Yawaita Azumi A Watan Sha’aban

0
649

Ana so musulmi ya yawaita azumin nafila a watan Sha’aban, domin koyi da Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) da kuma tattali da tanadin zuwan Ramadan.

An karɓo daga A’isha (Radiyallahu anha) ta ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya kasance yana yawaita azumi, har sai mun ce ba ya hutawa, wani lokacin kuma yakan huta (da Azumin) har sai mun ce ba ya azumi, kuma ban taɓa ganin Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya yi azumin wata guda cur ba, sai dai watan Ramadan, ban taɓa ganin wani wata da yake yawaita azumi a cikinsa ba, kamar watan Sha’aban”.(Bukhari 1969, Muslim 1156).

Domin karanta cikakken bayani a kan Azumin Kwanaki Shida A Watan Shawwal danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceFalalar Azumin Tasu’a Da Ashura
Labarin na GabaAzumin Kwanaki Shida A Watan Shawwal