyın tarbiyya yake
kansu sukan tafka waɗansu kura-kurai da sukan kawo cikas ko nakasu
ga tarbiyyar ‘ya’ya ko ma gaba ɗaya a rasa tarbiyyar.

Waɗannan kura-kuran suna da yawa, ga kaɗan daga
cikinsu:

1.Magana daban aiki daban.
Misali iyaye za su hana ‘ya’ya zagi ko ƙarya ko saɓa
alkawari amma su suna yi.
2. saɓani tsakanin masu tarbiyya
Misali Uwa ta ce, “Yi kaza”, Uba ya ce, “Kada a ka yi”, ko ka ga a gida
ana rusa abin da aka koyar a makaranta, ko akasin haka.
3.Gallazawa da tsanantawa.
Wani horon yakan zama azaba kamar hana yaro abinci da yi
masa dukan kawo-wuƙa da  korar sa daga gida, da ɗaure shi da
sauransu, wannan ba ladabi ba ne.

4.Rainon yaro a kan tsoro da ragwanci.
Tsanani da takurawa in suka yi yawa, sai yaro ya taso da
tsoro da gaulantaka.
5. Shagwaɓa
Bai kamata saboda tsananin ƙauna har kuma a bar ɗa ya
zama shagwaɓaɓɓe ba, ba faɗa ba kwaɓa ba a ganin
laifinsa har iyaye su rinƙa rigima da malamai da duk wanda
ya yi ƙoƙarin tsawatar da ‘ya’ya kan wani abu maras kyau.
6.Nuna bambanci
Nuna bambanci a tsakanin ‘ya’ya yana da mummunan
tasiri da kawo cikas ga tarbiyyarsu da zumuncinsu da ma
biyayyarsu ga iyayensu.

7.Barin ‘ya’ya a hannun ‘yan aikin gida ko masu raino.
Waɗansu iyayen saboda isa ko wayewa ko aiki sai su fice su
bar ‘ya’yansu a hannun masu raino, ko su kai su gidan raino
sai sun dawo su ɗauke su. Wannan babban kuskure ne.

8.Raina ‘ya’ya
Yaro yana so a mutunta shi. amma a wajen waɗansu iyaye
Ko da ya yi jikoki to yana nan dai a yaro bai isa komai ba.
Wannan kuskure ne.
9.Amfani da kayan Sadarwa:
Cikakken ‘yancin amfani da kayan sadarwa na zamani ba
tare da wata kulawa ba. wannan yana matuƙar gurɓata
tarbiyya
10.Ƙwauro da rowa.
Misali: Ƙin kashe kuɗi a bangaren ilmi da lafiya da ci da sha da sutura alhali akwai ikon yi.
11.Ƙin saka su aiki
Komai sai a sa almajirai da ‘yan aikin gida, su yara ba
abin da suka sani sai su wanke goma su tsoma biyar
12.Wulaƙanta ‘ya’ya da cin zarafin su.
13.Tsananin kyautata zato, da tsananin munana zato

Wasu iyayen ba sa yarda da laifin ‘ya’yansu, komai suka yi
sai su ce sharri a ka yi musu, in kuma a gabansu suka yi sai
su ce ba halinsu ba ne, ‘ya’ yan wane ne suka koya musu.
Waɗansu kuma kullum cikin tuhuma da zargin ‘ya’yan
suke. Ba sa nuna jin daɗinsu da murna ga wani ƙwazo na
‘ya’ya sai dai kullum su rinƙa gwale su, su kushe su. duka
wannan kuskure ne.

14.Baƙar addu’a
Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya hana a yi wa ‘ya’ya da iyali da
dukiya baƙar addu’a. Saboda in Allah ya amsa sai su lalace.
15.Kura-kurai lokacin haihuwa
Sun haɗa da jin haushin abin da aka Haifa saboda mace ce
ko namiji ne, saka musu suna marasa kyau, ƙin yin haƙiƙa
(ragon suna), alhali akwai ikon yi, jinkirin yin kaciya. ƙin sayan kayan jarirai da gallazawa da baƙantawa mai jego da sauransu. Ya kamata masu ba da tarbiyya su guji waɗannan kurakuran da ire-irensu. Allah ya taimake mu. Amin.

Domin karanta cikakken bayani a kan Matakan Tarbiyya Guda Ɗari danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Tarbiyar ‘Ya’Ya Daga Neman Aure Zuwa Girmansu wanda Shehu Usman Abubakar (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceSiffofin Masu Bayar Da Tarbiyya
Labarin na GabaIngantattun Nafiloli Da Falalarsu