Addu’ar Biyan Bashi – Wannan addu’a ce ga wanda bashi ya yi wa yawa, yana so ya biya, ko kuma mutum na cikin tsanannin ƙuncin rayuwa.
Akan so ka tashi cikin dare, ko kuma wani lokacin ka yi alwala, ka yi sallah raka’a biyu; sannan ka karanta wannan addu’a;
“Bismillahir rahmanir rahim, allahummag firli zanbi, wa was’is khulƙi, wa ɗayyib li kasbi, wa ƙanni’ni bima razaƙtani, wala tuzhib ƙalbi ila shai’in sarraftahu anni”.
Sannan ana so duk lokacin da ka idar da sallar asuba, ko kuma wata sallah cikin salloli biyar, to ka yawaita karanta wannan addu’ar. Yawaita karanta wannan addu’ar yakan sa Allah (Subhanahu Wata’ala) ya warware maka dukkan bashin dake kanka. Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ne ya bai wa Sayyidina Aliyu (Radiyallahu Anhu). Ya ce da shi; “Shin ina so in ba ka tumaki guda dubu biyar, ko kuma na ba ka wasu kalmomi biyar. Sai sayyidina Aliyu ya ce,” Ya Rasulullahi ka ba ni kalmomi guda biyar, sai sun fi dabbobi dubu biyar”.
Addu’ar Biyan Bashi – An samo wannan addu’ar ne a cikin littafin Miftahul Farj, shafi na 110.
Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Biyan Buƙata A Wajen Allah (S.W.T) danna nan.
Don karanta bayani a kan Lokuta Zaɓɓaɓu Na Karɓan Addu’a danna nan